Sarah tayi tunanin labarin da ta bawa Mardiyya zai sanya ta saku nutsuwa saidai tamkar sake 'karfafa mata tayi, tun ranar da sukayi maganar Mardiyya ta shiga sabon bincike duk inda take ajiyar evidence nata da wasu plots saida ta nemosu ta harhad'a, system ta nemi Sarah ta bata babu musu ta mi'ka mata.
Ta d'auki kwanaki tana bincike akan mahaifinta, kamfanoninsa, wanene akai yanzu, da kuma Dr Mansur.
Tana zaune tana buncikenta, taji an bud'e 'kofa bata waiwaya ba taci gaba da abinda takeyi, hugging d'inta taji anyi ta baya tareda zare hannunta daga kan keyboard d'in yace "Mardiyya stop stressing yourself".
Rufe idanunta tayi tana jin maganar na mata yawo a kanta, mamaki tayi ganin ta fara tuna lokutan da yake furta mata kalmar, dukkansu tana amfani ne da wayarta ko system kuma yanda yayi maganar yanzu haka yake mata a koyaushe, ba sai an fad'a mata ba a jikinta taji cewa mijinta ne.
A hankali ta juyo kanta ta zuba masa ido, yanayinsa ya nuna na mutumin da ya sha jinya saboda yanda idanuwansa suka koma ciki, ga fuskarsa alamun rama.
Murmushi yayi yace "i miss you too deedee na".
Wai meyasa kowa ke kiranta da nickname ne? Ba mamaki sunanta ya musu tsayi.
Hannu biyu ya sanya a 'kugunta ya d'agota daga zaman da tayi, juyota yayi suna facing juna yayi hugging d'inta tightly, Jim tayi sannan itama ta sa'kala hannunta a bayansa ta kwantar da kanta kan kafad'arsa, bata san yaya zatayi reacting ba kasancewar ta ma manta wanene shi, saidai yanda hankalinta ya kwanta tasan cewa tabbas shi wani sashi ne na rayuwarta, nutsuwa taji tana shigarta yayin da suke ri'ke da juna abinda ta manta rabon da taji nutsuwa kamar wannan.
Suna ri'ke da juna babu wanda yakeso ya saki d'aya kowannensu na cike da kewa, numfashi kawai suke ja suna saki har saida Sarah tayi sallama.
Sakin juna sukayi fuskarsa d'auke da murmushi ita kuma tata cike da tambayoyi, twins ya nufa yana shafa fuskokinsu Sarah tace "ka d'aukesu".
A hankali ya d'auki Hassana yana juyataz dukda sunyi wayo amma ganinta yake 'karama kuma bai iya d'aukar yara ba.
Dukkansu sunyi shiru Sarah tace "ya jikin naka?"
"Naji sau'ki sosai, tunda aka sanarmin anga Mardiyya Alhamdulillah jiki ya fara sau'ki, yanzu ina ganin tafiya zanyi tare da ita zata fi sakewa a can gida".
"To shikenan" Sarah ta fad'a tana kallon Mardiyya, 'karara farin cikin ya bayyana a fuskar Mardiyya domin ta gaji da zaman gidan Sarah dukda kwana biyu ta bata space d'in da take bu'kata dukda haka duk bayan minti 2-5 sai ta le'ko taga lafiyarta.
"Murna kike zaki tafi da mijinki ki barni cikin kadaici ko?" Sarah ta fad'a tana nuna fushin wasa.
Dariya Mardiyya tayi a karo na farko tunda ta samu kanta a wannan halin tace "Kar kiga laifina Sarah, overprotectiveness naki ne yayi yawa nasan kina sona amma kin 'ki barina nayi wani abu da zanji sau'ki a raina".
"Mardiyya kar kiga laifinta, ke kad'ai ce kika rage mata a duniya sannan kema kuma ta gama sanya rai kin mutu, rana tsaka ta tsinceki dole ne ta damu da duk yanayin da take ciki, da nine inaga 'daureki zanyi da rigata har sai na tabbatar kin dawo hayyacinki".
Barkwanci sukaci gaba da yi a tsakaninsu sannan Sarah ta tashi ta had'owa Mardiyya duk abubuwan da tasan zasuyi mata amfani suka tafi.
Dukda Mardiyya ta manta wanene mijinta amma sojoji biyu da ta gani a 'kofar gidan suka tabbatar mata yana harkan tsaro ne.
Sojoji biyun suka shiga gaba suna driving d'insu har gida, suna shiga gida Mardiyya ta zauna kan kujera tareda shafa kujerar, 'babu inda yakai gida dad'i' ta fad'a cikin ranta.

YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...