Da sauri Mardiyya ta tashi ta ture Mu'azzam daga yarinyar, a tsorace ta kalleshi tace "hubby idan ka kasheta fa?"
Bai saurari Mardiyya ba ya saka 'kafa yana shurar yarinyar har saida ta farka, a firgice ta farka numfashinta na neman d'aukewa saboda tsabar firgici.
Kunce abin idanunta yayi Mardiyya ta kunce hannunta sannan tace "dan Allah hubby, please I'm begging you don't hurt her".
Kallon yarinyar kawai yakeyi amma tamkar taga mala'ika sai zabura takeyi, kwarjininsa ya fito 'karara ya fito mata a real S. S d'insa, fita yayi Mardiyya tabi bayansa tareda kashe fitilar d'akin ta kuma rufeshi, ruwa mai d'an sanyi sosai ta d'auko masa bai jira ta zuba a cup ba ya d'aga gorar ya shanye. Gaba d'aya Mardiyya ta rasa me zata masa domin itama a cikin 'bacin ran take sannan rabon da ta ganshi a wannan yanayi tun ranar da su Abba suka samu hatsarinnan.
Hannunshi ta iya kamawa tana massaging tareda furta masa kalmomi masu dad'i da sanyaya rai, janyota jikinshi yayi tareda sanya kansa a kafad'arta yana sha'kar 'kamshin jikinta da ke sanyashi cikin nishad'i a kowane lokaci. Sun d'auki time a haka sannan yace "a Ina Kika samota?"
"Naje na kar'bo hotunan Uncle a wajen Radiyya na biya gidan Sarah, a hanyar dawowa na had'u da ita ina tunanin yaran Uncle ne zasu kasheta".
Tashi yayi ya nufi d'aki ya cire kayan jikinsa ya sanya wata ba'kar muscle shirt da ba'kin wando, wani belt ya d'auko ya fito, zuba masa ido Mardiyya tayi domin b 'karamin kyau yayi mata ba amma ta kawar da wannan tunanin suka nufi d'akin horo tare, yarinyar na takure duk wanda ya ganta idan baisan abinda tayi ba sai ya tausaya mata saidai sam ba abar tausayi bace, yarinya ce da tayi sanadiyyar rayuka har uku sannan tayi sanadiyyar farin cikin mutane da dama, tayi sanadiyyar saka wasu cikin 'kunci da talaucin rayuwa yayin da ta halaka mutumin da ya kasance musu bango, Babu wanda yasan adadin mutanen da suka rasa abinci, makwanci, sutura da iyalai ta daliln rasuwar Dr Abubakar Wada.
Kujera yaja ya zauna gabanta yace "ya sunanki".
Shiru tayi tareda tura kanta cikin cinyoyinta a firgice, sake tambayarta yayi ta masa shiru ya d'aga belt d'in ya zabga mata a bayanta, a take jini ya fara fita daga wajen da dukan ya shiga yayin da ta saki wani firgitaccen 'kara.
"Idan har bazaki amsamin tambayoyina ba ki sani jikinki yana gab da komawa jini gaba d'ayansa, bazan sake tambayarki sau biyu ba ko dai ki amsa a na farko ko kuma ki fuskancu hukunci, ya sunanki".
" Nadiya" ta fad'a bakinta na rawa, sake matsawa dab da ita Mu'azzam yayi yace "menene ala'karki da Mansur?"
Shiru tayi sai kuma tayi saurin cewa " bansan ala'kata dashi ba, da farko na d'auka mahaifina ne saidai daga baya ya fad'amin shi ba ubana bane".
Video Mardiyya ke mata yayin da take fad'in maganar saidai tayi 'ko'karin 'boye fuskar mijinta. Cikin wata murya mai tsoratar da duk mara gaskiya yace "ki fad'amin yanda akayi kika sanshi da kuma abinda ya kaiki gidan Dr Abubakar I Wada, a ranar da gobara ta tashi a gidan".
" Da farko na zaci ubana ne domin yana yawan zuwa wajen mahaifiyata, wani lokacin idan yazo sai yayi kwana biyu kwana uku sai wata rana naji suna zancen yanda suka sameni ba ta hanyar aure ba, mahaifiyata tana Masa barazanar zataje garinsu ta fad'a idan har bai bata wani abu da takeso ba, a wannan ranar suka fita tare mama Bata fad'amin inda zasu je ba tacemin yanzu zata dawo, kwana na biyar banga mama ko mansur ba a rana ta shida yazo yacemin mama ta sauya gida ne domin ta gano ubana na ainahi shine Dr Abubakar, taje ta fad'a masa ya koreta shine shi mansur yazo ya tafi dani ya nuna masa.
Bayan ya gama fad'amin irin dukiyar da mahaifina ke da ita ya kaini gidan Dr Abubakar daga waje ya nunamin gidan sannan ya kaini gidan wata tsohuwa yace itace kakata babar Dr Abubakar, na kwana a can washegari ya d'aukemu ni da tsohuwar ya Kaimu har cikin gidan Abubakar, kafin mu shiga ya bamu wani abu muka sha yace tsari ne ko da Dr Abubakar zai so illatani.
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...
