028

1K 113 9
                                        

Shigar da Mansur akayi VIP room na cikin prison d'in, kallon d'akin yake babu abinda ya rasa na 'kawa amma wani 'kunci je ya ziyarceshi da ya tuna a nan ake so ya 'kare rayuwarsa.

Matsakaicin d'aki ne da madaidaicin gado an shinfid'a masa wani lallausan bedsheet, bangon dake kallon bakin gadon kuwa tv ce a ma'kale, a table d'in bakin gadon lemo need da cup a ajiye sai kuma jarida da akwatunan kayansa.

Band'akin cikin d'akin ya duba shima baida wani matsala an tsaftaceshi sosai, zama yayi Kan kujerar da aka ware masa ta cin abinci sannan yace "Ina bu'katar waya".

Wayarsa mai kula dashi ya mi'ka masa sannan ya fice, kiran mutum na 'karshe da ya zamar masa gata yayi wani abokin adawar Abba a kasuwanci sunansa John wani inyamuri, shine suke gogayya da kasuwanci lokacin da Abba ke Raye, duk abinda Abba yayi shima wannan mutumi sai yayi shi hakan yasa suka Jone d Mansur yana fad'a Masa sirrikan abokin nasa.

"Ka isa lafiya?" John ya furta cikin nuna isa.

"Na isa, the place is fine amma har zuwa yaushe zan zauna anan?"

" Well.....it depends zuwa yaushe abubuwan da ka sayarmin zasu iso hannuna, zanci gaba da d'aukan nauyin duk abinda kake bu'kata, idan wannan takardu suka iso hannuna I will find a way to free you, but remember, bazaka iya zama free ba idan har baka biya tarar dake kanka ba".

Shiru Mansur yayi hankalinsa ya 'kara tashi, wannan masifar da yarannan suka janyo masa ta sanyashi mantawa da cinikin da sukayi da john, kame-kame Mansur ya fara yace "umm....ammm.....ehhhh....ka Gane John? Wannan ciniki bazai yiwu ba domin kotu ta 'kwace dukka dukiyar yarannan daga hannuna kuma tuntuni iya kamfanonin da na sayar maka sune takardunsu ke hannuna sauran duk banida masaniya ina takardunsu suke juyasu kawai nakeyi, a 'karshe ma na fahimci kud'in dai account d'insa yake tafiya".

" What!! You lie to me? Mansur I thought all the assets are with you kace zaka sayarmin da kamfanin glass d'insa is that also a lie?"

Shiru Mansur yayi ya kasa magana, tsaki John yaja yace "dumbass, I'm done with you thank your Lord kud'i bai had'ani da Kai ba da sai na wula'kanta ka, now figure how to  free yourself I'm done karka sake nemana idan ka nemeni you will regret it and remember sai ka biyani months allowance da na bayar domin a kula da kai ko ta wane hali sai sai ka biya". Katse kiran John yayi hankalin Mansur ya sake tashi, kiran d'aya daga cikin 'yan majalisar da yake hulda dasu a baya yayi amma sam ya'ki amsawa 'karshe ma yaji kiran ya dena tafiya.

Gata d'aya da Mansur ya samu na biya masa kud'in wata guda da akayi ne, a ciki ake kawo masa abinci da duk wani kayan masarufi na rayuwa har sai ya za'bi kalar abincin da yakeso, wayar hannunsa kawai suka kar'ba amma jaridar kowacce rana sai an kawo masa ita.

Bayan ya cika wata guda suka 'kara masa sati d'aya, ganin baida niyyar biya yasa shugaban prison d'in samunsa su tattauna.

"Ranka ya dad'e kud'in da aka turo mana na kula da kai ya 'kare har mun fara ta'ba kud'in da gwamnati ke turowa na abincin ragowar mutanen, kud'in da ake kashe maka a wuni d'aya dai-dai yake da kud'in da ake kashe musu na rana guda, a satinnan mun ta'ba kud'in mai yawa wanda idan har baa maidashi ba saidai biya ya hau kanmu".

Kamewa Mansur yayi yace nawa ne kud'in?"

Takarda mutumin ya zaro ya fara karantowa Mansur, "abinci ana sayo maka na 2500, ya Kama 7500 kenan a rana, a wata 225,000, sai jarida 500 a kullum ta kama 15,000, sai kuma lemo da kayan marmari 1,500 a kullum, wata ya Kama 45,000, sai kuma ruwa na 10,000 a wata, masu wanki 20,000, sai kuma 50,000 na tsaron lafiya da sauran abubuwa sai kuma abinda ake biyanmu 85,000 ya kama 450,000 a wata to kaga kuma ga qarin na satinnan 105,000".

Mansur na ri'ke da remote yace " a kawomin wayata na tura muku 600 yayi?"

Cikin murna mutumin yace "yayi ranka ya dad'e".

HASKEN RANA✔️Stories to obsess over. Discover now