Mardiyya har ta manta da Radiyya saboda zuwan Nadiya da kuma cikin jikinta dake wata na hud'u yanzu, har saida aka kirata a waya aka sanar mata Radiyya na neman had'uwa da Mansur. A ranar da Radiyya ta had'u da mansur Mardiyya taje har gidansu, a lokacin bata nan haka Mardiyya ta zauna jiranta.
Tayi kusan awa biyu sannan ta dawo, dariya tayi ganin Mardiyya a gidansu tace "a tunanina al'kawarinmu babu binciken juna, ganinki anan ya tabbatarmin cewar kina bibiyata".
Girgiza kai Mardiyya tayi tace " al'kawarinmu shine bazaki bibiyeni ba sannan a lokacin da kike bu'katata zaki ganni, nasan kinje wajen Mansur wanda Wannan ba 'karamin had'ari bane ga rayuwarki".
Cire d'ankwalin kanta Radiyya tayi tace " ai aikina ya gaji had'aruruwa, amma ba gashi ya barni da rai ba? Inada tabbacin zanyi ta zama da raina har lokacin da zan sadaki dashi yanda ya nema, na samu kud'i mai yawa sanadiyyar labarin da na kai masa kud'in da business d'ina bai ta'ba bani irinsa ba, saidai inada abinda kema kikeso wanda kinsan saidai ki saya".
" Zan saya ko nawa ne, daga naira d'aya zuwa miliyan d'aya amma sai naga menene wannan abun na kuma amince da muhimmancinsa".
Mamaki sosai Mardiyya tayi ganin video na Mansur, ba tareda tace da Radiyya komai ba ta fara sauraron video d'in
_"gaskiya ne duk abubuwan da ta fad'a miki, ina bu'katar wannan dukiya wadda ke zaki taimaka min a cikin hakan, inaso ki kawomin wannan yarinyar ni kuma zan baki miliyan goma"._
_" wace yarinyar kenan? "_ Radiyya ta tambaya tana kallonsa, murmushi yayi yace _" yarinyar da Kika kunna min voice d'inta a yanzu, idan har da gaske itace 'yar gidan Dr Abubakar to daga ni har ke Zamuyi arzi'ki na fitar hankali"._
Dariya Radiyya tayi tace _" Banda abinka Dr Mansur ai dukiya a hannunka take, sannan miliyan goma tayi kad'an nawa ka bawa wad'anda suka saka wuta a gidan"._
Yanayinsa saida ya nuna tsorata na d'an lokaci sannan ya dake yace "bansan me kike magana akai ba".
Sunkuyawa tayi kusa dashi tace " Mansur, Ni da kai Kar tasan kar ce, idan Zamuyi tafiyarnan Babu wani bo'ye-'boye, nasan ka baiwa wad'anda suka saka wutarnan fiye da miliyan goma inaso ka ninkamin wannan goman sau uk7 nima domin aikina yafi nasu wahala"._
A hankali ya furta _" Duhu5 d'ari biyu kawai na basu akan wannan aikin nasu, daga miliyan sha biyar bazan 'kara miki komai ba domin su ma da suka min gardama 'karshensu baiyi kyau ba, idan kinaso ki bisu can ne to".
Tsayawa video d'in yayi Mardiyya tace " a tunanina ku biyu ne kawai a d'akin, waye ya muku wannan video d'in".
Dariya Radiyya tayi tace " ke yanzu a 'kasarmu akwai abinda kud'i bazai siyar maka ba? A wannan 'kasar kud'i ya fara sayen rayuwa da mutuwa, kud'i yana sayen yarda da kishiyarsa, kud'i na sayen mutunci, yana siyan Tsoro, a yanzu kud'i ya sayemin duk wani tsoro da fargaba da nake dasu, kud'i ya Gama siyan mutuncina da kimata Kinga kuwa nasan darajar kud'i na kuma san yanda zanyi amfani dasu wajen samun abinda nakeso, Mansur ya cutar da babanki ne saboda yardar da yayi dashi to shima mansur d'in Yana gab da samun wannan matsalar, yanda yake ya'ki wajen 'kwatar dukiyar da babu komi nashi a ciki haka amintattunsa suke ya'ki akan ya samu su samu nasu suma, bari kiji akwai d'aya daga cikin amintattunsa da duk wani sirri nashi Yana dashi a killace, dashi Mansur yake komai wanda shine mutumin da na ro'ka ya bani wannan recording din5, ba a wayata nayi ba shi yayi da kansa cike da dabara yayin da yake tsaye a matsayin na hannun daman Mansur, idan har kinason kai mansur 'kasa da gaggawa kina bu'katar wannan mutumi, idan Zaki biyani zan had'aki dashi".
Shiru mardiyya tayi domin zuwa yanzu ta fara Jin tsoron Radiyya tareda jiye Mata tsoro, idan har tayi kuskure d'aya to tabbas Mansur na gab da jifan tsuntsu uku ma da tarko d'aya, Radiyya nada matu'kar wayo saidai batada basira sam, Mardiyya na 'ko'karin warning d'inta ta dakatar da ita tace "yanzu Deeyat ya ake ciki, nawa zaki sayi wannan videon?"
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...