025

973 94 12
                                    

Eid Mubarak to you all, Allah ya 'kara mana nisan kwana ya maimaita mana ya bamu ladan ibadar da mukayi.

25

Kwana biyu suna Shirin dawowa suna fasawa domin Mu'azzam tamkar ma a yanzu ya fara jin dad'in garin domin har mamaki Mardiyya keyi yanda yake sakewa da wasu matasa na cikin garin, fita yakeyi cikinsu su zauna suna hira abinda bata ta'ba tunanin zaiyi ba.

Kayan da taje dasu garin duk ta bayar wad'anda zata dawo dasu kawai ta bari a jikinta, haka ma kayan twins da sauran kayan amfanin da tazo dasu.

Shima Mu'azzam kayan da yazo dasu duk ya first ya bayar, ranar da zasu baro garin yayi rabon kud'i sosai manya da yara haka suka baro garin ana saka musu Albarka da yi musu fatan alkhairi.

"Garinnan suna da bu'katar abubuwan rayuwa da dama, Kinga da za'a musu fanfo ko borehole ba 'karamin amfana zasuyi ba domin rafin da suke de'bo ruwa yanada nisa". Mu'azzam ya fad'a yayin da suka d'auki hanyar fita daga garin.

"Hakane hubby and apart from that sunada wahalar abinci dukda suna noma amma basu noma kayan abincin da zasu gina musu jiki, da za'a samu hanyar shigar musu da kayan rayuwa za'a Samu sauyi sosai, idan muka gama da wannan issue d'in zamu dawo kansu yanzu ya kake ganin zamu fuskanci wannan mutumi".

"wannan issue ke da Sarah zaku tattauna, kuyi magana da lawyer d'in Abba Akan shigar da 'kara shi yasan hanyoyin da zaibi abubuwa su zo muku da sau'ki, tabbas akwai challenges da zasu taso sosai sai kun jure".

Murmushi Mardiyya tayi tace " hubby wani challenge ne bamu ganiba a baya? Wannan da zai taso ai ba komai bane Akan rayuwar da mukayi ko ma muke kan yi, Addu'a ce Zamu cigaba dayi".

Shiru sukayi yaci gaba da driving d'insu hankalin Mardiyya yana can wurin Sarah tana tunanin tashin hankalin da 'yar uwar tata zata shiga na rashin jinta a wannan tsawon kwanakin, Addu'a takeyi Allah yasa tana lafiya kuma bata koma Kaduna ba.

Tana ri'ke da wayarta tana kallo tana jiran network ya dawo, saida suka fara dosar wani babban 'kauye sannan network d'inta ya dawo, hannunta har rawa yakeyi cikin sauri ta shigar da number d'in Sarah ta kira ta da 'kyar ta samu kiran ya shiga.

"Mardiyya what is wrong with you!! Meyasa kikemin haka dan Allah kinsan tashin hankalin da na shiga saboda rashin jinki? Na tambaya a KD ba wani labari na Mu'azzam ko naki me kukeyi haka dan Allah?" Sarah ta fad'i maganar Cikin numfashi d'aya.

"I miss you Sarah, yaushe kika koyi masifa haka?". Mardiyya ta fad'a tana murmushin Jin dad'in sanin Sarah na lafiya. Tsaki sarah tayi tace,

"Abinda zaki ce ma kenan ko? Bayan kin barni cikin damuwa da tashin hankali amma kina zancen yaushe na koyi masifa ko?"

" Sorry sisterna kebbi naje wurin dangin Abbanmu, na samesu kuma".

" Alhamdulillah da gaske kin gansu Dee-dee? Kin tabbatar su ne?"

" Iya tabbatarwar da nayi Sarah sune, zakiyi mamakin yawan dangin da muke dasu amma muke rayuwa cikin kad'aici da 'kunci, a yanzu na shirya na kawo 'karshen komai domin muma muyi rayuwa kamar yanda kowa keyi cikin kwanciyar hankali ba tareda fargaba ba". Mardiyya ta fad'a tana tunanin respond d'in da Sarah zata mata idan taji niyyar dake ranta.

" Me Zamuyi kenan Dee-dee? D'aukesu zamuyi mu samu wani garin da Mansur bazai iya samun mu ba mu zauna tare dasu ko Yaya?" Sarah ta fad'a muryarta na nuna alamun akwai abinda take suspecting,

" Kotu zamu shigar dasu".

"Kotu? Are you insane!! Mansur d'in zamu kai kotu? Dee-dee kinsan wanene Mansur a yanzu? A wad'annan shekarun Mansur yayi shaharar da yake neman doke abbanmu lokacin da yake raye, 'yan siyasar da suke tare da Mansur sunada yawan da bana tunanin zamu iya cin nasara a kansa, Mardiyya wa muke dashi da zai tsaya mana? Abokanan Abba dukkansu abokan Mansur ne a wannan rayuwar da ake amfani da kud'i wajen saye imanin mutane Mansur zaiyi komai dan ganin kowa ya juya mana baya, Kar mu fara ya'kin da bazamu ci galaba a kansa ba".

HASKEN RANA✔️Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum