013

987 111 12
                                    

Mu'azzam ta kira ta sanar masa abinda ke faruwa cike da damuwa yace

"Ina kika je? Meyasa baki fad'amin ba? Su waye ke binki?..." Tambayoyi yake jero mata daban-daban saida ta katseshi tace "na fara tsira da rayuwata tukuna sannan na amsa duk tambayoyinka".

"Ina zuwa". Katse kiran yayi cikin mintina kad'an ya kirata yace "anyi tracking numberki yanzu ma'aikatan tsaro zasu zo suyi escorting d'inki gida".

Bata amsa ba taci gaba da gudu dukda gajiyar da tayi cigaba sukayi da zagaye, tayi mamaki da basu zagaye ta ba idan har ranta suke so ko kamata suke so suyi.

Daga nesa ta jiyo 'karan motar police da gudu ta nufi wurin kafin ta isa motocin da ke binta har sun 'bace tamkar babu su, gaisawa sukayi da ita suka mata rakiya.

Wasu sun tafi yayin da wasu sukayi gadinta har zuwa gari ya waye.

Tana shiga Mu'azzam ya kirata ya fara mata fad'a dukda ta sanar masa abinda ya faru, ganin bazata yi riba ba ya sanya ta kar'bi laifinta ta kuma bashi ha'kuri.

Bata samu kiran Abba ba sai da gari ya waye, kiransa ta fara gani lokacin da take 'ko'karin kiransa tana sallama yace,

"Mardiyya kina lafiya dai ko? Babu wanda ya biyoki gida?"

"Babu wanda ya biyoni Abba, kuma police sun zauna sai yanzu suka tafi".

Numfashi ya sauke tare da hamdala yace "karki sake irin wannan gangancin kinji ko? Da sun kamaki salwantar maki da rayuwarki zasuyi".

"To Abba, ya akayi da mutumin?"

"An kaishi asbiti suka ce poison ne yasha, ma'aikacin da ya kawo mana drink d'in kuma an nemeshi an rasa sannan babu wani alamu da zasu nuna wanene, restaurant d'in sunce basu sanshi ba kuma an tara duk ma'aikatan wajen babu shi".

"Ya salam, Allah ya ji'kansa yasa ya huta, baice komai ba ko?

Shiru Abba yayi na d'an lokaci sannan yace "eh".

"Ina Mama?" Mardiyya ta tambaya domin kawar da zancen, hira suka yi sannan ta katse wayar tana tunani akan wannan lamari, daga muryar Abba tasan cewa akwai matsala.

Mutuwar manager ta sake sanya al'amarin ya lalace domin baya raye kuma shine da laifi, Still Abba ne ya d'auki blame d'in.

Wannan al'amarin ya sanya kasuwancin Abba dur'kushewa sosai, duk wani shige da ficensa an sanya masa ido ga business d'in collapsing yakeyi.

A cikin shekara d'aya Abba ya rasa kaso mai girma na kasuwancinsa, dukda yasan wanene yake masa wannan zagon 'kasa amma bai nuna ba saboda iyalinsa.

Ta 'bangaren mansur kuwa maimakon yayi farin ciki sai 'karin ba'kin ciki da yakeyi, duk lokacin da ya raba Abba da dukiyarsa wannan kud'in basa masa albarka, duk yanda yaso ya gina kansa ta hanyar lalata kasuwancin Abba hakan yaci tura har takai ga ya saida d'aya daga cikin kamfanonin da Abba ke ta'kama dasu a China.

A wannan lokacin ne Abba ya gayyaceshi gidansa, hira suke yi ta abokai tamkar babu abinda ke faruwa.

"Kaga abinda yake faruwa damu ko?" Abba ya fad'a yana fuskantar Mansur, d'aga gira mansur yayi yace "na me fa?"

"Na lalacewar dukiyarmu, a yanzu abinda nake da shi a 'kasa baikai abinda nayi asara ba".

Murmushi Mansur yayi yace "to ai dama kasuwanci ya gaji haka, ka godewa Allah da ka tara wannan dukiya har kayi wannan suna ka zagaye Nigeria da wajenta, ni ka duba tun farkon kasuwancina na kasa zuwa ko ina haka duniya take ai, kaga ni kuwa a yanzu Allah yana bud'a min Ina shirin bud'e babbar plaza a kebbi".

Shiru Abba yayi sannan yace "hakane ita rayuwa haka take, to amma abinda nake tunani shine kamar mutanen dake kusa dani ne ban samu masu adalci da amana ba".

HASKEN RANA✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang