003

1.3K 133 1
                                        

UPDATED VERSION

"A'a Mum please, kar muyi haka bamu san wacece ita ba mu bata 'ya'yanta kawai". Abba ya fad'a cikin girmamawa.

"Ka fini sanin abinda ya kamata kenan ko? Da bakinka ka sanarmin Mahaukaciya ce ita, ta yaya zamu bar mata 'ya'ya har biyu? Dole ne a kar'besu ko kuma ta cutar dasu da haukan nata, idan kuma ba mahaukaciya bace zuwa zata yi ta jefar dasu a hanya ana kallo, kar'bar yarannan zamuyi and that final tunda har Hanan tace tanaso zanyi iya 'karfina na kar'besu day gareta".

Bud'e baki Abba yayi zaiyi magana Mum ta d'aga masa hannu ba don san ransa ba yayi shiru, Hanan tana ri'ke da dukka yara biyun ta zuba musu ido ko 'kiftawa bata yi.

Zama sukayi suka tsara zancensu in case za'a musu tambayoyi a kanta har Abba saida ta ja mishi kunne ya bada haɗin kai sannan hanan ta kirawo masu aiki suma ta karanta musu.

Office d'in doctor Mum ta nufa lokacin da aka kirata domin sanar mata da yanayin da mai jego ke ciki, bayan sun gaisa yace

''Kamar yanda muka miki bayani mai jego da yaranta are both okay alhamdulillah saidai yaran sun zo underweight suna buƙatar kulawa sosai, zamu kaisu nursery yanzu ayi monitoring ɗinsu for 24-48 hours''.

''Ita kum mai jego kun ce sunanta...'' File ya buɗe yace ''khadija ko?" Da sauri Mum tace ''eh, hakane khadija sunanta, me ya faru da ita?"

''Babu komai muna buƙatar bayanai ne saboda yanayin da aka kawota a ciki, muna son mu san alaƙarku da ita saboda irin wannan cases ɗin muna reporting idan ya kasance tsintar patient ɗin akayi ko makamancin haka''.

''A'a doctor ba tsintarta mukayi ba, ƴar uwata ce''.

Kafeta yayi da idanu yace ''wajen signing consent form ɗanki baiyi indicating ƴar uwa bace, sannan yanayin da aka kawo ta ma kamar mahaukaciya ce''.

''Doctor Abba baya cikin hankalinsa ne ya kasa indicating ɗin saboda shi bai taɓa ganin mace na labour ba, ko driving da yake ya kusa haɗa mu da traler a hanya, sannan abubuwan da aka rubuta ana so ya siyo kana gani saida yayi shirme, ƴar uwata ce tana da taɓin hankali wanda idan ya tashi sai a nemeta a rasa''.

Hawayen ƙarya ta fara tace ''last time da ta fice ne tsautsayin waɗannan yaran ya afka mata wanda ya saka condition ɗinta ya sake tsananta, tunda ta fita cikin na wata shida bata dawo ba sai jiya shim naƙuda ce ta hankaɗota gidanmu, ana faman ta sauke lafiya wa zaiyi tunanin yi mata wanka? Tunda ta fara naƙudar take cewa sai ta kashe duk abinda ta haifa shiyasa ma nake tsoron ta farka ta san cewa ƴaƴa biyu ta haifa''.

''Idan baka yarda da ni ba ga ƴaƴana nan, ga masu aikina na gida wanda suna hanyar zuwa ka tambayesu duk zasu tabbatar maka da abinda na faɗa, ko ita ce tace muku ba ƴar uwata bace? Wahalar da na sha da ita a baya ta isheni dan Allah kar ku ƙaramin wata a yanayin da muke ciki''

Ganin tana ƙoƙarin matse ƙwalla ne ya sanya ya sallameta bayan yayi mata tambayoyi kan lafiyar ƙwaƙwalwar mai jego da kuma referring ɗinsu zuwa psychiatry idan ta farka.

Har ta mishi godiya ta fita ta kom tace ''dan Allah doctor muna neman alfarma kar a sanar da ita abinda ta haifa yana raye saboda komai zai iya faruwa, ni zan bi ta hanyar da zata fahimta na sanar mata''.

Shiru yayi yana tunani sannan yace ''sai yanda muka ga ta farka ɗin ba zan ɗaukar miki alƙawari ba''.

Cikin murna Mum ta bar office d'in ta nufi wajen Hanan da ke nursery wajen yaran, ganin murmushi a fuskar Mum ya sanya itama Hanan ta saki murmushi tasan cewa sunyi nasara

_gudu take tana waiwayen bayanta cikin tsananin firgici, "Kar ku Bari ta 'bace muku kun sani cewa idan har bamu kaita ba kashemu zaiyi dukkanmu". Taji wani daga cikinsu na fad'a, gudu takeyi tana nadamar sanya takalmi mai tudu, ganin takalmin na bata wuya yasa ta jefar dashi, bata lura da dutsen dake gabanta ba saida taje dab dashi, a firgice ta ja da baya yayin da 'kafarta ta zame, wani itace dake jikin dutsen ne ya ri'ke rigarta, tana kallo rigar ta fara yagewa har takai 'karshe, rufe idanuwanta tayi tana ambaton kalmar shahada yayin da kanta ya bugi wani dutse, jini taji Yana zuba daga cikin kan nata kafin duhu ya mamaye ta.......

HASKEN RANA✔️Stories to obsess over. Discover now