🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 13 & 14*
Kimanin sati guda kenan da dangantaka ta yi tsami tsakanin Usman da Anty Sakina, cikin mako daya tak! Zaman doya da manja ne kawai ke wanzuwa. Babu wani abu dake hada su face yin sallama da kuma amsawa, sai kuma a dawo lafiya idan ya ce da ita zai fita ko kuma ita din za ta fita. Babu abinci a gidan, don haka baya saka ransa idan ya dawo ta kawo masa balle ya tambaya. A waje yake cin abincin kowanne lokaci, safe dare da kuma rana.
To dama dai ita Anty Sakina ke kawo kayan abincin da suke ci, a wajen aikinta take daukowa a matsayin rancen da ake bawa ma'aikatan idan suna bukata, sai a rika cire kudin kadan-kadan a cikin albashinsu. Don haka yanzu kuwa da haka ta faru tsakaninsu sai ta ki karba. Ta kanyi girki amma kadan take daidai cikinta, ba ta yi dashi.
A ranar Lahadin cikar makon ne Usman ya je wani kanti a nan cikin unguwarsu ya sayo wasu kayan abinci da suka hada da karamin buhun shinkafa, da carton din macaroni, sai garin semonvita leda uku ya kawo mata. Kwance take kan kujera a falo tana bacci, ya shigo da kayan. Taba ta ya yi tare da cewa, “Tashi mana.”
Farkawa ta yi bude idon tana daga kwancen ta ce, “Ya ya dai me ya faru ne, lafiya?”
Zama ya yi kusa da kafafuwanta sannan ya ce, “Tashi zaune mana, ga wadannan kayan, ayi manage dasu bashi na karbo su wajen Danliti mai kanti. Yanzu abin da nake so dake ki yo mana ragowar cefanen sai a cigaba da yin girki kamar yadda aka saba.”
Kallonsa kawai ta yi fuskarta ba yabo babu fallasa, babu fishi kuma babu fara'a ta nisa tare da cewa, “Sai yanzu ka gaji da daukar alhakin ne? To ai tunda ka ciyo bashin wadannan kayan ragowar ma sai ka koma ka ciyo bashinsu. No babu inda zan je na sake karbo kaya.”
“Kin ga Sakina bana son wannan taurin kan naki, komai ya riga ya wuce kawai, kin yi abin da kike so ban kula ba ya kamata ace kin huce kin sauko daga dokin zuciyar da kika hau.”
“Hmm! Usman kenan, ce maka aka yi fishi nake? Kai ne baka so a fada maka gaskiya, duk abin da ka yi daidai ne. I Kai gwani ne ba ka yin kuskure, don haka ba ka daukar maganar kowa. Ban yi haka don na yi maka gori ko tagayyaraka ba, hakkinka ne na bar maka ka sauke. Maganar gaskiya ba zan sake dauko komai ba a matsayin loan, idan kana bukata alfarma daya zan yi maka, ita ce idan anyi albashi ka bani kudin sai na sayo maka.”