Shɑfi nɑ 57 & 58

3 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Shɑfi nɑ 57 & 58*

To, fitar Anty Sakina ke nan ta isa titi ta tari Adaidaita Sahu, ta yo wa gidansu tsinke, zuciyarta a tunzure kamar ta fashe. Tun a cikin Adaidaitar take jin wani sabon kukan na neman balle mata, amma ta daure. Suna tafe kafin a iso da ita gida ta fara binciken wayar Humairar, domin abin da ya daure mata kai shi ne, yadda alaka ta kullu tsakanin Usman da Humaira har ya samu lambar wayarta. Kuma har suka yi sabon da mu'amala irin wannan take wanzuwa a tsakaninsu?

Lambobin wayar ta rika bi tana bincika daya bayan daya, har ta ga lambar Usman din an yi saving da suna *Yaya Usman.* Bayan nan sai ta shiga binciken wayar lungu da sako, ciki da waje. A cikin sakonnin karta-kwana wato (SMS) ta ga abubuwan da kanta ya sake kullewa hade da sara mata, irin zantukan batsar da Usman yake tura wa Humaira.

Tunani ta shiga nan da nan, shin yaushe Humaira ta zama haka? Anya ma  Usman din kawai take kulawa, ba a makaranta ba ne kuwa ta hadu da mutanen banza suka sauya mata rayuwa? Sai dai bayan ta gama bincikar sakonnin sai ta takaita zarginta akan Usman, domin ba ta samu wani koda sau daya ba ya taba turo mata irin makamancin sakon da shi Usman din yake turo mata. Ko Najib da zai aure ta ba ya mata sakon karta-kwana, sai dai ya kira ta kawai. Kuma akalla ya yi kusan sati uku bai kira ta ba saboda ba cika sauraren sa take ba. Tun uzurin karya da ta gindaya masa na cewa ba za ta iya hada karatu da soyayya ba, ya sa shi numfasawa da kiran nata ko ma zuwa zance.

"To kodai yarinyar nan tana kallon fina-finan batsa ne? Har hakan ya kai ta jefa rayuwarta cikin wannan hali?"

Tunanin da Anty Sakina ta yi ke nan wanda kuma ya haska mata cewa ta sake kutsawa cikin wayar dai da bincike, domin waya waje ne da akan samu bayanan sirri game da mai ita. Hakan kuwa ta yi, cikin memoryn ta shiga da nufin ko za ta gani irin wadancan bidiyoyi da take zargin Humairar na kalla. Tana budewa, folder farko Audio ne, ta shiga ta duba, duk wakokin Hausa ne na 'yan nanaye. Folda ta biyu kuma an rubuta *Call Recorder*, wato wayar tana da tsarin nan na idan mutum ya yi waya, za ta nadar masa muryoyin zantukan da suka tattauna ta ajiye a cikin memorin. Budewa ta yi, ga jerin muryoyi nan da yawa, recording na farko da ta cikaro da shi shi ne, na maganar da Humairar ta yi da Usman dazu da safe lokacin da ta fito daga gida take sanar masa cewa tana kan hanya. Jin wannan murya ya sa Anty Sakina ta girgiza kai hade da jinjina lamarin. Haka nan ta rika bude muryoyin daya bayan daya tana sauraren abubuwa marasa dadin ji, har aka kawo ta kofar gida ba ta iya gama sauraren su gabadaya ba. Wani recording din ka ji suna tattauna wajen da za su hadu, a hotel kaza, da dai sauran wuraren da yake daukar ta ko kuma ya kira ta zo su sheke ayarsu.

"Wannan ma sun isa hujja."
Ta fada a ranta daidai lokacin da Mai Adaidaita Sahun ya tsaya cak a kofar gidansu, ta zaro kudi ta biya shi kudinsa ta sauka ta shige gidan. Mummy na kitchen tana dafa abincin rana, ita kadai ce a gidan su Haidar na makaranta. Anty Sakina ta yi sallama hade da zubewa a tsakar gida ,hawaye suka fara zarya a kan kuncinta.

ƘUDA BA KA HARAMWhere stories live. Discover now