Shɑfi nɑ 51 & 52

6 1 0
                                    

🐝 
🐝🐝 
🐝🐝🐝 
🐝🐝🐝🐝 
🐝🐝🐝🐝🐝🐝 
       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*  
             🐝🐝🐝🐝🐝🐝 
                      🐝🐝🐝🐝 
                          🐝🐝🐝 
                              🐝🐝 
                                  🐝


*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*


_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

👮👮👮👮👮👮👮👮👮 
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑn yi don cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️ 
👮👮👮👮👮👮👮👮👮


*Shɑfi nɑ 51 & 52*


Wani irin wulakantaccen kallo Humaira ta bi Binta da shi sannan ta ce, “Allah Ya jarabce shi da son mu ko dai Ya jarabce shi da so na? Ke ai ba son ki yake ba, ke ce dai kike ta cusa kai kina masa tallar kanki amma sam ba ya son ki, ni yake so. Don haka ki gyara lafazin bakinki malama.”


“Hmm! To Alhamdulillah! Na ji aje a hakan, ni dai na san yaya Sadik ko a mafarki ba zai ce ba ya so na ba. Domin ba a fi ni zannuwa ba, to ba za a baɗa mini kwarkwata ba. Ina da sura da diri ba yabon kaina nake ba, zance ne ya kawo hakan kuma komai hassadar mahassadi idan ya bude idonsa ya dube ni zai shaida haka, to don haka Allah na gode maKa da ba Ka ba ni izza da wulakanci ba. Kuma ina son ki sani na fi ki da na ce ina son sa, ke kuwa fa? Bullensa ya karya ya gabatar miki da bukatarsa amma sai kika yi fatali da ita, ba ki duba kima da martabarsa ba.”


Cike da tsananin mamakin yadda Binta ta zage sai fada mata maganganun da ranta yake so take yi, ta dube ta sannan ta ce, “Lallai yau kin fito mini a asalinki, da ma ashe haka kike? Ba shakka na yarda da maganar mutane, *'mutum shege ne.'*”


Binta ta yi wani shegen murmushi me cusa takaici sannan ta ce, “Ban gane na fito miki a asalina ba, da ya nake? Magana ce ta gaskiya, bawan Allahn nan ya ce yana son ki, ke kuma kin ce ba kya son sa, to ba shi kenan ba sai ki rabu da shi ya yi sha'anin gabansa; duk ma wacce zai so ke ina ruwanki? Amma kin dame shi, kodayaushe zancensa. Kuma tun farko sai da na ce miki ki tsaya ki yi tunani game da shi, samun namiji kamar yaya Sadik me tausayi da kulawa abu ne mai matukar wahala a zamanin nan, amma sai kika yi kunnen uwar shegu da ni. Saboda haka ban ga dalilin da za ki damu kanki ba. Kuma gaskiya na fada miki ba zan iya zuwa makarantar nan ba ba tare da na je wajensa ba, hasalima kin ga ya koya mini aikin café ina taya shi.”


“To shi kenan tunda kin ce haka, kin yi da 'yar halak. Idan na sake fada miki gaskiya duk abin da kika yi niyya ki yi mini.”


“Allah Ya huci zuciyarki, ni ban ce ba na son ki fada mini gaskiya ba, amma yanzu mene ne illar yaya Sadik? Malami ne babba fa a makarantar nan, duk da ba ya koyar da mu ai yana da matsayin da za mu girmama shi. Ko ba ki duba komai ba ai kin duba darajarsa ta malami, kin san da wahala ya ce yana son ki ba auren ki zai yi ba, duk da cewa akwai masu irin wannan hali amma shi dai daban ne.”

ƘUDA BA KA HARAMWhere stories live. Discover now