🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
* _PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️✍️✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮✤✤✤ *_sᴀᴅᴀᴜᴋᴀʀᴡᴀ_* ✤✤✤
👇👇👇*Sα∂αυкαrωα gα 'yαท υωα, αвσкαi, мαsσyα ∂α ∂υккαท мαsυ кαrαทτα ℓiττατταƒαท нαυsα. Aℓℓαн yα вαr ʑυмυทci.* 💝💖✌
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_*
*Dukkan godiya da yabo marasa iyaka sun tabbata ga Allah mahaliccin kowa da komai, tsira da amincin Allah su kara jaddada ga Annabi _MUHAMMAD_ ((Sallallahu Alaihi Wasallama)).*
*Shɑfi na ❶ & ❷*
"Assalama alaikum, salama alaikum mutanen gidan nan ba kwa amsa sallama ne? Ko babu kowa a gidan ne?"
Me yin sallamar ta dan numfasa ta ji ko za'a amsa mata, amma dai shiru. Sai ta matsa ta cigaba da rafka sallama,
"Salama alaikum, salama alaikum, ikon Allah! Watakila dai babu kowa a gidan, amma kuma sai su fita su bar gida a bude babu kowa haka."
Rufe bakinta keda wuya sai ta ji motsin tafiya daga cikin falon gidan bayan da ta matso kusa da kofar. Mai gidan ne ya taso daga bacci, short nicker ne a jikinsa kawai ko singlet babu, ya leko yana sakin mika, baccin ma bai gama sakin idonsa ba. Yarinyar da ke ta kwada sallamar ta yi saurin sunkuyar da kanta kasa tare da juyawa, ganin a yanayin da ya leko. Juyawar shima ya yi da saurin lokacin da ya fahimci wacece ta zo, jallabiya ya sako sannan ya sake fitowa ya ce,
“Humaira ce a gidan namu, sannu da zuwa. Bisimillah shigo mana.”
Ta dago kai tare da bin bayansa cikin falon suka zauna bisa kujeru mabanbanta. “Ina yini.” Ta gaishe shi hade da tambayar, “Ina Anty Sakina, bata nan ne?”
Ya amsa mata da cewa, “E yanzun nan ta tafi gidan kitso, lafiya dai ko?”
“Lafiya lau dama na zo nan kusa daku ne gidan wata kawata shine nace bari na biyo mu gaisa.”
“Gaskiya ya yi kyau wallahi kin kyauta kuwa. Ya mutanen gidan?”
“Duk suna nan lafiya kalau, bari na koma idan ta zo a fada mata cewa na zo.”