Cikin ikon Allah a wannan lokacin Mansur ya fara samun d'aukakar da yake nema, dukda cewa Abba ya hanashi shiga harkar kasuwancinsa amma hakan bai hanashi cusa kai ba saboda yasan Abba bazai ta'ba fitowa yace 'karya yake ba.
A cikin wannan lokaci Abba kuma fafutuka yake akan ya mallakawa 'ya'yansa kamfanoninsa gaba d'aya, dukda cewa sunayensu ne akai amma yasan sharrin Mansur saboda haka duk kamfanoninsa dake 'kasar waje ya kaisu ajiya bankunan dake 'kasashen tareda bada sunan Mardiyya da Sarah a matsayin mamallakan kamfanonin.
Duk abubuwan da Abba keyi bai sanarwa kowa ba har lawyer d'insa domin bai amince da lawyer d'in nasa ba, sabon lawyer yayi bature a England wanda a yanzu shine ke sane da komai nashi.
Yayin da Abba ke fafutukar nemawa iyalinsa 'yanci Mansur yana gefe guda yana neman haram da sunan Abba, cocaine ya fara shigowa da ita a 'boye wadda ta kawo masa riba mai yawa.
*********
"Ya kamata muci abinci a waje yau" Mu'azzam ya fad'a yana kalba da gashin Mardiyya, amma masa tayi da "um" tana lumshe idanunta.
Sakin gashinta yayi tareda d'agata daga cinyarsa yace "oya tashi ki shirya".
"Kai Hubby....." Ta fad'a cikin shagwa'ba tareda buga 'kafarta a 'kasa sannan ta koma ta kwantar da kanta a cinyarsa taja hannunsa ta d'aura a gashinta.
"Saura kad'an nayi bacci fa dan Allah cigaba dad'i, zanyi mana na yanzu muci na dare sai mu fita".
"Okayyyyy". Ya furta tareda cigaba da murd'e mata gashi tana lumshe idanunta, sun jima a haka har ta fara gyangyad'i sannan ta bashi comb ya taje mata kan nata.
Gashinta yana masa dad'i a hannu baya gajiya da shafawa musamman idan tana lumshe ido tana sakin d'an sauti alamun tana jin dadi.
"Ya Abbana" ta fad'a tana gyara kwanciyarta fuskarta na kallon tasa.
"Ke zan tambaya ai ya Abbanmu yake? Yana lafiya? Ya Mama? Ya Sarah?"
"Kowa yana lafiya, amma ba wannan nake nufi ba kaga Abba fa yanzu baya cemin komai yanzu sannan account d'insa da nayi hacking ma yanzu bana ganin komai".
Hancinta ya lakace yace "saida nace karki sake hacking account d'in wani ba tareda izni ba sannan karki damu Abbanki lafiya lau yake".
Numfashi taja tace "Hubby inaji a jikina akwai abinda ke Shirin faruwa, Abba yayi shiru haka shima d'ayan yayi shiru baka tunanin wannan babban Abu na neman faruwa? Banaso wani abu ya samu Abbana ko Mama ko Sarah".
Brush comb ya sanya yana taje gaban gashinta yace "ki kwantar sa hankalinki kinji Mardiyya, babu abinda zai faru sai alkhairi".
Zumbur ta tashi tareda had'e gashinta ta tufke da ribbon tace "muje cin abincin ko? Dan na fara jin yunwa".
"Kika ce sai dare?"
"Tunawa nayi gobe inada aiki".
Bayanta yabi suka shirya tare suka fita cin abinci, ta hanyar gidansu ta wuce ta zuba ma window ido, rabonta da gida wata biyu kenan Abba yace kar taje saboda tsoron kar wani abu ya faru.
"Plate d'aya". Ta fad'a tareda kallonsa ta gefen ido
"A'a biyu".
"A'a d'aya, sai muyi order d'ayan ma d'aya".
"Okay" ya fad'a tareda sallamar waiter d'in dake tsaye yana kallonsu suna musu akan abinda sukeso.
Mintina kad'an aka kawo musu abincin, ci sukeyi a hankali ta kalli plate d'in sannan ta de'bi abincin a spoon ta bashi a baki, ciyar da juna sukeyi har abincin yazo 'karshe sannan suka fara kokawar wa zaiyi lomar 'karshe, kowa da abinci a spoon d'insa amma da zarar d'ayansu yakai spoon d'in baki d'ayan zai janye, dariya sukeyi suna cike da walwala har suka gama cin abincin suka baro wajen, ko da suka shiga mota gasar wa'ka suka fara har suka je gida.
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...
