Dake zuciyarta tayi suka shiga ma'kabartar tare, a kusa-kusa 'kabarin su Abba yake.
Dur'kusawa sukayi suka musu addu'a suka fito, "mutane nawa ne suka rasu a gobarar?" Baba ya tambaya yana sake kallon ma'kabartar Mardiyya tasan tabbas akwai abinda baba yake tunani ta maida hankalinta gareshi.
"Anyi dace gaskiya su ukun ne suka rasu ragowar wasu sun d'an samu raunuka kad'an wad'anda ke waje kuma basuji ciwo ko kad'an ba". Mu'azzam ya fad'a Cikin girmamawa.
" Kayi magana da wad'anda suka samu raunukan ne?"
Girgiza kai Mu'azzam yayi yace " a'a Mansur a lokacin ya hana ko da 'yan jarida magana dasu sannan shi ya d'auki nauyin kula da lafiyarsu har suka warke, lokacin da nace masa inason magana dasu yacemin an sallamesu duk sun koma garinsu, har yanzu ban samu wani labari daga garesu ba sannan a wannan lokaci ya fara nufar Mardiyya da sarah da sharrinsa wanda ya sanyani kaida hankali a kansu".
" Baba dan Allah meyasa kake wad'annan tambayoyin? Maganganunka Baba suna sanyamin shakku akan rasuwar iyayena". Mardiyya ta fad'a 'kwalla na cikowa a idanunta
Dafa hannunta yayi yace "tabbas a jikina inajin cewa d'ana yana raye, nayi addu'a na kuma bincika naji tabbas yana raye saidai yana ina? Idan har ba shi bane a kwance anan Ina yaje tsawon shekarunnan?"
Kallonshi sukeyi dukka su biyun domin basu fuskanci inda zancensa ya dosa ba, anya kuwa baba malami ne na gaske ko kuwa dai Yana kauce hanya? Anya ba aljanu ke neman cusa Masa 'karairayunsu na banza ba? Wannan shine tunanin dake yawo a 'kwa'kwalwar Mardiyya.
"Nasan zaku fara tunanin maganar da nayi muku ko 'karya ne ko Kuma shirka ce, inaso ku sani bana shirka amma ni malami ne gangaran nayi karatun Allo na 'kureshi, ilimin da Allah ya bani cikin wannan karatu dashi nayi amfani, bazan muku 'karya ba iyayenku suna raye saidai Allah mahaliccinmu kawai yasan inda suke, zaku iya gane inda suke idan kukayi amfani da ilminku na zamani kaman yanda nayi da ilmina na litattafai".
Mardiyya mutuwar tsaye tayi yayin da Mu'azzam ke 'ko'karin danne nuna mamakinsa, tunani ke yawo cikin kansa daban daban saidai dukkansu babu amsa.
Cikinn sauri yace da Mardiyya "muje na maidaku gida akwai wurin da zanje".
Da'kirewa Mardiyya tayi tace "hubby gida fa kace? Bayan kanaji Baba yace iyayena suna raye? Bazanje gida ba har sai naga iyayena".
Gaba baba yayi ya barsu a tsaye Mu'azzam cikin rarrashi yace "Mardiyya nasani nima bazan samu nutsuwa ba idan har banga Abba ba amma ki kwantar da hankalinki idan har Abba na raye har tsawon lokacinnan kuma Baba ya gano yana raye to yana cikin safety, ki koma gida akwai wanda zanyi contacting ne ya had'ani da d'aya daga cikin ma'aikatan gidanku mata, duk information d'in da na samu daga gareta zan fad'a miki".
" Aa bazan koma gida ba Hubby tare dakai zamuje".
Hugging d'inta yayi yace " babyna ki koma gida twins are waiting for you".
Zata sake magana ya d'ora hannayensa a kan lips d'inta yace "ki dena ja inja dani okay? Abinda na fad'a shi za'ayi I'm not changing that, ki koma gida ki zauna da twins zan kiraki when I found something". Yayi maganar cikin bada umarni, yanda ya had'e girar sama da ta 'kasa yasa sam ta kasa yimasa musu domin kwarjininsa na ma'akacin tsaro ya bayyana.
Tura baki tayi tareda yin gaba ta barshi a wurin, murmushi yayi tareda girgiza kansa yace "Mardiyya wani lokacin kamar 'karamar yarinya".
Driving yake yana kallonta ta gefe amma ta'ki yarda su had'a ido ita a lallai fushi takeyi dukda tasan gaskiya ya fad'a, wad'annan abubuwan dake faruwa sun hanata samun isasshen lokaci da yaranta, idan tana gida suna nuna kewarta da sukeyi ita kanta batason hakan saidai 'bangarenta jan'yar jarida ta tsani ayi abu ba a gabanta ba, tafiso komai ayi a kan idanunta.
KAMU SEDANG MEMBACA
HASKEN RANA✔️
Misteri / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...