Saida tayi kwanaki hud'u a asbiti taga dai da gaske an rabata da abinda ta haifa, ko nurses ta tambaya me ta haifa sai suyi mata shiru hakan ya sanyata shiga damuwa sosai.
Ranar da ta cika kwana hud'u doctor yazo dubata Mum bata nan, bayan ya dubata ya sanar mata za'a yi discharging nata yau idan suka koma gida da zaran taga matsala ta fad'a.
Yana gama bayaninsa tace "likita akwai abinda ke damuna".
Mamakin maganarta cikin nutsuwa yayi, tunda ta farka yake kallonta cike da mamaki domin dai yanayin jikinta zai tabbatar maka ba mai cikakkiyar lafiya bace, gashin kanta ba'a ganin kalarsa saboda 'kura ga ciwon dake 'kafarta wanda ke neman ru'bewa, yanayin rashin wanka da ya bayyana 'karara a jikinta amma farkawarta daga C.S halayyarta da dabi'unta babu alamun na mai ta'bin hankali.
"Ina jinki meke damunki?"
"Likita inaji a jikina abinda na haifa bai mutu ba, nasan da kai da Hajiya da kowa na asbitinnan akwai abinda kuke 'boyemin, nasani abinda na haifa bai mutu ba ku fad'amin gaskiya dan Allah". Mardiyya ta 'kare maganar hawaye na zuba daga idanunta.
Tausayinta ne ya kamashi saidai bashida damar fad'a mata gaskiya, dukda yaga duk alamun tana son 'ya'yanta, tuna maganar Mum yayi da tace haukan Mardiyya tashi yakeyi, idan ya sanar mata gaskiya haukan ya tashi yaya zaiyi?
"Mardiyya kinsan yayarki dai bazata miki 'karya ba, abinda ta fad'a miki gaskiya ne dukda zakiji ba dad'i ha'kuri zakiyi ki kar'bi hakan a matsayin 'kaddararki".
"Yayata kuma likita? Ni banida masaniyar yayata ce Abba d'anta ne ya fara taimakamin da abinci a lokacin da nake bu'katar taimako sannan ya nemi da ta taimakamin ganin ina na'kuda a titi".
"Daga ina kike wai ke?" Ya fad'a tareda kama gefe ya zauna domin bashida sauran aiki ita kad'ai ce patient a asbitin.
"Bansan wacece ni ba bansan daga ina nake ba, ina cikin hayyacina likita ni ba mahaukaciya bace yanda kuke kallona, na farka ne a jeji bansan inda nake ba, na tashi tamkar jaririn da yazo duniya yau domin bansan komai game dani ba, babu wanda yake niyyar taimakona shiyasa ka ganni a haka, kango shine makwancina nayi kwanaki cikin yunwa kafin na had'u da Abba ya fara taimakamin da abincin da zanci a kullum har wannan lokacin, likita idan akwai abinda sukayi da 'ya'yana ka fad'amin, nasan ba jarurit d'aya na Haifa ba mahaifar 'ya'yana ta nunamin haka, ka taimakamin bansan mutanennan ba taimakona sukayi banaso su cutarmin da 'ya'yana".
Tausayinta sosai yaji sannan ya sake amincewa da hukuncin da Mum ta yanke na kar'bar 'ya'yan, idan har a kango take kwana ina zata kai 'ya'yan nata?
Ha'kuri ya sake bata ya tabbatar mata abinda ta haifa ya rasu, ba don ranta yaso ba ta ha'kura saidai kawai tasan babu yanda zata yi.
Bayan Isha Mum da Abba suka d'auketa, 'bangaren masu aiki ta kaita tace su gyarata.
Wanka aka fara mata aka wanke mata kai, dattin dake jikinta har saida taji kunyar kanta musamman gashin kanta tamkar tayi birgima a cikin datti.
Bayan an mata wankan suka had'u suka fara tsefe kitson dake kanta, sun d'auki lokaci suna tsifar sabida 'kananun kitso ne a kanta ba'a ma ganesu saboda tsufa.
Bayan sun gama suka tufke mata gashin sannan ta kalli kanta a mudubi, murmushi tayi ganin yanda ta fito fes da ita sa'banin kafin tayi wanka, saida tayi nadamar kallon mudubin domin suffarta ta bata tsoro amma yanzu ta fito a mutum.
Zuwa Mum tayi ganinta saida tayi mamakin matar da ta gani, ta banbanta da waccan dake rufe da daud'a tayi fes kyawunta ya bayyana, kallon gashin kanta tayi a ranta tace 'dole 'yan biyunta suyi gashi masha Allah".
Gaida Mum Mardiyya tayi sannan tace "Hajiya nagode da taimakona da kikayi Allah ya saka da alkhairi Allah ya biyaki, bansan dame zan biyaki taimakon da kika min ba".
YOU ARE READING
HASKEN RANA✔️
Mystery / Thrillerwacece ita? menene sunanta? inane garinsu? suwaye iyayenta? wace irin rayuwa ta gudanar a baya da ta tsinci kanta a wannan hali? ta farka a tsakiyar ciyayi, bata tuna komai na rayuwarta ko da sunanta, mutane suna mata kallo na daban wasu na zarginta...