"zan fad'a muku komai idan Allah ya kaimu aka gama aurenki lafiya, inaso dai mu kasance cikin shiri dukda na tura Mansur wata 'kasar daban ban sani ba ko yana da ido a kaina, banaso kema ki Shiga matsala". Mahaifin Mardiyya ya fad'a cikin murmushi
"Shiyasa fa Abba nace kawai tunda anyi d'aurin aure ba sai anyi wasu abubuwan ba, media kawai sun isa su yad'a labarin idan har suka ganni tare da kai, idan wannan dinner d'in zata zama matsala Abba a fasa kawai".
"A'a Mardiyya ke kad'ai ce saura da kika ragemin, yanda akayi bikin Sarah kema haka za'a yi bikinki, sannan ki bamuyi ba dangin mijinki zasuyi ai ko? Allah zai kare zamu san yanda za'ayi ki 'badda kama amma inaso ki ajiye komai sai bayan aurennan, Allah yayi baza'a yi aurenki da dangina ba".
Shiru mardiyya tayi domin shi kansa Abba ya sani idan ta sanya Abu a gaba bata ta'ba hutawa sai ta sameshi, dukda ta za'bi 'bangare mafi wuya a aikinta na jarida amma batada tsoro ko fargaba.
"To Abba zan bari amma meyasa ka manta da kowa naka? Hatsari kukayi ko kuma haka nan ka manta dasu? Meyasa kuma Abba duk hotunanka da suke yawo a duniya babu wanda ya gani a danginka balle ya nemeka?"
"Mardiyya wad'annan tambayoyin a kullum su suke min yawo a kaina kuma na kasa amsa su, inaso na tuna dangina nima amma bazan iya tuna lokacin da na manta su waye 'yan uwana ba, garinmu ma Mansur ne ya fad'amin amma bai sake fad'amin komai ba, mu bar wannan maganar a ina ake a shirye-shirye? Me ake bu'kata?"
"Nidai babu komai". Mardiyya ta fad'a tana tunanin next target d'inta, a cikin kanta ta sake sanyawa Mansur alamar tambaya.
Sarah ma amsa masa tayi da babu komai Mama kuma tace masa akwai d'an abubuwa amma tayi magana a turo mata su daga kamfani.
"To shikenan, zan turo muku 500 duka idan akwai abinda kuke bu'kata kuyi dasu, idan kuna bu'katar 'kari kuyimin magana".
"Okay mungode Abba" suka fad'a a tare.
Mardiyya na zauna bakin gado tana jiran Abbanta, cikin ikon Allah anyi taro mai matu'kar armashi ba tareda kuma Mansur ya sani ba, sannan duk wanda ya danganci mansur ma Abba saida yayi 'ko'karin 'boye masa auren, dukda wad'annan shirye-shirye saida aka sauyawa Mardiyya kamanninta da kwalliya wanda bata damu da hakan ba.
"Fito Abbanki ya shirya". Mama ta fad'a tareda kamo hannun Mardiyya, tashi Mardiyya tayi tabi bayan Mama.
Sallama sukayi ya tafi kaita gidanta, suna tafe suna hirarsu a mota kamar ba amarya za'a kai ba.
Mu'azzam na waje da wasu masu uniform a bayansa, suna fitowa mutanen suka Sara musu sannan suka 'kame, gefe Mu'azzam ya koma suka gaisa da Abba, hannu Mardiyya ya kama ya sanya a cikin na Mu'azzam yace "d'ana, Mardiyya amana ce a wajenka duk wuya duk dad'i a kowane irin yanayi inaso ka ri'kemin ita amana a yanzu kai ne family d'inta".
Kallon Abba Mardiyya tayi ta kalli Mu'azzam, wani communication sukeyi da ido wanda ta kasa ganewa sannan suka shiga gidan.
Gate ne mai matu'kar kyau suka wuce sannan suka fad'a cikin gidan, nan ma yalwataccen fili ne sannan babu wani alamar 'kofa a wajen bazaka ta'ba cewa ga ta wurin da ake shiga ba.
Palour suka zauna Abba yayi musu addu'a sannan ya tafi, 'yan mutanen da suka mata rakiya duk a d'ar suka ga gidan suka fita domin idanun Mu'azzam a kansu yake, bai yarda da kowa ba wanda hakan shine abinda aikinsa ya nuna masa, kowa a cikinsu suspect ne kuma a wajensa kowa nada niyyar cutar da Mardiyya ne.
Bayan kowa ya tafi Mardiyya ta cire mayafinta ta cilla gefe tareda mi'kewa kan kujera,
Zama yayi a hannun kujerar yace "kin gaji kenan".
Tunawa tayi fa kamata yayi ace a zaune ya ganta fuskarta a rufe, amma gata a kwance kamar tayi wata a gidan.
Zama tayi da sauri taja mayafinta , kallonta yayi yana dariya sannan ya cire mayafin yace "babu komai ajiye mayafinki, yanzu mu samu muyi sallah, sai muci abinci sai mu samu wani channel mai kyau mu kalla saboda daga ni har ke wannan ne time na hutunmu bayan yanzu dukkanmu bamuda hutu, ya kamata mu ribaci time d'inmu ko?"
DU LIEST GERADE
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...