*sumayya Abubakar* shine sunan dake rubuce a 'kasan hoton 'yar jaridar, cikin sauri Mansur yayi zooming hoton domin yaga kamanninta saidai hoton yayi duhu da yawa.
"Inada tabbacin itace Abbas, inaso a bincika min komai nata a cikin gaggawa, wannan yarinyar tana neman tsaidamin komai".
Abbas amsawa kayi yayi da to ya d'auki kayansa ya fice, cikin kwana biyu ya samo inda sumayya ke aiki da address d'in inda take zaune ya turawa Mansur.
*********
Mardiyya na zaune ta zubawa Mu'azzam ido yayin da yake ta zuba zance akan babyn abokinsa da yaje ya gani dukda tasan inda zancen ya dosa amma tayi kamar bata fahimta ba.
Hamma tayi tace "wannan zancen naka har ya fara sakani gyangyad'i Hubby, Allah ya raya babyn".
"Ameen" shiru yayi sannan yace "Mardiyya nima fa na 'kagu naga jariri ko jaririyata a hannuna please yaushe zaki bani?" Ya 'kare maganar yana turo baki tareda langa'be kai kaman yaro, dariya tayi tace
"Duk ranar da Allah ya kawo, kuma kaima ai da laifinka a shekara d'ayan da mukayi watanni nawa kayi a gida?" Ta 'kare maganar tana had'e rai tareda d'aga gira.
Gyara zama yayi yace "hakane fa, amma yanzu ai na dawo gida kuma bana tunanin zanyi aiki a watanni uku masu zuwa banda na...um never mind yanzu dai sai mu fara sabon Honeymoon".
Shafa cikinta tayi tace "u'um ban shirya ba ni ambaton baby ma tsoro yake bani".
Murmushi yayi ba tareda yace mata komai yana tunanin wannan auren nasu, aure ne da akayi domin ya zame mata kariya wanda a yanzu ya fara tunanin meyasa ya amince? Gasu nan dai zaman aure sukeyi amma babu wani armashi cikinsa, mafarkin da ya jima yana yi akan matar da zai aura duk ya ruguje, Mardiyya batada wani tunani da ya wuce Abbanta da yanda zata fidda shi daga matsala yayin da shi bata masa ma kallon miji.
"Tunanin me kakeyi?" Ta fad'a tana kallon idanuwansa, kafin ya amsa tace "na fahimta zancen Babies da akayi ne ya 'bata maka rai ko? Hubby ba wai banason haihuwa dakai bane kawai Ina tunanin....."
"Na fahimta Mardiyya kina tunanin idan kika samu ciki zai shiga cikin aikinki, na fahimta nima lokacin da zanyi aure nayi tunanin auren zai hanani wasu ayyukan amma yanzu naga duk ba haka bane, ba wannan nake tunani ba zamanmu gaba d'aya nake tunani".
"Kamar wasu strangers, shekara guda mun kasa warwarewa mu zama normal couples...Ni kaina hakan na damuna kuma nasan laifina ne, banida wani tunani sai na Abba da kasuwancinsa". Ta fad'a tana wasa da yatsunta.
Tashi yayi ya koma gefenta yace "ba laifinki ne ke kad'ai ba harda nawa, nayi kusan 6 months bana gari amma yanzu sai muyi 'ko'karin gina rayuwarmu, zan ajiye aikina a gefe na d'an lokaci kema inaso ki ajiye komai mu fahimci juna".
Tan'kwashe 'kafarta tayi tareda juyawa tana facing d'insa kan kujerar sannan tace "naga a movies da novels ana fara fahimtar juna ne ta hanyar fara sanin juna da tambayoyi, yanzu nasan sunanka, best food d'inka, nasan kakarka da kake zaune a wajenta amma ban san siblings d'inka basu kuma ta'ba zuwa ba, nasan aikinka, shekarunka, kayan da kafi son sanyawa, lokacin da yafi maka dad'i, abinda ke 'bata maka rai, ....bansan menene ban sani ba a kanka".
Dariya yayi tareda zama yanda tayi yace "nima na sanki, na san family d'inki, aikin da kikeyi, abinda kika fi so a rayuwarki, bansan best food d'inki ba saboda duk abinda ya miki dad'i kina cewa shine best food d'inki, bansan me yake sanyaki farin ciki ba".
"To mu fara da kai, ka fad'amin a hannun kakarka ka tashi a wani gari daban ba Kaduna ba, amma iyayenka fa?"
"Umm iyayena suna nan amma suna nesa ne sosai inada 'kanne biyu wad'anda zan iya tunawa mace da namiji amma yanzu nasan akwai wasu da ban sani ba".
