Shɑfi nɑ 25 & 26

6 0 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

      ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
      ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*_Shɑfi nɑ 25 & 26_*

Zaman suka yi a kan kujeru nan waje domin su jira a rage layin da suka tarar a wajen. Suna zaunen suka fara hirarsu iri-iri suna ta kallon jama'a kala-kala na ta kai da kawo, kowa da hidimar da ya sa gaba. Cikin hirar da suke har zance ya zo kan batun karatun sakandire da yadda kowannensu ya rubuta jarabawar kammala sakandiren wato (WAEC). A nan ta ne Humaira take tambayar Binta, “Wai ni kam wace makaranta kika gama?”

Binta ta nisa tare da cewa, “GGSS JOGANA, amma ba ma a wannan shekarar na Candy ba. Shekarar da ta gabata ne, to matsala aka samu a lokacin da muka rubuta jarabawar darasin lissafi an samu bulllar satar amsa da yawa a ranar. Dalilin da yasa aka soke duk jarabawar makarantun da ke wannan shiyya.”

“Ayya! Allah sarki, ashe kina gaba da ni kenan. Sannan kuma ga shi makarantar kwana, gaskiya na jinjina miki kin yi kokari sosai. Ai ni ba zan iya matsa wa na bar Mummyna ba har a kai ni makarantar kwana ni kadai babu wanda na sani. Kuma ga shi an ce ana ladaftar da mutane da duka sosai, hatta Perfects ma duka suke, lallai kin yi kokari.”

“Hmm! To ya za ayi dole mutum ya yi hakuri wataran sai labari, yanzu ni ba ga shi ba kamar ban yi ba. Ke wacce kika yi ne?”

“Ai ni a cikin garin ma ina kusa da gida, GGSS MASAKA ce, ko ihu na yi za a jiyo daga gidanmu a kawo mini dauki.”

Dariya suka yi gabadaya, Binta ta dora da cewa, “Ke amma ba ki da dama wallahi, to me zai same ki ma. Kuma ni duk zuzuta wahakar boarding school da ake ban gani ba, wani abin ma mutane ke kara wa. Amma sam ba haka abin yake ba, kawai dai abinda makarantar kwana ta fi jeka ka dawo shine halin da'a da nagartar karatun. Babu shakka daliban Boarding school sun fi na Day discipline da kuma academic performance.”

“E haka ne kuma gaskiya akwai wannan bambancin, tunda kin ga kuna can makaranta a kambame dindindin na tsawon zangon karatu, babu wani abu da za ku yi idan ba karatun ba.”

“Yawwa kin gane kenan, shi ne da ma don haka dole mutum ya yi karatu koda baya so.”

Suna nan a zaune suna ta hirar kimanin mintuna goma sha biyar sai ga wani mutumi nan ya tunkaro inda suke. Sadik kenan shi ne mai cafe din. Tun kafin ya iso ya hango Humaira, idonsa akanta ko kiftawa baya yi. Kai tsaye ya karasa daf da su ya tsaya bisa kan Humaira tare da cewa, “'Yanmata sannu da hutawa.”

ƘUDA BA KA HARAMWhere stories live. Discover now