Nayi mistake wajen saka garin da take ciki wato garin su Hafsa na sanya kaduna, a cikin BAUCHI take zataje KADUNA.
Bayan saukarsu a Kaduna bata san inda zata nufa ba ga twins na kuka ga kaya a hannunta, gaba d'aya ta rud'e bata san inda zata nufa ba.
Tafiya ta fara saida ta samu wuri ta zauna 'kafafunwanta sun ri'ke ga ciwo, bayan ta huta ta samu nutsuwa ita da yaranta ta tashi ta fara zagayen neman kango domin batada wani wurin fakewa da zata samu nutsuwa banda kango bataso ta sake ra'bawa da kowa kar tayi sanadiyyar wani ran.
Tayi rashin sa'a babu wani kango kusa ga 'kafarta da take d'osanawa bazata iya tafiya me nisa ba.
Ledar dake hannunta ce ta fad'i ta dur'kusa ta d'auka tareda ciro kayan tana ninkesu domin sufi mata sau'kin d'auka, gaba d'aya a duniya kayanta kala hud'u twins ne ma keda kala shida-shida domin Mum da Hanan sun musu sayyaya.
"Baiwar Allah na siyarwa ne?" A firgice Mardiyya ta juya tareda tuntu'ben ta kusa fad'uwa, ri'ke hannunta matar tayi tace "yi ha'kuri dan Allah banyi niyyar tsorataki ba, Kaya nagani na yara kamar na siyarwa shiyasa na tambayeki".
"Eh na siyarwa ne" Mardiyya ta fad'a cikin sauri tareda mi'kawa matar duka ledar, karantar fuskar matar tayi taga alamun tana Shirin cutarta domin taga desperation d'inta, tashi tsaye Mardiyya tayi tace "na 'ya'yana ne kud'i nake bu'kata shiyasa zan saidasu".
Murmushi matar keyi ganin banza ta fad'i, kayan da ganinsu masu tsada ne sannan gashi basu tsufa ba, kala shida ta d'auka tace "kin sayar 700?"
"Ban siyar ba" Mardiyya ta fad'a tareda kwace ledar daga hannun matar, domin tunda matar ta fara kallan kayan take karantarta, taga yanda idanunta ke yaba kayan da yanda ta ri'ke su a hannunta tana juyawa cikin kula, idan har tana tunanin zata cuceta ta yaudari kanta.
"A'a baiwar Allah me yayi zafi haka? Kinga dawo nawa zaki siyar?"
"2500" Mardiyya ta had'e rai ta fad'a, zare Ido matar tayi tace "Haba ke kuwa 2500? Ai wallahi ba mai siya a haka to nawa zan samu? Ki ragemin dai ki siyarmin dasu 300-300 na saya".
"To kawo hakan".
Da sauri matar ta bud'e Jakarta ta ciro 2000 ta bawa Mardiyya tace "bani canji".
"Banida canji".
'dari biyar ta zaro ta mi'kawa Mardiyya tace ki ragemin mana".
Harder hannu Mardiyya tayi tareda girgiza kai a hankali matar tace "wannan ko jarabar naci".
Bayan ta bata kud'in Mardiyya tace mata "dan Allah ko kinsan wani masauki da zan samu? Mai sau'kin kud'i".
"Eh to akwai wani gidan haya kusa dani muje kigani, ina tunanin kud'in baifi 5000 a shekara ba".
Bin matar tayi tana d'ingishi matar tace mata "kije a miki dressing kar ya zama matsala".
Mardiyya bata bata amsa ba domin neman wajen da zata aza ha'kar'karinta kawai takeyi, tun daga 'kofar gidan tasan cewa bazata ga abin arzi'ki ba, kaca-kaca yake ga mutane a 'kofar gidan, kai tsaye suka danna kai cikin gidan Mardiyya ta saki baki tana kallon ru'bewar gidan, toilet babu 'kofa sai katako tana kallo ta hango mutum a ciki, cikin sauri ta kawar da kanta ta fara kallon tsakar gidan, turmi ne 'kato sai shirgi ta ko ina ga mutane kamar an 'kyan'kyasosu.
