023

1.2K 109 10
                                    

Mardiyya na Shirin kiran Sarah taga kiran Sarah ya shigo, kai wayar kunnenta tayi tace "Sarah meyasa zakiyi haka? Muna gab da kawo 'karshen komai meyasa zaki jefa kanki da ni cikin matsalar?"

_"Mardiyya na gaji, a kowacce Rana banida burin da ya wuce yau naga family na sun zama waje d'aya cikin farin ciki da aminci, Deeyat tun daga haihuwarki farin ciki yayi 'kaura a gidanmu, yanzu mun rasa iyaye na rasa d'a, na rasaki na tsawo watanni bazan iya jira har lokacin da zan rasa ki da twins na har abada ba, mun fara tara family dole ne mu ha'kura na yafe dukiyar Abba gaba d'ayanta I need my sister back, dan Allah ki ha'kura da wannan ki bar ya'ki da Uncle ki 'kyaleshi yayita cin haram bazai mutu ba sai Allah ya wula'kantashi"_

" Na fahimci inda kika dosa Sarah, amma na miki al'kawarin komai yazo 'karshe, na gama ya'ki da Mansur a yanzu haka neman family d'in Abba nakeyi kuma insha Allah zan samesu da wuri, na sani kinyi haka ne saboda kulawarki gareni amma ki sani Mansur bazai 'kyaleki ba a yanzu haka tabbas ya aiko a d'aukar masa ke ko kuma yazo da kansa, daga ni har ke a wannan lokacin muna cikin takura sosai, Sarah I know you love me but there's an easy way of doing this, yanzu ya kikeso muyi? Daga ni har ke kashemu zaiyi".

_"zamu bar masa dukiyar Abba ne gaba d'ayanta mu Kuma sanar cewa mun bar masa, mazajenmu sunada arzi'kin da zasu ri'kemu wanda duk zuri'armu bazasu d'and'ani talauci ba, zamu bar 'kasar mu koma can wata 'kasar mu gina sabuwar rayuwa".

" Na fahimceki Sarah amma bazan iya backing out yanzu ba, I need to finish this please take care of yourself idan kina gida ne yanzu hubby ya turo securities su zagaye gidan kafin Mansur yayi wani abu, da zarar kinji wani alamu da baki amince dashi ba number ta na emergency call naki ki kirani".

_"Mardiyya... I'm pregnant please even if not for my sake for the sake of my babies dan Allah ki bar wannan abun, doctor ya fad'amin damuwa zata iya sakani na rasa abinda ke cikina banaso na sake rasa wani babyn Dan Allah Dee"_

" I'm sorry Sarah". Mardiyya ta fad'a tareda katse kiran, tambayar address d'in Mansur na kebbi, kwatance Gwoggo tayi musu yanda ta tuna garin.

Saida gari yayi duhu sosai sannan suka koma gida domin su shirya tafiya kebbi, a hand suka tsaya gidan Sarah suka tabbatar security d'inta is intact sannan suka koma gida, dukda Sarah na 'kar'kashin tsaro sosai amma hankalinta Mardiyya sam ya'ki kwanciya, washegari tana tashi sallar asuba ta kira mijin Sarah ta ro'ki ya d'auki Sarah su tafi wata 'kasar domin ta samu nutsuwa, kasancewarsa d'an kasuwa ne tafiye-tafiye basa masa wahala, a baya yana d'aya daga cikin masu yiwa Abba aiki a d'aya daga kamfanoninsa, ri'kon amanarsa yasa Abba ya bashi jarin da zai tsaya da 'kafarsa wanda a wannan lokaci ya samu Albarka sosai ya zama wani babba a duniyar saye da sayarwa.

4am Mardiyya suka bar gida suka nufi airport, a can suka had'u da sarah, Sarah na ganinta ta fara kuka tana ro'konta su tafi tare domin ita Sarah tunaninta business ne zai fidda mijinta, da kyar Mardiyya ta samu Sarah ta kwantar da hankalinta, saida suka ga tafiyar su Sarah sannan suma suka d'au hanya.

Saida suka sauka Mu'azzam ya yiwa dangin mahaifiyarsa sayayya, gidan baiyi musu wahalar ganewa ba saidai dukkansu a tsorace akan wacce irin tar'ba za'a musu.

Garin 'kauye ne sosai da babu wadatar ruwan sha ma balle ayi tunanin wutar lantarki da kuma wayoyin hannu, saboda haka hankalinsu kwance suka shiga garjn ba tareda fargabar wani zai kawo musu hari ba.

Sun Isa gidansu Mahaifiyar Mu'azzam suka tambaya aka tabbatar musu nan ne, a 'kofar gidan suka ga wani tsoho yana zaune kan dandamali da yara biyu a hannunsa, dur'kusawa sukayi suka gaidashi Shima ya dur'kusa yana gaishesu, fara'a ce ta bayyana a fuskarsa domin ba kasafai suke samun irin wad'annan ba'ki ba.

HASKEN RANA✔️Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora