End

1.2K 133 12
                                    

_tsaye yake a gaban gawawwaki uku da aka fito dasu daga gidan Dr Abubakar, wani farin ciki ke ziyartarsa yayin da yake kallon abokin nasa wanda ya Tara dukiya mai matu'kar yawa, yayi suna a 'kasashe da dama yau shine a nad'e cikin leda._

_"Sir ka duba gawar saboda a tabbatar shine ko ba shi bane". D'aya daga cikin 'yan sandan dake kewaye da wurin ya fad'awa Mansur cikin girmamawa, wani dad'i ne ya sake ziyartarsa domin tun kafin a binne abokin nasa suna da d'aukakar da yake nema sun fara isowa gareshi._

_tsugunawa yayi gaban gawar ya bud'e zip d'in jikin ledar 'konanniyar gawar dake ciki ta bayyana, gawar tayi ba'ki 'kirin babu wanda zai gane mutum ne ma a ciki ko aljani._

_'ko'karin zuge zip d'in yayi cikin sauri saidai maimakon ya rufe gawar tamkar ma 'kara bud'ewa yakeyi, kama zip d'in yay8 ya ri'ke Yana turashi gaba da dukka 'karfinsa saidai tamkar bayayi, kallon wurin zip d'in yayi yaja baya a firgice_

_wani ba'kin hannu yaga ya fito daga cikin jakar ya Tare zip d'in, ja yayi da baya a tsorace tareda waiwaye, maimakon ma'aikata da 'yan jarida da suka zagaye wurin wasu halittu ya gani jikinsu a 'kone sunyi ba'ki wuta na fita daga idanunsu da bakinsu._

_guduwa yake Shirin yi wannan jakar ta gabanshi ta bud'e, wani ba'kin mutumi ne ya fito daga ciki siffarsa irin ta mutanen dake zagaye dashi saidai yanayinsa yana da matu'kar tsoratarwa domin iya kallon Mansur baiga 'karshen tsayinsa ba, rikid'ewa wannan mutumin yayi ya koma Dr Abubakar ya nufi Mansur yana murmushi_

_ A dur'kushe Mansur yace "abokina dan Allah ka taimakamin ka cetar dani daga wurinnan"_

_Cikin wata murya mai amo mutumin yace "har kasan Allah? A lokacin da kake 'konani ni da iyalina ka tuna akwai Allah?"_

_wani irin kuka mutanen dake kewaye da wurin sukeyi mansur na d'aga kansa ya ganshi a cikin gidan Dr Abubakar, wasu irin halittu ke fitowa jikinsu na kamawa da wuta suna ihu da naiman d'auki, muryoyinsu sunada matu'kar razanarwa_

_hannu Mansur yasa ya toshe kunnuwansa saidai wannan ihun tamkar ninkashi akeyi, mutane yake gani suna fitowa jikinsu ya Kama da wuta suna zubewa a gabansa suna 'konewa, cikinsu harda yara_

_mansur gaba d'aya ya gama gigicewa domin duk tunaninsa a jahannama yake, tashi mutanen sukayi suka zagayeshi idanunsu na fidda wuta wanna mai siffar Abubakar d'in yace "ka 'kona ni ni da ahalina ba tareda munyi maka laifin komai ba, kayi zaluncin da ire irena Basu yishi ba, ka cutar da rayuka da dama sannan kakeso ka tsira!!"_

_sake juyewa mutumin yayi 'barin jikinsa ya zama siffar mansur d'aya 'barin kuma siffar wata halitta daban, tsananin firgici yasa mansur ya kusa suma, kama wuyansa mutumin yayi ya sha'ke_

_mansur ji yayi tamkar ana 'kona wuyan nasa da wuta har cikin naman jikinsa yake jin zafin wutar, ga firgici ga azabar wuta ji yake tamkar ransa zai fita, ciki murya mai razanarwa mutumin yace "ka cutar da abokinka wanda bashida wata niyya a zuciyarsa face alkhairi, min zauna dashi zama na tsawon shekaru bai ta'ba cutar damu ba bamu ta'ba cutar dashi ba, amma kai saboda ba'kar zuciyarka ka cutar damu!! Sai na kasheka!!"._

_wuta ce ta fito a jikin hannun Wannan mutumin ya danna cikin mansur da wutar, wani gigitaccen 'kara Mansur ya saki tareda farkawa daga baccin wahalar da yakeyi.... _

Waiwaye yake a cikin cell d'in cikin tsoro da firgici, numfashi yake saukewa jikinsa ya had'a gumi, idanun mutum uku dake tare dashi ya gani a kansa a tsorace yace "kuyi ha'kuri".

Tsaki sukayi dukkansu suka koma bacci, zama yayi Yana maida numfashi sannan ya kai hannunsa wuyansa, janyewa yayi cikin sauri kasancewar wani rad'ad'i da yaji a wuyan nasa, wurin da ya ta'ba ma har fatar ta cire.

'menene yake faruwa dani?' ya fad'a Cikin ransa, mafarkinnan ke maimaituwa a cikin kansa yanajin ihun wad'annan mutane suna masa yawo, ga kumburarren hannunsa da yake masa zugi baisan ma yanda akayi yayi bacci ba, ga kuma wuyansa dake tamkar an kwara ruwan zafi.

HASKEN RANA✔️Место, где живут истории. Откройте их для себя