Girgiza kai tayi domin da ta zauna a wannan wajen gara kangon da take zama a baya, ko 'kazantar gidan bazata barta ta zauna ba, kewar Hafsa ta fara tana tunanin inama wannan ibta'i bai faru ba da yanzu tana tareda hafsa cikin kwanciyar hankali tana nuna mata kulawa.
Bayan sun fito matar tace "to nidai bari na shiga gida idan dai wannan bai miki ba to bana tunanin akwai wani gaskiya da zaki iya biya da kud'in hannunki".
"To nagode dan Allah ina ake saida abinci?"
Shiru matar tayi tana karantarta sannan tace "shigo na baki amma kiji tsoron Allah karki shigarmin gida da mugun nufi".
"Bazan cutar dake ba ni ba muguwa bace" Hadiyya ta fad'a cikin gajiya, suna shiga matar ta shimfid'a mata tabarma ta kawo mata ruwa, sauke twins tayi ta kwantar dasu kan kayan dake hannunta, sai mi'ka sukeyi saboda gajiya ita kanta bacci take bu'kata a wannan lokacin.
Taliya ta bata da mai da yaji cikin sauri Mardiyya ta cinye abincin, duk yanda taso ta zauna ta huta babu hali domin matarnan bata bata fuska ba.
Godiya tayi mata ta wanke 'kafarta tayi sallah sannan ta canza zanin jikinta ta cire mayafi ta sanya hijab ta fita, saida tayi nisa sannan ta fara tambayar gidan haya bata samu ba har dare yayi.
Tana zaune 'kofar wani gida ta zuba tagumi taga wata tsohuwa tazo wucewa, da sauri ta tashi ta gaidata sannan tace "baaba tambaya nake dan Allah ko akwai wani gidan haya a nan kusa da zan samu?"
"Eh akwai gidan d'ana naji yana zancen zai zuba haya a ciki, saidai amma ki dawo gobe".
Cikin tsananin gajiya tace "baaba banida inda zanje ni ba'kuwa ce a garinnan idan har zan ganshi yanzu ki taimakamin".
Matsowa tsohuwar tayi gab da Mardiyya sannan tace "ke kuwa baiwar Allah me zai raboki da garinku a wannan hali? Ba dai sha'kiyancin zamaninnan kikayi iyayenki suka koreki ba ko?"
"A'a baaba ibtila'in jos ne ya rutsa damu".
Tausayin Mardiyya ne ya kamata tace "Allah sarki bayin Allah kunga rayuwa, Allah ya saka mana ya 'kara mana zaman lafiya wad'anda suka mutu Allah ya ji'kansu, muje gidana dama ni kad'ai ce ".
Motsi Mardiyya taji a bayanta wanda ya sanya gabanta fad'uwa, waiwayawa tayi a hankali taga zarginta ya tabbata, me mutanennan keyi a nan kuma? Wa ya sanar musu tana kaduna?
Cikin ikon Allah basu ganeta ba saboda sauyin kayan jikinta sannan ba sanin fuskarta sukayi ba, Allah ya dubeta gidan matar baifi taku biyar daga inda take ba kusan da gudu ta 'karasa bayan sun wuce.
'daki guda baaba ta bata da shimfidarsa da komai sannan tace idan tana bu'katar wani abu ta tambayeta kawai.
Kwanciya Mardiyya tayi ta dinga juyi sabofa ciwon jiki, ashana ta nema da sauran kayan girki ta d'aura ruwan wanka, kafin ruwan yayi taje d'akin baaba ta zauna taba bata labarin 'karya na yanda abun ya ritsa da ita har ta rasa family nata.
Tsohuwar ta tausaya mata sannan ta amince ta zauna tareda ita har 'kafarta ta warke sannan ta samu nutsuwa idan Allah yayi da danginta ragowa sai ta gansu.
Farin ciki ne ya saukarwa Mardiyya a cikin ranta tana murnar ta tsira, saidai bata san cewa masifun dake jiranta a wannan gari sunfi na baya yawa ba........
KUYI HA'KURI DA WANNAN WALLAHI INA TYPING INA GYANGYAD'I SABODA GAJIYA, GOBE BA LALLAI NAYI BA TNX
ŞİMDİ OKUDUĞUN
HASKEN RANA✔️
Gizem / Gerilimwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...
