017

1K 113 9
                                    

"sir babu kowa a gidan na tambayi neighbor d'insu yace bai sani ba domin baiji d'uriyarsu ba sama da sati guda".

Tsaki mansur yaja sannan yace "inaso ki shiga gidannan ku ciromin duk wani takarda ko shaida da ya danganci kadara".

Mota ya shiga ya nufi banki ya bu'kaci statement d'in abba domin yasan nawa ne a ciki, bayan ya fad'i sunansa an duba manager d'in yace "sorry sir amma ya bada warning kar a baka bank statement nashi ko wani abu da ya shafi nasa".

"Ban gane ba, baka karanta jarida bane? Baka San cewar ya rasu ba kuma kafin ya rasu ya mallakamin duk abinda ya mallaka saboda ni kad'ai ne d'an uwansa kuma family d'insa da ya rage, wannan ai zancen banza ne!!".

"Sorry sir amma ba kaine next of kin d'insa ba sannan wannan itace takardar da ya kawo mana yau one month kenan yace kar a sake a bawa kowa dukiyarsa idan ba mutane biyun da suke rubuce a jiki ba".

D'ago takardar manager yayi sannan ya maidata, a fusace mansur ya daki table d'in yace "idan ka sake min maganar banza zanyi sueing d'inka!! Kasan wanene ni? Wani zancen banza kake kawomin haka? Ina bu'katar sanin nawa ne a account d'in d'an uwana da duk wasu information akai!!"

Cikin nutsuwa manager yace masa "d'an uwanka shi keda alhakin baka wad'annan informations mu bankinmu bamuda wannan damar ya sanar mana wadda zata zo zata taho da informations na duk abubuwan da suka danganci banking d'insa anan".

Mansur ji yake kamar ya kamar ya haura table d'in ya sha'ke wuyan manager amma ya dake yace "manager wadda yake fad'a harda ita wutarnan taci, ta 'kone tareda iyayenta".

"Sorry mister, amma mu protecting ha'kkin customers d'inmu is our number one priority, ya bani suna da duk information na wad'anda za'a mallakawa dukiyarsa a cikinsu d'aya zata iya zuwa, saidai idan ka sami permission daga wurinta sannan mu baka abinda kakeso".

Tashi Mansur yayi ya fice fuuu cike da 'bacin rai ya nufi wani bankin, the same abinda aka fad'a masa a wancan bankin shi aka fad'a masa a wannan.

"Wallahi sai na raba wannan yarinyar da duniya kamar yanda na raba iyayenta da duniya!!" Ya fad'a cikin 'kara yayin da yake tu'ki cike da ganganci, yana komawa gida yaransa da ya bari su shiga gidan Sarah sukace sun kasa shiga wani sabon 'bacin ran.

Ganin bai samu abinda yakeso ba ya sanyashi maida hankalinsa ga kamfanonin da zai iya mallaka kai tsaye wanda ya maida duk al'amuran kamfanonin hannunsa shi yake juyasu yanda yaga dama.

************
Mardiyya ta fara samun lafiya saidai kullum tana cikin tunanin fansar da zata d'auka ta iyayenta.

Kaman yanda suka saba sunje therapy cike da fara'a matar tace "Meeyah ya jikin naki?" Cikin harshen turanci

"Da sau'ki" Mardiyya ta fad'a tareda zuba tagumi tana kallon matar, "Deeyerh tunanin me kike?"

Sauke numfashi Mardiyya tayi tace "ina tunani ne hanyar da zanbi na kasheshi cikin sau'ki Kuma hanya mafi wahalarwa".

"Mardiyya...ri'ke mutum a rai ba abu ne mai kyau ba musamman duba ga lafiyarki....."

Tuni Mardiyya tayi zooming maganar matar tareda lumshe idanunta tana hango kanta a yayin da take aiki akan d'aukan fansarta, saida Mu'azzam ya ta'bota sannan ta dawo daga duniyar tunanin da take wadda tafi zamanta a wajen dad'i a cikin idanunta tana hango Mansur a wula'kance.

"Thank you Miss....."

"Megan". Matar ta fad'a tareda murmushi, kafin Mardiyya ta sake jin wani abu tuni ta fice.

"Mardiyya..."

Kafin Mu'azzam ya 'karasa tayi kissing d'insa sannan tace "hubby I am fiiiiiiiiine, nasan me kake 'ko'karin yi kuma hakan ya taimaka min sosai amma ina bu'katar wannan 'kiyayyar tasa a raina domin na cimma burina, Kar kace zaka hanani".

HASKEN RANA✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang