Shɑfi nɑ 73 & 74 (Ƙarshe)

6 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑn yi don cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Shɑfi nɑ 73 & 74*
      *(Ƙarshe)*

Usman ya sunkuyar da kai kasa ya gaza yin magana, DPOn ya dora da cewa, "Na ba ka dama tun kafin a zo wannan gabar, ka fito da yarinyar nan amma ka ce ba ka san zancen ba. Saboda haka yanzu doka za ta yi aikinta a kanka. Kamar yadda ka taka doka ita ma za ta taka ka, ka ci zarafin aikin dansanda. Ka dade kana aikiata rashin da'a da kakin gwamnati. Kashedi an yi maka ya fi sau shurin masaƙi, amma ka yi kunnen uwar shegu da mutane. To idan ka ki ji na tabbata ba za ka ki gani ba. Hakazalika duk dan da ya ce uwarsa ba za ta yi barci ba, to la shakka shi ma ba zai runtsa ba."

Yana kawowa nan a zancensa ,ya kira wani kurtun dansanda ya umarce shi da ya tisa keyar Usman zuwa cell. DPOn da kansa ya rubuta zungureriyar takarda mai dauke da dukkan tuhume-tuhumen da ake wa Usman da korafe-korafe, zuwa can Shalkwatar 'Yansanda. Bayan zuzzurfan bincike, aka sallami Usman daga aikin dansanda kwatakwata kamar yadda dokar aikin ta tanada. To ma iya cewa, ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata. Karshen tika-tiki-tik, karshen alewa kasa in ji masu iya magana.

Bayan sati daya da korar Usman daga aiki, sai mahaifiyarsa ta kwanta dama, Allah Ya yi mata cikawa. Da ma mahaifinsa ya rasu. Tashin hankali goma da ashirin ya same shi, cikin dan kankanen lokaci sai da ya rame, abinka da mai garin jiki. Laila ba ta san an kore shi daga aikin ba, domin bai sanar da kowa ba. Sai bayan addu'ar bakwai ta mahaifiyarsa sannan yake fada wa Laila din. A karyar da ya tsara mata ta girgiza sosai kuma ta tausaya masa, daga karshe ta yi masa addu'ar fatan alkairi da samun wani aikin cikin gaggawa.

      *BAYAN WANI LOKACI*

To a halin yanzu dai ma iya cewa, rayuwa ta fara sauyawa Usman, gararamba ce ta zame masa aiki. Kodayaushe yana majalisa, sai caca, abin da ya rika ke nan a matsayin hanyar samun abin batarwa. Watarana ya yi nasara, wataranar kuma a yi nasara a kansa, da ma haka sana'ar caca ta gada.

Lokacin da ya cika watanni uku cif da kora daga aiki, Laila ta haifi 'ya mace kyakkyawa da ita, tubarakAllah Ma Sha Allah! Satin suna ya kewayo aka sa wa jinjira sunan mahaifiyarsa  wato Maimuna, amma bai yi mata hakika ba. To wannan ke nan.

Ita kuwa Anty Sakina, jinjina bukatar yaya Ahmad take, tunani ta yi zuzzurfa daga karshe ta sallama. Da ma dai ba ta ki ba ne, ko dan rashin sanin halinsa, yaya Ahmad mutum ne na-gari. Saboda haka soyayya ta rika nuna masa, shakuwa ta wanzu a tsakaninsu, suna bala'in son junansu abin sha'awa tamkar babu wata kaddara da ta same su a baya. Dukkansu suna zumudin ganin kasancewarsu ma'aurata, kulawa da tarairaya sosai Anty Sakina take nuna wa yaya Ahmad. Su da kansu suka tsayar da watan bikin da ranar daurin aure. Wannan biki dai zai kasance irinsa na farko, naira za ta koka sosai. Kai a tsaya ma bayyana irin shirin da aka yi ya zama kauyanci, su Anty Zara'u kuwa murna baki har kunne, farinciki ba ya misaltuwa.

ƘUDA BA KA HARAMWo Geschichten leben. Entdecke jetzt