Afuwan sisters an mana haihuwa ne jiya akayi suna an samu baby boy that's why am very busy these days, here is an update, love you all😍😍
*NB: Idan kun tuna Mu'azzam na bawa Mardiyya labarin abinda ya faru ne baya, so na tafi complete flashback ne saboda Kar nayita gutsira labarin, akwai wuraren da zasu zama a little confused saboda Mardiyya bata tuna su ba amma na rubuta su, so ko da zaku ga na maimaita abu it's still in the story.*
*END OF FLASHBACK*
Shiru mardiyya tayi tana consuming abinda Mu'azzam ya fad'a mata, tagumi ta zuba ta runtse idanunta tana so ta tuna menene ya faru dab da barinta garinsu? Mu'azzam ya sanar mata taje had'uwa da wasu ne shikenan ba'a sake samun labarinta ba, ko da yaje wurin yaga gawar Radiyya wadda a yanda ya fad'a itace wadda zasu had'un, waye ya kashe Radiyya? Ko dai itace ta kasheta ta gudu?
Tsoro ne ya fara ziyartarta cikin sauri ta tashi ta d'auko flash drive d'in da yayi sanadiyyar rayuka ta ri'keshi a hannunta, a tsorace tace "Hubby........ Idan har na fahimci abinda kake nufi wannan flash d'in shine abinda naje kar'ba wanda daga shi baa sake ganina ba, kenan ni na kashe Radiyya saboda wannan abin? Ko kuma.... "
Rawa bakinta ya fara Mu'azzam ya dafa hannunta yace "a'a Mardiyya baki ta'ba kashe kowa ba kuma na tabbatar bazaki ta'ba kashe kowa ba, mutumin da suke tareda Radiyya na nemeshi ban sameshi ba wanda shine wanda ya baki flash d'innan, sannan a tunanina indai y gudu ya rabu da Mansur to wad'anda suka kashe Radiyya su Mansur ne".
" A duk lokacin da na jona wannan abin yana tracking inda nake, kenan Mansur yana sane da wannan mutumin yana sa masa ido ya kuma san da wannan flash d'in wanda haka ne yasa yake tracking d'insa, meyasa bai 'kwace flash d'in ba tunda yanada iko da mutumin sannan ba sai ya wahalar da kansa ba akan haka? "
" Nayi wannan tunanin nima Dee-dee amma abinda na lura shine flash d'in yanada password da Mansur ya kasa ganewa sannan. Kuma ya kasa samun wanda zai cire masa, shiyasa yake tracking abin yana jira mutumin ya jonashi, idan aka budeshi duk abinda ke ciki to wanda ke tracking d'in zai iya gani shiyasa yake tracking d'insa, idan har ba cire wannan tracker d'in akayi ba aka cire password d'in dake kai bazamu iya ganin komai ba, idan ma mun gani to danger d'in da zamu shiga tafi wannan, zasu san inda muke sannan zasuyi sau'kin illata mu musamman a yanzu da kika manta komai".
Numfashi Mardiyya taja tace " na manta komai na baya amma nasha wahalar da bazan manta da ita ba a yanzu, ko dan wannan wahalar da nasha Ni da 'ya'yana bazan iya sassautawa ba".
Murmushi yayi yace " kinanan a yanda kike, shikenan zamu fara da step na farko shine Nadiya, tana gidan Goggwo tun bayan tafiyarki na kaita saboda haka ita ba matsala bace inada tabbacin kuma bazata gudu ba domin bata da wurin zuwa, next step namu shine nemo dangin mahaifinki, idan har muka kama Mansur muka kaishi kotu ba tareda munsan inda dangin mahaifinki suke ba, tamkar munyi tufka da warwara ne zai dinga yaudararmu dasu ya hanamu samun nasara, a yanzu Mansur yana kan dukiyar mahaifinku ba tareda damuwa ba, zamu barshi a hakan mu fara neman family d'in Abba, idan muka ganshi da mu da su zamu had'u mu ya'ki Mansur".
"yaushe zamu fara nemansu kenan?" Ta fad'a tana juya flash d'in hannunta domin ita bata 'ki a gama komai a yau ba domin tasan gaskiyar lamarin ta lura duk yanda take tunanin munin abin ya wuce haka, wace irin rayuwa muke ciki haka da zaka kankane dukiyar wani kace ta zama taka? Da ace shi mutum na gari na ba sai ya bi wannan hanyar ba da hannunsu zasu dan'ka masa dukiyar domin basuda ilmin juyata saidai ta lalace, amma ya nuna maitarsa a fili gashi baya komai sai dur'kusar da dukiyar.
"Mardiyya kin fiye gaggawa kuma kinsan ance gaggawa daga shaid'an take, ki samu nutsuwa da kanki zaki tuna wasu abubuwan daga nan sai mu san ta inda zamu fara neman dangin mahaifinki, domin ke kad'ai ce mai masaniyar inda zamu iya samunsu kece kawai kike tattaunawa da Abba a kansu ko Sarah batada masaniya kaman ke, ki huta ki samu nutsuwa memory d'inki ya fara dawowa tukuna".
أنت تقرأ
HASKEN RANA✔️
غموض / إثارةwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...