007

1.2K 125 8
                                    

"ki huta anan, akwai ruwan zafi cikin band'akin idan zakiyi wanka bayan kin gama sai ki fito ki fad'amin wacece ke sannan kici abinci". Tsohuwar ta fad'a da fara'a a fuskarta.

"Nagode sosai yakumbo Allah ya saka da Alkhairi". Mardiyya ta dur'kusa tana gaisuwa, d'akin ta shiga ta kwantar da babies d'inta kan katifar dake d'akin, yayi mata yanayi da na Hafsa saidai wannan ginin zamani ne sa'banin wancan siminti da siminti.

Toilet ta nufa ta kunna ruwa ta wanke gajiyar jikinta sannan ta d'auki twins tayi musu wankan suma, sallah ta gabatar da d'an kishingid'a bacci ya d'ebeta.

_"ki fita Mardiyya yanzu zamu fito kinji? Ki kula da jakarnan sosai ki tsaye jikin waccan bishiyar zamu fito yanzu"_

_Abba...bazan iya fita na barku ba Abba" Ta fad'a cikin shesshe'kar kuka dukda haya'ki na neman illatasu amma bata damu ba, idan har mutuwa zasuyi saidai su mutu dukkansu._

_Abu ya sanya ya toshe mata hanci yace "Mardiyya wutarnan 'kara yawa takeyi, mahaifiyarki.....ki bari naje na d'aukota inaso ki fara fita kafin mu biyoki, kiyimin al'kawari za'ki fita ki jiramu kinji? Ki yimin al'kawari bazaki dawo ba har sai mun sauko"._

_kafin ta amsa ya d'auketa a hannunta yana gumi tareda tari, gobarar da ta tashi ta fara yawa ga matarsa tana d'aki, 'kara yayi yayin da labule ya sauko kan hannunta wanda ya sanya hannun rigarsa kamawa da wuta, ajiye Mardiyya yayi ya bibbige wutar sannan ya d'auketa ya turata ta emergency exit d'insu, saida ya tabbatar ta gama taka benen ta sauka sannan ya juya._

_"ABBA!!! MAMA!!! ABBA!!!!!!!!!!" Sune kalmomin da Mardiyya ke furtawa, zubawa gidan ido tayi tana kallon wutar tana ci ta gama tabbatarwa ta rasa iyayenta har abada.....a cikin wannan hali na 'kunci ta 'kuduri niyyar kashe duk wanda ya kashe mata iyaye ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyyar rayuwarta...._

Farkawa tayi a tsorace saidai babu abinda ta tuna banda wuta, wuta ce take ci amma me take cin wani gida saidai menene fa'idar wannan mafarkin? Duk yanda taso ta tuna wani abu ta kasa banda wutar dake yawo a cikin ranta, sunayen da aka ambata ta manta, ita Karan kanta fitowarta a mafarkin ta manta.

Fuskarta ta shafa taji hawaye, kuka take kenan a mafarkin nata? Munin mafarkin har yakai haka?

"Kin tashi kenan".  A firgice ta dawo daga duniyar tunani sai yanzu ta tuna inda take, goge fuskarta tayi da sauri sannan tace "kiyi ha'kuri yakumbo wanka mukayi ne kuma ina niyyar fitowa bacci ya d'ebeni".

"Ai dake darene sannan ga gajiya, kukan yara naji nace bari nazo sai kuma naji sunyi shiru nayi zaton ma kin d'aukesu ne, amma kukan me kikeyi Mardiyya?"

"Babu komai" ta fad'a kanta a 'kasa.

"Kiyi ha'kuri a rayuwa komai mai wucewa ne kuma Allah yana jarabtar bayinsa ta hanyoyi da dama, ke taki jarrabawar kenan idan kika kar'beta da hannu biyu zakiga alkhairi ce a gareki, daga 'karshe zakizo kina godiya ga Allah da ya jarabceki ta wannan hanyar kiyi ha'kuri kinji? Bazan ce ki dena kuka ba saboda bakida hanyar fidda damuwarki sai wannan amma ki daure kiyi ha'kuri".

Kasa furta komai Mardiyya tayi domin kamae yakumbo ta karanci zuciyarta, tabbas ta gaji da wannan rayuwar da takeyi saidai maybe maganar yakumbo gaskiya ce, Allah baya jarabtar bawansa a banza, kuma yana jarabtar za'ba'bbu ne daga bayinsa.

Abinci yakumbo ta fita ta kawo mata sannan tayi mata sallama, bayan taci abincin bacci yayi 'kaura daga idanunta, sallolin dake kanta ta fara yi saida tayi sallolin kwana biyar, saura kad'an ta gama sallolin da ta rasa kafin ta haifi twins saidai sallolin da ta rasa a baya suke damunta, tasan batayi shekara a wannan halin ba cikin jikinta ma shaida ne, sannan idan har zatayi mummunan raunin da zai ta'ba mata 'kwa'kwala to da jaririn ciki gareta sai ya zube, tasan sallar watanni ake binta, wata d'aya zuwa biyar saboda haka zatayi ta sallah har hankalinta ya kwanta.

HASKEN RANA✔️Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang