009

1.2K 99 1
                                    

"shikenan zan miki bayani kuje d'akin ki". Sarah ta fad'a tareda nufar d'akin Mardiyya.

Zama sukayi bakin gado Sarah tace "zan miki bayanin komai, amma akwai wasu abubuwa da kika bani ajiya bari na d'aukosu".

Ita dai Mardiyya bin Sarah take da kallo har Sarah ta nufi 'kofar, cikin sauri ta cire key d'in 'kofar ta fita ta rufe Mardiyya a ciki.

Takaifi ya sanya Mardiyya ko 'kofar bata kalla ba balle ta jujjigata, tashi tayi tana zagaye d'akin cikin 'bacin rai yayin da tunani ya fad'o mata, idan har wannan d'akinta ne bazata rasa wasu clues a ciki ba.

Kayan wardrobe d'inta ta fara bincikawa cikin sauri duk ta hargitsasu, ciwon kai ta fara ji wanda ya sanyata dakata abinda take ta sha magani.

Kwanciya tayi gefen twins tana kallonsu cike da tausayi, a cikin ranta tana jin 'ya'yanta basuyi sa'ar uwa ba domin sam bata tunaninsu, a cikin d'akin ma idan wani abun ya d'auki hankalinta mantawa take dasu idan ba kukansu taji ba, kowacce uwa 'ya'yanta sune first priority nata amma meyasa ita take ganin abinda take hange yafi 'ya'yanta muhimmanci? Meyasa bazata amincewa Sarah ba ta manta da abinda ya faru a baya ta fara sabuwar rayuwa? Da wannan tunanin ta samu bacci ya d'auketa.

Tana farkawa taga abinci a bedside d'inta, agogon d'akin ta kalla taga lokacin sallah yayi ta tashi tayi sallah taci abinci sannan ta fara bincikenta a nutsuwa.

Kayan da ta zubar ta d'auka tana ninkewa a hankali, har ta gama ninkewa bata ga komai ba ta d'aukesu ta jera ta d'auko na 'kasan su.

Ta gama fito dasu duka ta lura da wani abu, katakon dake bangon wardrobe d'in saman da na 'kasan akwai banbanci wanda idan ba kula kayi sosai ba bazaka gani ba.

Kalarsu d'aya yanayin zamansu ma d'aya, saidai na saman yafi na 'kasan kauri.

Shafa bangon wardrobe d'in ta farayi tana duba ko zataga wani abu bataga komai ba, kayan da ta jera ta kwashe ta fara lalubar jikin bangon shima, wani katako ta ta'ba a gefe taga murfin yayi motsi ya bud'e kad'an.

Hannunta ta sanya ta 'karasa bud'ewa saida ta kusa tsalle domin murna, takardu ne kala-kala a ciki da flash guda biyu wad'anda suke sak wanda take yawo dashi.

Maida kayan tayi sannan ta d'auki takardun ta koma kan couch d'in dake d'akin ta fara dubasu.

Jarida ta d'auka mai taken *EVERYMOMENT* ta fara karanta labarin da taga an masa alama da biro, headline na rubutun an rubuta *TRAGIC DEATH DR ABUBAKAR WADA*.

Gabanta ne fad'i yayin da taga sunan mahaifinta da hotonsa a gefe da na mahaifiyarta, zuba musu ido tayi tana jin wani yanayi na daban a jikinta sannan ta fara karanta labarin da ya biyo bayan rasuwar iyayenta, labarin dake cikin harshen turanci.

_a jiya ne muka wayi gari da mummunan labari na mutuwar Dr Abubakar I Wada, labarin ya girgiza mutane da dama ciki harda president na wannan 'kasar tamu yanda ya nuna rashin jin dad'insa game da al'amarin, kamar yanda aka muka sani Dr I Wada shahararren d'an kasuwa ne da yake da kamfanoni fiye da 20 a wurare da dama na Nigeria kamfanonin da aka fi sani da *M&S COMPANIES*, yanada kamfanoni da dama a cikin Africa har ma da sauran 'kasashe na duniya, yana da kamfanoni da suka had'a na 'kera takalma, plates, kamfanin zare, gidajen mai, kafanin rodi, da kuma had'in gwiwa da kamfanoni da dama a China da America, kamar yanda muka samu labari wutar da ta tashi a gidan babban attajirin wadda har zuwa yanzu babu wanda ya san sanadiyyar faruwarta tayi sanadiyyar mutuwarsa da dukka iyalansa wanda suka had'a da matarsa da 'yarsa d'aya tal da ya haifa, abin tambaya anan shine wanene zai gaji wannan dukiya da Dr Abubakar ya bari? Muna mi'ka sa'kon ta'aziyya ga dukkan d'aukacin jama'a domin rashin Dr Abubakar rashi ne mai girma, ya kasance mai tausayawa mai taimako, mun samu ziyarar ba'ki da dama daga 'kasashe na fad'in duniya........

HASKEN RANA✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang