027

789 103 5
                                    

"Sarah bakya jina ne kikayi shiru?"

"Waye kai d'in?"

"Ban gane waye ni ba? Baki Gane me magana ba? "

" Ban gane ba"

" Man.... " Shiru yayi bai 'karasa ba tareda katse wayar cikin sauri, jifa yayi da wayar ya daki table d'in dake gabansa, meyasa ya aikata hakan? Wani irin ganganci yasa yayi hakan ana tsaka da shari'a ya Kira masu 'kararsa?

Cikin sauri ya d'auko wayar domin kiran lawyer yaga ta fashe, tsaki yayi tareda jifa da ita ya zaro d'ayar wayar tasa ya kirawo lawyer, bayan ya sanar masa abinda yayi lawyer yace masa "ranka ya dad'e hakan da kayi kuskure ne babba, domin tun a farko na sanar maka idan har zaka kirasu to ya kasance sasanci zaka nema ko sulhu, wannan kiran zasu iya amfani dashi a matsayin babbar hujja shi kad'ai ya isa a...... "

" Karka fad'amin maganar banza!! Ba kiranka nayi ka yimin fad'a ba kud'ad'de na biyaka saboda ka tsaya min, saida kuma na sanar maka a samo mana al'kali wanda zaiyi mana abinda mukeso amma bakayi hakan ba babu abinda kakeyi sai 'batamin lokaci, idan bazaka iya abinda ya kamata ba ka janye na d'auko wani".

Cikin tausasawa lawyer d'in yace " ranka ya dad'e.....nifa bance bazan iya ba Kuma kana sane da cewa baka bari nayi abinda ya kamata, baka sanarmin ba a lokacin da ka tura aka yiwa yarinyarnan barazana yanzu komai zai kwa'be mana idan aka koma kotu, sannan yanzu ka kirasu inaso ka kwantar da hankalinka idan har zaka bi shawarata ha'karmu banajin zata cimma ruwa idan har da dama mu nemesu muji abinda suke so idan da Hali a sasanta ya wuce wurin".

" Har abada!!" Mansur ya fad'a cikin d'aga murya, " wallahi ko zan mutu bazan Basu dukiyarnan ba domin ita kad'ai ta ragemin a rayuwata, iyalina basa gabana dukiyarnan kawai itace a gabana bazan ta'ba basu ita ba ko da hakan zaiyi sanadiyyar rasa rayuwata inaso kasan hakan".

Numfashi lawyer d'in ya ajiye domin shi kansa saida ya raina kansa da yayi tozali da lawyers d'in su Mardiyya domin dukkansu 'kwararru ne wanda duk Nigeria an sansu wajen samun nasara a kan 'karar da suka sanya gaba gashi Mansur ya hanashi gabatar da aikinsa yanda ya kamata, a hankali yace "shikenan ranka ya dad'e zamu san abinyi". Katse kiran yayi yana mamakin 'karfin hali na Mansur Akan wannan shari'a.

Kiran Mardiyya Sarah tayi a tsorace take fad'a mata abinda ya faru, hamdala Mardiyya tayi tace "kinyi recording kiran ko?"

"Nayi Dee-dee amma ni inajin tsoro me kike ganin zai faru da su? Mansur fa zai iya kashesu da gaske kuma.....".

" Calm down me ciki, ba abinda zai faru zamu san abin yi amma Mansur bazai samu nasara akan wannan abin da ya fad'a ba insha Allah, zan sanarwa hubby shi yasan me zaiyi akan hakan".

Mu'azzam da kansa yaje har 'kauyen su Baba domin ya taho dasu bayan ya sanar musu abinda Mansur yayi i'kirarin aikatawa saidai Baba yace sam babu inda zaije sai yaga 'karshen rashin kunyar Mansur, yana jiransa yazo yaga abinda zaiyi masa. Har dabara Mu'azzam yayi yace suzo suga zaman kotu Baba yace babu kotun da zai shiga haka Mu'azzam ya ha'kura ya dawo.

Mardiyya na zaune tana jujjya flash d'in da ya zamowa rayuwarta matsala a baya, tunda aka fara case d'innan take gwada flash d'in amma ya'ki bud'ewa, ji take tamkar ta tattakeshi ya lalace saboda takaici, duk abinda suke bu'kata yana cikin wannan flash d'in amma da alamu saidai suyi asararsa. Meyasa wannan mutumin ya bata flash babu pin?

Jujjuya flash d'in takeyi a hannunta tana le'ka cikinsa, bud'e murfin takeyi tana rufewa ta lura da rubutun dake jikin flash d'in ya d'an karkace, shafa rubutun tayi taji tamkar leda, meyasa bata lura da wannan ba? Cikin sauri ta nemi inda zata bud'e ledar tayi nasara kuwa tana d'ago ledar taga ta cire, wani 'kara tayi cikin murna wanda ya sanya twins zubar da kayan wasansu cikin tsoro suka maida dubansu gareta, roba CE bayan ledar da takarda a ciki da kuma wannan tracker d'in, tamkar 'karamar yarinya Mardiyya ke tsalle tana 'kwalawa Mu'azzam kira.

HASKEN RANA✔️Onde histórias criam vida. Descubra agora