005

1.3K 117 1
                                    

Tunawa tayi da rayuwar da tayi a baya, idan ta bar gidan a wannan hali ina zata je ga yara ga d'inki ga jego?

"Hajiya kiyi ha'kuri na samu sau'ki sai na tafi, zan miki aikace-aikace dan Allah ki barni na zauna har na warware".

"Iya taimako nayi miki, na biya miki kud'in aiki na kula dake a zamanki na asbiti, na kawoki gidana an kula dake idan har bazaki min godiya a wannan taimakon da na miki ba kin cika butulu, na miki iya abinda zan iya".

"Ko kayan sakawa banida su". Ta furta a hankali, d'aga kanta tayi ta kalli Hauwa dukda ta taimaka sai taji a ranta batason matar.

D'aki Hanan ta nufa ta fito da kaya cikin leda ta mi'kawa Mardiyya "kayansu ne". Wasu kayan ne a hannunta set biyu duka riga da zani da mayafi guda d'aya da underwear ta ajiyesu kan cinyar Mardiyya tace "wannan kuma naki ne, mun cutar dake amma kuma iya taimakon da kike bu'kata mun baki, ki d'auki hanya ki koma garinku ki koma wajen iyayenki ko mijinki".

Godiya Mardiyya tayi mata ta d'auki yaranta da ledar kayansu ta nufi sashin masu aiki, sanar musu tayi gobe da safe zata tafi, abinda bata ta'ba zato ba saida suka had'a mata 1200 tayi kud'in mota sannan suka bata zannuwa da hijabu kirkinsu har yafi na Mum.

Tun gari bai gama wayewa ba d'aya daga cikin masu aikin ta yiwa twins wanka Mardiyya ta goyasu duka biyun a bayanta ta d'auki kayanta ta fita, bataso tayi arba da kowa a cikin gidan musamman Abba.

Tana fita ta duba ma'ajiyarta ta d'auki abubuwan da ta ajiye, kangon da take kwana ta nufa domin a can take ajiye kud'in da Abba ya fara bata.

Da 'kafarta ta ture dutsen da ta ajiye kud'in 'kar'kashinsa ta d'auki kud'in, 'kirgawa tayi taga 2000, ya zama 3200 kenan, me zatayi da wannan kud'in? Zasu isheta samun matsuguni da abinci?

Zama tayi a kangon domin ta huta ta kunce yaranta, d'inkin cikinta da ciwon 'kafarta zugi suke mata saidai bata da yanda zatayi, dukda an mata dressing d'in ciwon 'kafarta a asbiti saidai sake lalacewa yakeyi.

Ta jima a kangon tana sa'ka da warwarar inda zata nufa, taimako a wannan duniyar abu ne mai wuya domin taga hakan a baya, ina zata nufa yanzu?

Saida ta fara jin yunwa sannan ta goya twins dake bacci, ro'kon Allah takeyi ya sassauta mata rayuwarta ko dan wad'annan yaran.

Bayan taci abinci ta d'auki hanya,  wasu mutane ta wuce taji suna hirar 'yan gudun hijira dake zuwa daga jos, sai a yanzu ta tuna bata san ma garin da take ba.

"Unguwar gabas" taji wata mata ta tsaida abin hawa ta fad'a, kafin ya tafi itama ta shiga ciki tace "unguwar gabas nima zanje".

Sun gama ciniki zai kaisu a 200, tunani take idan taje unguwar a ina zata sauka.

Mutsu-mutsun 'ya'yanta taji a bayanta ta fara 'ko'karin kuncesu, ri'ke mata d'aya matar tayi ta kuncesu daga bayanta ta ri'kesu a hannunta.

" 'yan biyu Masha Allah, ni ina mamakin yanda masu 'yan biyu ke iya goyon biyunnan kuma basa takura?" Matar ta fad'a tana kallon Mardiyya

Kafin Mardiyya ta bata amsa cikin 'yan dakanni ta gama karantarta sannan tace "ai dake 'kananu ne shiyasa".

Basu sake magana ba har matar tace "na kusa sauka wani layi zaki shiga idan layi d'aya ne kinga sai a shigar damu ni layin ado mai hoto zan shiga".

Cije le'be Mardiyya tayi tace "bansan inda zanje ba, bansan ko ina a garinnan ba jin kin ambaci unguwar gabas ne ma ya sanya na biyoki, daga jos nake".

Cike da tausayawa matar tace "Allahu Akbar, ba dai wannan hatsaniya ta shafeku ba".

"Ta shafemu, na kwana biyu a garinnan bansan inda zan dosa ba ko akwai inda kika San zan samu masauki ko na haya ne?"

HASKEN RANA✔️Where stories live. Discover now