"Meyasa baka zuwa gidan naku? A tunanina ba'a ganin nisan gida, Abbana yana cike da damuwar manta family d'insa da ace yasan inda suke da ko duk abinda ya mallaka zai 'kare sai ya je garesu".
Shiru yayi kansa ya d'auke kansa ba tareda ya bata amsa ba itama bata nemi ya amsa mata ba, sunyi hira sosai bayan haka sun sake fahimtar junansu.
Bayan ya fita masallaci Mardiyya ta d'auki wayarta ta kira Abba ta tambayeshi ko akwai wani shiri da Mansur keyi Abba yace babu hakan ya matu'kar sanyata a damuwa domin tasan Abu d'aya yakeyi, shine nemanta wanda hakan zai iya jefa wasu mutanen a cikin had'ari.
Internet ta hau ta fara bincike akan Abbanta, abinda ya tsorata ta shine duk inda sunan Abba ya fito to tabbas na Mansur Yana biye dashi, duk wani hoto na Abba akwai mansur a ciki abin takaici dukka hotunan ya du'kar da kansa cikin ladabi tamkar kare da uban gidansa, ashe mugunta yake shiryawa.
Babu wasu bayanai da suka nuna Mansur ba mutumin kirki bane saidai ma yanda ake yabon Abba haka ake yabonsa, dafe kanta tayi tareda sakin sauti cikin fushi tace "Abba ya amince da mutuminnan, ya yarda dashi yarda da har takai yana 'boye laifukansa meyasa zai ma Abba haka?"
Cigaba tayi da dubawa bata samu wani bayani ba akan ala'kar Abba da Mansur ba har ta ha'kura.
***********
"Fita ka bani wuri" Mansur ya fad'a a fusace, da sauri mutumin dake bayansa ya fice cikin sauri.
Bayan an bincika Sumayya da akayi aj tabbatar masa batada ala'ka da Dr Abubakar domin babu abinda ba'a samo masa a kanta ba.
"Nasan hanyar da Zan bi" ya fad'a tareda murmushin mugunta sannan yace "idan kasan wata hanyar baka san wata ba sai muga ta yanda zaka kaucewa wannan tarkon nawa".
Birthday d'in Abba na shekaru 62 cikin kwanaki biyu ne saboda haka Mansur ya fara binciko hotunan da yayi tareda Abba tun na baya wanda yake ta ajiyarsu a baya ba tareda yasan amfaninsu ba yau ga amfaninsu yazo.
Ranar birthday d'in Abba 1am Mansur ya d'auki hotunan da sukayi, wanda sukayi farkon had'uwarsu lokacin basu fi shekaru 12 ba, sannan wad'anda sukayi yayin da suka fara sana'a har zuwa na zamani, editing d'insu yayi ya had'a da na zamani ya d'aura a Twitter ya rubuta *happy birthday brother* sannan yayi tagging Abba a hoton ya rubuta *little bro*.
Wannan hotuna sun tada zaune tsaye domin maganganu mutane suka fara wasu na mamaki wasu na fad'in yanda ake ganinsu tare dama da wuya idan ba 'yan uwa bane mutanen da basu amince ba kad'an ne.
Kafin gari ya waye 'yan jarida masu jiran kad'an da 'yan social media masu jiran 'kiris suka fara yad'a zancen, ko da Abba yaga hoton murmushi yayi yana tunanin 'karamin abu ne saida yaga hirar da akayi da Mansur wanda ya bada labarin asalin kafuwar kamfanonin M&S ya sanarwa da Media cewar kamfanin an ginashi ne da sunansu wato MANSUR $ SADIQ, sannan asalin kamfanin sun fara shi ne da 'karamin shago da mahaifinsu ya bar musu, kasancewar Abubakar ya fishi maida hankali da 'kwazo akan harkar kasuwanci yasa kamfanin ya zama a hannunsa.
Maganganu ne ya yisu wanda zasu zarce duk tunanin me tunani, duk 'kwa'kkwafinka bazaka ta'ba cewa 'karya ya fad'a ba domin ya fad'i abubuwan da babu wanda ya sani game da Abba wanda Kuma suke gaskiya ne.
Mardiyya na ganin hirar ta nufi gida tayi rashin sa'a Abba baya gari, zama tayi suka d'an tattauna da Mama saidai ita Mama batada wani abun cewa saidai tace "Allah yana tare damu".
VOCÊ ESTÁ LENDO
HASKEN RANA✔️
Mistério / Suspensewacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...