🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*_Shɑfi nɑ 33 & 34_*
Misalin karfe 5:30pm na yammaci ln ranar Anty Sakina ta shirya za ta koma gida, wasu kudade ta dauko cikin jakarta ta ba wa Mummy, sannan shi ma Abbansu ta bayar aka ajiye masa hade da sakon gaisuwa dayake lokacin da ta zo ya riga ya fice kasuwa, kuma lokacin dawowarsa bai yi ba. Humaira na can dakinta ta ki fitowa bare ta raka Antyn ta ta kamar yadda ta saba, har sai da Mummy ta aika aka fada mata cewa, ta zo ta raka Anty Sakina za ta tafi. Alatilas ta fito, ganin yanayinta kamar ba ta so yasa Anty Sakinar ta ce,
“Aa ta yi zaman tunda aiki take, su Hydar ma za su rakani.”
Tana fada ta ciro naira dubu biyu ta mikawa Humairar tare da cewa, “Ga wannan ko photocopy kin yi a makaranta.”
Babu kunya bare tsoron Allah Humaira ta sa hannu ta karbe kudi tana sakin murmushi, komawa dakin ta yi ta sako hijabi ta fito ta raka ta.
To dawowar Anty Sakina gida kenan, sai ta fada wani sabon tunanin. Tunani take akan yadda bacin ran Usman ya fara illata rayuwarta, har ma ana cewa tana ramewa. Don haka yanzu ya zama tilas ta yi duk me yiyuwa wajen yakice tunaninsa daga ranta, babu shakka idan har ba ta yi da gaske ba to ba iya rama abin zai tsaya ba. Wata cutar ma na iya kama ta ba a sani ba, daga karshe kuma iyayenta za ta dorawa wahala. Yadda cututtukan nan na zamani ba jin magani suke ba, hawan jini da ciwon zuciya yanzu sun zama na zamani, babu babba babu yaro kowa damka suke su galafaitar ko ma su hallakar gabadaya. Don haka dole ne ta nemi mafita, to mene ne mafitar gare ta ? Wannan ita ce tambayar da take yi wa kanta.
A wata ranar Litinin ne suna zaune tare da abokiyar aikinta Anty Zara'u a Staff Room, suna hira. Anty Zara'u ta dube ta ta ce, “Wato na lura kin saka damuwar Usman a ranki sosai, ga shi nan duk yanayinki ya sauya tamkar wacce ba ta da lafiya.”
Wata rarraunar ajiyar zuciya Anty Sakina ta sauke, babu shakka yanayinta abin tausayawa ne. Nisawa ta yi cikin sassanyar murya ta ce, “Wallahi na rasa ya zan yi na ture wannan abin daga zuciyata, nima kaina na san na canja. Satin da wuce na je gaida su Mummy, ita ma tambaya ta yi ya a kai na rame? Sai karya na yi mata na ce bani da lafiya ne. Anty Zara'u bakin cikin Usman ne zai kashe ni na tabbata.”
“Ki daina fadin haka, insha Allah babu abin da zai faru sai alheri. Amma me yasa ba ki fada wa Mummy abin da yake faruwa ba? Kin ga ko jan kunne ne sai a yi masa kila ya daina ko kuma ya rage.”
“Hmm! Anty Zara'u kenan, duk yadda kike tunanin Usman ya wuce nan wallahi. Iya zance ne da shi, indai za a ba shi dama ya yi magana to wallahi sai kin amince da abin da zai fada miki.”
“Hakane akwai mutane irin su sosai, to amma ina ga da kin jaraba sanar da koda Mummy ne ba wai sai iyayensa watakila su san yadda za su bullied wa lamarin. Domin gaskiya zama cikin wannan yanayin ba zai yiyu ba.”