"Sarah? Yayata?" Ta maimaita a hankali, kallon Sarah tayi tana karantarta dukda a tsorace take kuma zuciyarta na cikin rud'ani sai taji wani sanyi da nutsuwa a cikin ranta, karantar Sarah da tayi bata ga alamun cutarwa a tattare da ita ba.
Murmushi tayi tace "ke yayata ce Sarah?"
"Yayarki ce ni Deeyerh, me ya sameki Mardiyya? Saboda bayan ni da mijinki da iyayenmu a cikin garinnan babu wanda yasan asalin sunanki, ki yarda dani 'kanwata".
Kuka Mardiyya ta fara itama Sarah kukan take, matar Rabi'u tana tsaye ta rasa me zatayi kallonsu kawai takeyi, saida suka d'an nutsu sannan Sarah tace "baiwar Allah wacece ke?"
"Naja'atu sunana matar dake ri'ke da Mardiyya suruka ta ce, zata fita ne tace Mardiyya taje gidana mu zauna kafin ta dawo".
"Idan bazaki damu ba muje gidana dani dake da Mardiyya, Mardiyya 'kanwata ce da ta 'bata watanni hud'u kenan ana nemanta sai yanzu na ganta".
Cikin mamaki Naja tace "amma kuma ce mana tayi ita 'yar gudun hijira ce daga jos, danginta duk sun rasu".
Kallon Mardiyya Sarah tayi ta dafe kanta sannan ta sauke numfashi, ba tareda tace komai ba taja hannun Mardiyya suka tsallaka titi, wata mota suka nufa Mardiyya ta ja da baya ta ma'kale domin ita yanzu bazata amincewa kowa ba, idan kuma Sarah itama cutar da ita zatayi fa?
"Mardiyya muje mana, mijina ne kawai a cikin motar".
"Ni bazan biki ba zaki iya cutar dani".
"Mardiyya ko zan cutar da kowa zan cutar da dangi d'aya da ta ragemin a rayuwata? Banida kowa sai ke ta yaya zan cutar dake?"
"Mardiyya? Ashe da gaske Sarah take, Allah mun gode ma, Allah kaine abin godiya, Mardiyya ina kika shige munata nemanki? Mub shiga tashin hankali saboda 'batanki Mardiyya, saboda wannan abin da ya sameki mijinki bashida lafiya yanzu haka......"
Dakatar dashi Sarah tayi tace "menene haka? Ka bari tayi settling yanzu tace bazata bini ba saboda bata amince dani ba".
Shiru sukayi yana kallon Mardiyya, dukda cewa tana Jin a ranta ba zasu cutar da ita ba amma ta kasa amincewa ta bisu, idan har neman rayuwarta akeyi to batada damar amincewa kowa....ko da iyayenta ne a wannan halin.
Waya Sarah ta ciro ta bud'e hannunta na rawa, picture ta bud'e ta nunawa Mardiyya tace "bayan ni da mijinki babu wanda yakeda picture naki a nan, ki yarda dani Mardiyya idan har zan gane fuskarki da kika 'boye shekaru da dama ta yaya bazaki amince dani ba?"
Kallon hoton Mardiyya tayi ta ganta a gefen Sarah, suna zaune kan kujera dukkansu da murmushi a fuskarsu, saida ta kalli hotuna kusan biyar duk nata da na Sarah sannan ta amince zata bita.
"Zan biki, amma saidai kizo muje gidan yakumbo idan nayi mata sallama sai na biki, Sarah inaso nasan wacece ne menene ke 'kunshe da rayuwata?"
"Mardiyya baki san wacece ke ba?"
Girgiza kai Mardiyya tayi tace "bansan wacece ni ba, tashi nayi na tsinci kaina a wani jeji dake cikin garin bauchi ko sunana ban sani ba sai bayan na haihu, idan har ke 'yar uwata ce kamar yanda kika fad'a inaso ki sanar dani wacece ni kafin na biki".
"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun" Sarah ke maimaitawa, idan har Mardiyya ta manta komai kenan duk wahalar da tayi a baya a banza?
A Cikin motar su Sarah suka koma gidan Yakumbo, Naja ce ta bud'e gidan suka shiga d'akin Mardiyya.
Kallon d'akin Sarah tayi tace "anan kike zaune kenan?"
"Eh, anan nake zaune Yakumbo tana min komai sannan tana biyana kud'in aikin da nake mata dukda d'awainiyar da sukeyi dani da yarana".
ESTÁS LEYENDO
HASKEN RANA✔️
Misterio / Suspensowacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...