🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑ yi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑn yi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑn yi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 65 & 66*
To zance duniya dai ba ya buya, an ce magana ko kai kadai ka yi ta, wataran za ka iya jin ta a bakin wani. Kawo yanzu dai Najib da mahaifiyarsa sun samu labarin abin da ya faru da Humaira. Da farko dai ita mahaifiyar Najib din ta ja dunga ta nuna rashin amincewarta. Sam ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa, a cewarta, danta daya tilo ba zai auri sauran titi ba. An kai gwaro an kai mari, an kuma kai ruwa rana sosai kafin daga bisani ta sauko ta amince. Da ma dai shaidan ne ya so ya yi wasa da tunaninta, amma cikin ikon Ubangiji sai shi Najib din bai yi fushi ba, bai kuma tayar da hankalinsa ba. Cikin dabara da tattausan harshe ya buga wa mahaifiyar tasa wani misali wanda ya daure ta da jijiyoyin jikinta.
Misali ya buda mata da cewa, "Mama, yanzu idan ya kasance Humaira a nan gidan Allah ya kaddara a nan gidan ta fito, ma'ana ke ce kika haife ta, sai wannan lamari ya faru da ita; wani saurayi kuma ya zo yana son ta tun asali har ma ya yi alkawarin auren ta, sai mahaifiyarsa ta ce ba ta yarda ba, ya ya za ki ji a ranki? Ki kalli yadda aka ce abin ya faru, ba da yardarta ba ne, ya yi amfani da dabaru iri-iri ya yaudare ta. Kowa ya shaida Humaira yarinyar kirki ce, babu wani aibu ko mugun hali da aka taba samun ta da shi. Wannan abu iftila'i ne ya fada mata, wanda kuma bai kamata a ce ni na guje ta saboda haka ba. Idan aka ce duk matan da irin wannan abu ya taba faruwa da su ba za a aure su ba, to ya ya za su yi da rayuwarsu? Kin ga kamar an ce su je su ci gaba da aikata alfashar ke nan. Ki tuna fa, wasu matan ma sun bar gidan iyayensu sun shiga bariki yawon duniya harkar karuwanci kawai suka sani, amma za ki ga wasu mazan bayin Allah sun yi jahadi sun aure su domin su raba su da waccan kazamar rayuwar mai hallakarwa. Babu shakka idan na juya wa Humaira baya, na ki auren ta to hakika ban yi musu adalci ba, da me za su ji? Ki duba yadda har Anty Sakina ta rasa aurenta fa! Don Allah Mama ki yi hakuri, ki yi mana addu'a kawai."
'Da da uwa sai Allah! Tausayinsa ne ya ratsa zuciyarta, yayin da nasihohinsa ke ta kewaya mata zuciya, sun shiga ranta sosai babu shakka abin da ya fada gaskiya ne, bai kamata a kyamaci Humairar ba. Don haka buda bakin da za ta yi sai ta ce, "Allah Ya yi maka albarka, Allah Ya ba ku zaman lafiya da zuri'a dayyaba. Ita ma Allah Ya yafe mata Ya kara tsarewa."
Ya amsa cike da murmushi, "Amin Ya Allah, na gode sosai Mama."
Madalla! Haka ake son 'ya'ya su rika mu'amalantar iyayensu da kyakkyawar dabi'a, a duk lokacin da aka zo batun aure ko wani al'amarin to lallai mu bi zabin iyayenmu. Kada mu daga musu murya har ransu ya baci. Iyayenmu ba za su taba zaba mana abin da zai cutar da mu ba. Duk fadin duniyar nan ba mu da masoya na hakika sama da su, babu wani mahaluki da zai nuna mana soyayyar da ta fi ta iyaye. Wallahil Azim! Ko ita budurwar ko kuma shi saurayin bai kai iyayenmu son mu ba.