012

1K 95 2
                                    

Cikin sauri Mardiyya ta bud'e system d'inta ba tareda ta katse wayar ba.

"Basu saki a media ba wai kar su 'bata masa suna".

"Ban gane ba Sarah, idan basu saki a Media ba ta yaya kika sani?"

"Sa'ko suka turo mishi, kuma kinsan gobe zai tafi Thailand yanzu idan ya tafi cewa zasuyi ya gudu". Sarah ta fad'a tareda sauke numfashi

"Zanje na samesu naji ainahin maganar". Mardiyya ta fad'a tana laluba wardrobe zata d'auki gyale

"No bazai yiwu ba, sunyi al'kawarin bazasu fitar da maganar ba idan za'ayi settling d'inta silently, idan har kikaje a matsayin 'yar jarida zaki 'bata komai, kuma kinsan bazai yiwu kije a matsayin a matsayin 'ya ba".

A fusace Mardiyya tace "Sarah akan Abba fa muke magana babu abinda bazan iya yi ba, nayi wa wasu ma balle mahaifina? Nasan Abba lawyer d'insa zai tura wajensu ni kuma ban amince dashi ba, inaso naje a matsayin lawyer d'in Abba".

"What? Are you stupid?!" Sarah ta furta cikin sauri, ji take kaman ta shiga cikin wayar ta ri'ke Mardiyya domin tasan tunda ta sanyawa ranta to fa sai tayi.

"Of course I am not stupid,  idan har Abba ya fad'a musu zanje a matsayin lawyer d'insa babu abinda zasu iya yi sannan ai inada qualification ba wai ta hanya mara kyau zanbi ba".

"Mardiyya karki sake....." Katse kiran Mardiyya tayi ta turawa Abba text akan ya sanar musu lawyer d'insa zataje, d'auko ID card d'inta tayi na lawyer ta sanyashi a jakarta saida ta gama shiri tsaf tukuna ta tuna ashe fa tana da miji da sai ta nemi izninsa, yana zaune ya zuna mata ido.

"Umm... Hubby Abbana ne ya shiga 'yar matsala zanje na duba".

Murmushi yayi yace "to Mardiyya Abujan zaki tafi haka?"

"Abuja kuma?" Ta tambaya cikin mamaki, dariya yayi yace " 'kwarai, head office zakije na NNPC ko? A Abuja yake ki bari idan kin shirya sai ki tafi".

"Amma Abba...".

"Abbanki is fine, idan zaki tafi ai ba hakanan zaki tafi kai tsaye ba ko? Sai kinyi magana da Abba kinji me ya faru idan da evidence ma ya nuna maki".

"Naji amma kar ka koyamin aikina, nasan duk abinda ya kamata ba sai ka fad'amin ba".

Murmushi kawai yayi ya fita ya bata wuri, Abba ya kira ya tambayeshi me ke faruwa yayi masa bayanin komai.

Sun gama tsara komai nasu sannan ya koma cikin gidan ya sami Mardiyya tana zaune ta zuba tagumi tana kallon system d'inta, da alamu batada wata mafita kasancewar basu saki maganar a media ba balle a gani, balle ta bincika taga asalin maganar, an barta a duhu abinda tafi tsana.

Washegari da sassafe ta fara shiryawa tana yi tana kallon Mu'azzam dake danne danne a wayarsa baice mata komai ba, kaya ta d'iba tana zubawa a trolley still taga ya shareta, mamaki yake da bata ma tambayeshi ba ta hau had'a kaya, da alamu ko sallama bazata masa ba.

Tana rufe akwatinta wayarsa tayi 'kara, tashi yayi ya fita yana amsawa ta 'karasa had'e kayanta.

Sallamar Abba taji daga parlour cikin sauri ta fita tana murna, "Abba sannu da zuwa, tun jiya nake kiranka ka 'ki picking na turo maka text ba reply, yanzu kaga ma na shirya zan tafi muga sa'kon da suka turo maka? Waye ya turo me dame suka ce a ciki?"

Kallon Mu'azzam Abba yayi ba tareda ya amsa mata ba yace "naji tace zata tafi ina zata je?"

"Nima ban sani ba Sir".

Kallonshi tayi tace "jiya fa da kai muka gama maganar zanje Abuja Head office na NNPC akan maganar Abba".

"Mardiyya look at me, fad'a masa kikayi ko neman izninsa kikai?"

HASKEN RANA✔️Onde histórias criam vida. Descubra agora