"ya sunanki?"
"Nadiya Muhammad"
"A cikin garinnan kike zaune? Ina iyayenki suke".
" Eh ni 'yar garinnan ce, mahaifiyata ta rasu bansan mahaifina ba".
" Kinada wasu dangi ne da suka rage?"
" Bansan kowa a dangina ba".
"Kinsan wancan mutumin? "
" Eh na sanshi, yana zuwa gidanmu lokacin da mahaifiyata take raye".
Tafa hannu barrister sabir yayi yace "well done Nadiya kinyi 'ko'kari, yanzu zan 'karasa miki tambayoyin nasan ma kin haddacesu a kanki. Indai kika amsa tambayoyinnan sune zasu dawo a kotu kina amsawa shikenan fa ba wani wahala".
Idanunta ne suka ciko da 'kwalla tace " barrister ance idan mutum yayi kisa ratayeshi akeyi yanzu nima rataye ni za'ayi har sai na mutu? "
" A'a Nadiya ko da za'a zartar moki da hukunci baza'a kasheki ba balle kuma rataya, hukunci yana kan wanda ya tilasta miki ne kika aikata hakan, ke kuma za'a dan'ka ki hannun gwamnati ta kula dake".
" Gidan marayu za'a kaini kenan? "
Shiru yayi bai bata amsa ba domin yasan idan yayi mata bayani ma bazata gane ba, ta sanya gobara har ta kashe mutane wannan abin Dole zaiyi affecting 'kwa'kwalwarta hakan yasa had'ata da sauran yara da suke innocent bazai yiwu ba sai tayi undergoing some processes.
"Dafata yayi yace inaso ki san wani abu Nadiya no matter what bazamu barki haka ba zamu taimaka miki ko da bakya hannunmu".
" Inaso naci gaba da zama. Da gwoggo". Ta furta tana goge hawayen da ya wanke mata fuska. Rarrashinta barrister sabir keyi domin ya kwantar mata da hankali kafin shiga kotu wanda yake saura kwana biyu.
A kwana biyun da suka rage kullum sai Barrister yaje ya yiwa Nadiya rehearsal, yayi mamaki da bakinta ya fara rawa yayin da take maimaita labarin a karo na kusan goma, rubuta mata yayi a paper yace taci gaba da dubawa har gobe ranar da za'a shiga kotu kenan.
A kotu bayan an sake maida bayanai aka kira Nadiya ana tambayarta, bayan ta gama fad'in sunanta da inda take barrister sabir yace "kinsan wannan mutumin".
Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace " ban sanshi ba".
Gaban Mardiyya saida ya fad'i domin batayi zaton hakan ba, kallon Nadiya takeyi saidai Nadiya ta d'auke kanta daga garesu tsoro ya bayyana tattare da ita.
Sake maimaita mata tambayar akayi ta sake cewa bata sanshi ba, cikin hikima da 'kwarewa alkalin yace "a ranar Asabar 21 ga watan mayu shekarar 2014 kin shiga gidan Dr Abubakar I Wada, hakane?"
" A'a". Ta fad'a muryarta na rawa, dafe kai Mardiyya tayi a ranta tace 'Nadiya kina neman saka kanki a matsala'.
Maimaita tambayar barrister yayi Nadiya ta sake denying shi kansa jikinshi yayi sanyi ya fara tunanin me Nadiya ke tsoro da zata yi hakan?
Komawa lawyer d'in yayi ya zauna lawyer d'in Mansur ya tashi, bayan ya gabatar da kansa ya nuna su Mardiyya yace "Nadiya kinsan wad'ancan?"
"Eh" ta fad'a tana kallonsu a tsorace, murmushi yayi yace " karki tsorata Nadiya nan kotu ce babu wanda yake da ikon cutar dake, zaki iya fad'awa kotu a ina kika san wad'annan mutane?".
" Bayan mahaifiyata ta rasu waccan da mijinta sun ganni a hanya suka d'aukeni suka kaini gidansu".
" Daga nan kuma me ya faru".
Gaba d'aya jikin Nadiya rawa.
yakeyi har wani layi take a tsaye alamun tasan girman abinda take Shirin aikatawa sannan tace "bayan sun d'aukeni sun 'kulleni a wani d'aki suka bani wannan takardar sukace zasu kaini kotu sunaso na fad'i abinda yake cikin takardar, ko.....um ko kuma.....".
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...
