Shɑfi nɑ 15 & 16

5 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Shɑfi nɑ 15 & 16*

Anty Sakina da Usman sun jima sosai suna ta hira abin gwanin ban sha'awa tamkar ba su bane ke rikici. Koda yake dama duk lokacin da Usman din yake son ya karbi wani abu ko kuma ya ranci kudi haka yake mata. Sai ya zama mutumin kirki ya kwnatar da kansa kamar ɗa da uwa.

Ita kuwa Anty Sakina ba ta nuna masa ta gane manufarsa ko kadan, kawai ita burinta a duk lokacin da ta ga yana nuna halin kirki shine da ma ya dore da wannan hali, ya cigaba da kasancewa mai halin kirkin. Abin duk da take yi tana sane, ta yi ne don Allah. Amma duk lokacin da rashin mutuncinsa ya motsa baya ji baya gani, rufe idonsa yake ya yi duk abin da ransa yake so. Babbar damuwarta ita ce neman matan da yake, da zai karo aure zai fi mata alkairi sau dubu a kan neman matan banzan da yake. Bata san wace cuta zai ya yo ya goga mata ba.

Har misalin karfe 9:30pm na dare Usman na nan zaune suna ta hira ba ta ga ya mike ya yi shirin fita ba, tambaya ta jefa masa da cewa, “Yau babu fitar ne, ko an fara bada hutun zuwa club ne?”

“Ban gane wannan tambayar ba, so kike na fita din kenan, korata ma kike daga gidan?”

“Hmm! Ni ba korarka nake ba, da can din da kake fita so nake? Kawai dai tambaya ce na yi. Na ga yadda masu zuwa club din suke bada himma wanda ko wajen ibada basa ba wa muhimmanci kamar haka.”

“To ni ban sani ba, bani da amsar wannan tambayar.”

Dariya Anty Sakina ta yi tare da cewa, “To Allah ya ba ka hakuri, daga tambaya sai *_cibi_* ya zama ƙari.”

“Ke kin idan ba ma zuwa irin wannan wajen tashin hankalin da za'ayi na kadan ne? Allah kadai ya san yawan mutanen da za su hallaka, za'a rika kashe mutane kullum ta Allah. Don haka ki sani mu aiki ne ke kai mu ba wani abu ba.”

Cikin sigar mamakin ya raina mata wayo da hankali ta yi wani dan guntun murmushi tare da cewa, “Lallai kam dole a kashe mutane a wajen idan bakwa nan, ai ya kamata ku cigaba da zuwa kare rayuwar jama'ar.”

“Kin ga ni tashi kiyi kawo min ruwa na sha idan kin gama tuhuma ta din. Ke wallahi da ma aikin namu kika koma kawai domin kin iya tuhuma sosai, babu shakka idan kika saka mutum a gaba ko bai yi laifi ba, za ki yi masa gadar zare ya taka ta burma da shi.”

ƘUDA BA KA HARAMWhere stories live. Discover now