016

976 106 5
                                    

Tamkar mutum-mutumi take tsaye tana kallon wutar abu d'aya ke ranta wannan wutar iyayenta take ci, cikin mintina goma fire service suka iso wurin wanda bazaka yi tunanin akwaisu a Nigeria ba, kusan motoci 15 na fire service ne suka zo suka fara kashe wuta.

Ganin mutane sun fara nufar inda take yasa tayi baya ta fake cikin bishiyun dake wurin, zama tayi ta rungume jakar a 'kirjinta yayin da hawaye ke zuba daga idanunta, tayi ihu har muryarta ta dashe wadda 'karan abubuwan dake fashewa a gidan bazasu bari aji ihunta ba dukda ba cikin gidan take ba.

Saboda yawan motoci da tukunyar gas dake gidan an d'auki lokaci ana kashe wutar, Mardiyya na zaune ta zubawa gidan ido tana hango yanda wuta ke cin jikin iyayenta, duk haihuwarta ce sila da ace ba'a haifeta ba kuma Mansur bai Gane cewar haihuwarta zata zamo masa masifa ba da iyayenta na raye shine abinda take rayawa a ranta.

Bata lura da 'karan da wayar Abba keyi a aljihun jakar hannunta ba saida taji ana magana cikin d'aga murya.

"Kai mahaukacin ina ne!! Ba saida nace maka karka sake wutarnan ta tashi ba tareda ka d'auko duk wani abun amfani a cikin gidan ba?!! Menene amfanin sanyaku da nayi a 'kar'kashinsa na wannan tsawon lokacin?"

Nan take ta gane muryar Mansur ce, fad'uwar gaba ta fara ji saidai ta kasa motsi tana addu'a kar ya juyo ya ganta, cigaba yayi da masifarsa yace,

"Stupid!! Wanda baisan darajar rayuwarsa ba, mace zaka saka tayi wannan aikin? To inaso ka kasheta a yau d'innan tunda wutar bata kama da ita ba kuma ka sani wannan asarar da kayimin sai na hukuntaka!!".

katse kiran yayi ya sake wani kiran a lokacin wayar Abba ta fara 'kara, cije baki Mardiyya tayi ta sake danna jakar a 'kirjinta tana kallon yanda yanayin mansur ya canza yace "what? Me hakan ke nufi? Kenan wayar bata cikin gidan ko wutar bata ta'ba ta ba? Impossible".

Katse kiran yayi ya kira wata number daban yace "ranka ya dad'e ina tunanin fa Dr Abubakar baya cikin gidansa domin na kira wayarsa tana ringing....... sosai kam indai haka ne alhamdulillah muna fata hakan ya tabbata, saboda mu tabbatar yana lafiya me zai hana kayi tracking number d'in tasa.....wallahi Commissioner ina cikin tsananin tashin hankali kasan banida wani d'an uwa bayansa.....to nagode Commissioner dan Allah a hanzarta".

Yana gama wayar ya bar wajen bayan ya furta "saura ke munafuka bari muga zakiyi biyayya ko zaki bi iyayenki".

cike da tsoro Mardiyya ta ciro wayar Abba ta kashe ta sannan ta cire Sim d'in, a wannan lokacin wutar ta fara raguwa, ba tareda wani tunani ba ta fara gudu har ta fita titi, babu wayarta a hannunta babu jakarta gashi ta kashe wayar Abba balle ta kira Sarah ko Mu'azzam ta sanar musu.

Napep ta tsare ta fad'a masa kwatancen gidan Sarah tare da sanar masa yayi hanzari.

Tasan Sarah bazata san abinda ke faruwa ba domin ita duk wani harkar Media bata damu dashi ba tun lokacin da taga had'arin da Mardiyya ke shiga, tasan cewa da yanzu tasan abinda ke faruwa.

Tayi sa'a tana zuwa ta sami Sarah da mijinta sun fito, da gudu Mardoyya ta fita ta rungume Sarah tareda sakin kuka, cike da zolaya Sarah tace "ke fa Lil Dee bazaki girma ba ko? Dubi kina danne min baby a ciki mene ya faru? Yanzu gida muke shirin zuwa ina Mu'azzam d'in? Wait tun farko ma wani gangancin yasa kika hau motar haya Mardiyya? Kinsan fa Abba....."

"Sarah Abba ya rasu".

A hankali Sarah ta zare hannunta daga jikin Mardiyya ta dafe cikinta tace "Mardiyya me kike fad'a haka?"

"Sarah abubuwa ne da dama nake fad'a miki su a dun'kule, Abba ya rasu shi da Mama wasu ne suka saka wuta ina cikin gidan, Abba yayi 'ko'karin cetona amma shi da umma suna ciki Sarah.....Ina kallon wutar tana ci Sarah....".

HASKEN RANA✔️Where stories live. Discover now