Afuwan kwana biyu Kun jini shiru, ina bincike ne akan abinda zan rubuta that's why.
Tamkar mahaukaci Mansur ke zagaye a office d'in Yana huci, a hankali Habib ya furta "calm down sir, indai yarinyarnan da gaske tana existing sai na samo maka ita ko ina take, kamata yayi ka zauna kayi dogon tunani idan har Yana da 'ya a ina zai 'boye ta? Wa ya sani a garinnan da zai amince dashi ya bashi 'ya har tsawon shekarunnan?".
Kujera mansur yaja yace "a sanina Mahaifiyar yarinyarnan danginta ba sonta suke ba saboda 'yar tsuntuwa ce, accident akayi Mai gidan ya ceceta ya kawota to gaskiya mutanen gidan basa sonta wanda haka ne ma ya Sanya na takura masa ya aureta saboda 'ya'yansa su taso basuda wani family fa zasuyi alfahari dashi, akwai wata dattijuwa da tayi musu aiki shekarun baya ina tunanin ita aka baiwa ajiyar yarinyar saboda matar Abubakar ta sha'ku da matar, inda zamu samo tsohuwar shine aiki".
"Ba kace ka ganta a gidan ba? A yanzu 'yan aikin gidan samu fara nemowa ku tuhumesu su fad'a mana kamannin yarinyar idan bamu samu ba sai mu tambayi wad'anda suka kwana biyu a gidan adress d'in matar, amma a tunanina ranka ya dad'e ai baka bu'katar wannan wahalar kanada ikon 'kwace dukiyarnan ta 'karfin iko meyasa bazaka yi haka ba?"
Had'e hannayensa Mansur yayi yace "matsalar shine kasan cewa inada illegal activities da dama da nake gudanarwa wanda idan aka sani na shiga uku, inaso su mallakamin ne da kansu yanda bincike bazai biyo kaina ba akan yanda na mallaki dukiya ba tareda wannan yarinya ta sa hannu ba, dukda na sanarwa media ta mutu amma da aka duba gawar aka ga namiji ne suka tabbatar bata mutu ba suka fara zuba Ido, a yau da ta dawo 'kasarnan har wani munafikin ya samu hotonta kwanaki kad'an za'a nemi hira da ita, idan kuma aka San tanada 'yar uwa ai nazo duniya a banza nayi asarar zamana, domin duk abinda na kafa shekaru da dama Ina kallo zai su'buce, so nake na kar'ba ta sanyi idan suka takuramin na kaisu gaba, ko na tsawatar musu ta hanyar da ta dace".
A lokacin da Mansur ke bincike a kan Mardiyya ita Kuma bincike take a kan kamfaninsa na niger-delta, abin mamaki ba 'karamin kamfani bane domin lemukan da sukeyi fake sunada yawa kuma na kamfani daban daban, sannan ma'aikatansa 'yan can ne wanda yana amfani ne da basirarsu Yana samun kud'i, ta tabbatar idan ya rasa kamfaninnan to yayi babban rashi.
Tana zaune tana chat da d'aya daga cikin masu supplying kayan zuwa sauran states Mu'azzam ya shigo, amsa masa sallama tayi ya sunkuya dai-dai kanta yace "yau kuma me akeyi?"
"Order nake so nayi".
Zama yayi gefenta yace "order kuma na me?"
"Na kayan da kamfanin Uncle ke sarrafawa, magana nake da shugaban kamfanin wanda Uncle ya d'aura saboda bayaso asirinsa ya tonu, zanyi order ne wadda ba'a ta'ba yin kamarta ba ta kud'ad'de masu yawa amma akwai alfarmar da nake nema daga gareka".
"Kinaso kine Niger ko? Babu inda zakije I'm not risking your life on this, Dee-dee na mutanennan hatsari ne dasu mugayen 'yan ta'adda ne da gwamnati ma ta gaza juyasu, Allah a second guda zasu yi gutsi-gutsi da namanki akan kud'i, bazai yiwu ba".
Zama tayi ta tallafi fuskarsa tace "dad'ina dakai saurin yanke hukunci, nima me zai kaini Niger-delta da raina da lafiya ta? Kayi tunani mana ga Uncle anan, Zan sanar musu bazan je ba su had'ani da shugabansu domin real business nakeso nayi".
"Sai kuma kije ki sameshi ko? Idan yaga fuskarki bakya tunanin zai ganeki ko ki fad'a cikin matsala?"
"Hmm wannan tunanin nakeyi nima, inaso na tura wani namiji wanda yasan business sosai, namijin da zai iya 'badda kama sai kuma na hanga na hango babu wanda zai iya yimin haka....."
Kafin ta 'karasa Mu'azzam ya fara sulalewa, dariya tayi tareda 'kan'kame hannunsa tace "sai mijina, abin alfaharina, sanyin idaniyata, my one and only, habibey na, my other half, mine and mine only, haba mijina idan baka yimin ba wa zaiyi min? Nasan kanada talent d'in da zaka iya zuwa kayi magana dashi ka bar wurin ba tareda ya ganeka ba, Hubby idan ba kai ba saidai naje da kaina".
VOCÊ ESTÁ LENDO
HASKEN RANA✔️
Mistério / Suspensewacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...
