Hannu d'aya Mansur ya sanya ya dafe kansa d'ayan kuma yana d'aga musu alamun su dakata, dariya sukayi tareda zagayeshi d'aya daga cikinsu mai suna tukur yace "ka Gane ni? Ka tuna lokacin da ka rabani da mahaifiyata na tsawon lokaci? Ni kad'ai ne ke taimaka mata amma ka tilastamin na gujeta na bika ina maka aikin bauta, ganinta da ban sake Yi ba kenan har yau shekaru bakwai kenan, wallahi d'acin da ka Sanya naji da wahalar da ka saka na sha hannun yan sanda har sukamin karaya biyu sai na rama a kanka".
Yatsan Mansur ya kama ya murd'e tsabar azaba saida Mansur ya saki 'kara amma abin mamaki cell d'in dake kallon nasu da na gefe duk ko jikinsu.
Sakin hannun tukur yayi yayin da aka zo bud'esu Mansur kuwa gumi kawai yake had'awa tsabar azaba, gandrobar da ya bud'e musu d'akin d'auke Kai yayi kaman ma baiga halin da Mansur ya shiga ba domin yasan halin wad'annan mutanen, duk wanda aka yankewa life imprisonment to duk imaninsa da tsoro da wani fargaba an kwashe, iskancinsu sukeyi son ransu ganin dama makomarsu ta duniyar da lahirar d'aya ce, daga ma'aikata har 'yan uwansu prisoners babu wanda ke shiga harkarsu idan ba haka ba saidai a tsinci gawarka ko kuma a d'aukeka sumamme, babu yanda za'ayi dasu domin ko aiki aka 'kara musu saidai su saka marasa galihu a wurin yi.
Tasa 'keyar Mansur sukeyi tamkar an kama 'barawo yana tafe yana tangal-tangal ragowar mutanen nayi masa kallon tausayi domin tunda wad'annan samari uku suka shiga prison duk wanda aka had'asu d'aki d'aya sai an fitar dashi, mutum d'aya ne ya juri zama dasu shima sharri akayi masa aka kawoshi.
Suna fita filin da zasuyi aikin gona suka tunkud'a Mansur ya fad'i 'kasa tareda buga goshinsa, yekuwa sukayi suka tattaro 'yan uwansu sholi ya taka bayan Mansur yace "kunsan waye wannan? Nasan ba lallai ku sanshi ba amma kunsan Dr Abubakar shahararren mai kud'innan? Wanda duk shekara yake zuwa da 'kafafunsa wannan kurkuru ya fitar da masu 'kananun laifi, ya bimu d'aya bayan d'aya yana raba mana abinci mai rai da lafiya? Nasan wasunku sun sanshi sabbin zuwa kuma ba lallai su sanshi ba, wannan da kuke gani abokinsa ne, munafuki ne azzalumi ne babu abinda yakeyi sai zaluntarsa, ya jima yana tsara yanda zai kasheshi a lokacin muna yaransa, to a yau gashi me Sama ya had'amu a inuwa d'aya, kai d'ago ka fad'a musu laifukan da kayi".
Mansur bai ta'ba tunanin zai fuskanci irin wannan cin mutuncin ba saidai har yanzu bai fidda rai ba yasan watarana wani zaizo ya cireshi daga wannan 'kangin, d'agoshi sholi yayi ya sha'ke masa wuya har saida ya amince zaiyi magana.
Zayyano yanda ya kashe Mansur yayi sannan ya fara fad'ar yanda yake umartar samari irinsu suna aikata ayyuka marasa kyau da zasu kaisu ga halaka, yana gamawa sholi yace "to 'yan uwana kunji fa, a cikinmu mutum nawa ne suka aikata laifukan da ya zayyano kuma umartarsu akayi?"
Kusan dukka mutanen wurin saida suka d'aga hannu, gefe ya koma yace "gashinan ku masa rabin dukan da akayi muku a wannan gida domin banaso ya mutu, ku huce haushinku a kansa domin a lokacin da ya jefomu tsaka mai wuya Yana can yana holewa da dukiya ko a jikinsa".
Tamkar jira sukeyi sholi na gama magana suka rufe mansur da duka, tun yana karewa har ya fara basu ha'kuri saidai ya manta zuciyoyinsu sun 'ke'kashe basu san tausayi ba domin suma ba'a nuna musu ba.
Sun fitar dashi hayyacinda gaba d'aya kayan jikinsa sun yayyage ga jini ta hanci ta baki, duk ma'aikacin da ya matso da hannu d'aya sholi ke dakatar dashi hakanan suka tsaya ba yanda zasu iya, saida ma'aikatan suka ro'ki sholi a bar Mansur haka tukuna ya dakatar da 'yan uwansa.
Clinic d'in cikin prison d'in aka kai Mansur aka dubashi, yayi sa'a baida karaya amma yanada targad'e hud'u haka ma fuskarsa ta kusa tashi daga aiki, bayan an gama dubashi ya kalli wanda ya kawoshi yace "ina bu'katar waya bazanci gaba da zama anan ba".
Sunkuyowa ma'aikacin yayi yace " Banda abinka ai akwai wani me 'boyayyar waya a ciki nine ma nake kai masa katin waya zai baka waya kayu waya ka biyashi"
KAMU SEDANG MEMBACA
HASKEN RANA✔️
Misteri / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...