D'auke numfashi sukayi dukkansu su biyun suna jiran me zaice, addu'a Mardiyya takeyi Allah yasa Danginta suna garin idan aka ce sunbar garinnan wahalarta ta koma farko.
"Gidan malam yana nan amma kuma tun jiya malam sama'ila baya garinnan yaje wani 'kauye d'aurin aure amma a darennan zai dawo, idan garin Allah ya waye gobe sai muje gareshi amma meyasa kuke son ganinsa? "
" Ni jikarsa ce 'ya ce ni ga Abubakar... Ina nufin habu".
Shiru d'akin yayi babu wanda ya iya cewa komai, bayan lokaci Baba yace "Ina labarin Habu d'in? Ashe yana raye har yayi iyali?"
"Baba mahaifina baya raye zan sanar muku komai idan Allah ya rayamu xuwa gobe".
Yanda tunaninta ke cike da tambayoyi haka nasu Suma, kafin wayewar gari zance ya karad'e ga 'yar habu d'an malam tazo gari, ashe habu yana birni yayi kud'i har yayi iyali Amma ba ta'ba zuwa ganin iyayensa ba, maganganu dai kala-kala marasa dad'i wanda suka sanya jikin Mardiyya yayi sanyi sosai.
Ranar baccinta ba isasshe bane domin zuciyarta na cike da waswasi, ta yaya kakanta zai kar'beta? A yayin da suke can suke jin dad'in rayuwa wacce irin rayuwa danginta ke ciki? Mahaifinta yanada arzi'kin da zai wadata dukkan mutanen garin. Idan suka san wanene mahaifinta wane reaction zasuyi?
Tashi tayi ta fara nafila har asubahi, tana idar da sallah ta yima twins wanka ta had'a breakfast ta zauna jiran gari ya waye taje tayi nata wankan, Mu'azzam kuwa bata san wane toilet yake shiga ba ta shirya tambayarsa idan ya dawo daga masallaci.
Sun shirya tsaf sun fito yayin da duk idanuwan mutane ke kansu domin dukkansu ababen kallo ne, addu'a Mardiyya keyi cikin zuciyarta kan Allah ya karesu daga mugun ido har suka isa gidan malam.
Wata kwata suka fara cin Karo da ita a 'kofar gidan, sallama sukayi suka shiga ana Bindu har saida sarkin fawa ya tsaya ya kori yara da 'yan matasan dake biye dasu.
Tunda Mardiyya ta saka 'kafa cikin gidan 'kwalla ke cikowa a idanunta, 'karamin gida ne ba kamar na sarkin fawa ba sannan kana ganin gidan kasan babu wadata, yara ke shige da fice dukkansu malnutrition ya cinyesu.
Wani 'bangare suka nufa katangar 'kofar ta zube, Mardiyya kasa danne kukanta tayi ta bar hawayenta na zuba tana bin gidan da kallo, wannan shine gidan da iyayen mahaifinta ke zaune?
Sallama sarkin fawa yayi wats budurwa ta fito, "Ina babanku yake?"
"Ya fita bari na kirashi".
"To ki hanzarta Iya fa tana nan?"
" Ta fita amma bari na kirata".
Fita tayi cikin sauri Mardiyya taci gaba da bin gidan da kallo, dukda laifin na Mansur ne sai take jin inama mahaifinta ya tsananta bincike da zai gano inda suke dukda nisan akwai yawa.
Sun kusa minti 20 a cikin gidan suka ji sallama, amsawa sukayi suka kalli malam Ismail wanda kallo d'aya zaka masa kasan mahaifin Abubakar ne, dukda tsufan da ya bayyana a fuskarsa amma kamanninsu sun 'baci.
Kallon Mardiyya yayi yace "sannunku da zuwa".
Kasa amsa masa tayi saboda yanayin suturar dake jikinsa da alamu Tasha wuya, yadi ne amma layukan jikin yadin duk sun bayyana.
"Bayin Allah me ya kawoku?" Ya furta maganar yana kallon Mardiyya domin ance jini baya 'karya, a jikinsa yana jin jininsa ce saidai ya kasa gaskata hakan kamar yanda ya'ki aminta da jita-jitar dake tashi a garin.
"Baba....ni sunana Mu'azzam kuma ni yaro ne a wajen Alhaji Abubakar ita kuma wannan 'yarsa ce".
Shiru malam Ismail yayi Yana kallon Mardiyya, zuciyarsa cike da tambayoyi yace "ya sunanki? A ina kika san Abubakar?"
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...