🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*_Shɑfi nɑ 31 & 32_*
Da yake lakca Sadik zai shiga, dalibai na jiransa, bai tsaya lallai sai Humaira ta yi masa magana ba. Binta ce ta saurare shi ta rika amsa masa, kuma ta ji nasihar da ya yi musu sosai, don haka sai ta ce,
“Insha Allah za mu kiyaye, za mu kula sosai ba za mu yi wasa ba. Mun gode Allah ya saka da alkairi Allah ya kara girma.”
Sadik ya sara zai tafi kenan, Binta ta sauri ta mike tare da karbar takardun dake hannunsa tare da cewa, “Kawo na rike maka.”
Mika mata ya yi yana murmushi sannan ya wuce gaba tana biye da shi. Wani irin kududun bakin ciki ne ya turnuke zuciyar Humaira, gaza yin magana ta yi sai wata zazzafar harara da take aikawa Binta. Ita kuwa ko a jikinta sam ba ta san tana yi ba, wai kunu a wani gida.
Binta biye take da Sadik tiryan-tiryan har cikin hall din da zai gabatar da lackar, ta dora masa takardun akan Lecture Stand, sannan ta fito. Dawowa ta yi wajen da ta bar Humaira, tana karasowa ta ga fuskar Humairar ta sauya, dama ta yi tsammanin hakan don haka ba ta wani damu. Ce mata ta yi, “To mu ci gaba ko?”
Banza Humaira ta yi da ita ba ta tanka mata ba, ta sake cewa, “Ya ya lafiya dai? Na ce mu ci gabaa ina muka tsaya ko kin gaji ne? ”
“Ban sani ba, kin ga ya isa haka ba na bukata.”
“Wai mene ne kuma ya faru don Allah? Ko saboda na karbar wa Sadik kayan hannunsa na kai masa aji shi ne abin laifin?”
“To akan me za ki karba ki kai masa? Shi ba shi da hannu ne? Wannan ai shisshigi ne da zubar wa da kanki daraja. Wallahi idan ba ki yi wasa ba sai ya yi miki wulakancin da za ki raina kanki. Wannan ai zubar da aji ne.”
Ta karasa maganar da yin tsaki.
“Haba Humaira ya ya za ki yi masa wannan mugun zato haka? Gaskiya da ganin Sadik mutumin kirki ne, hakan sam ba zai taba zama halinsa ba. Ki duba shawarwarin da ya ba mu fa, tunda muka zo makarantar nan waye ya taba saurarenmu bare har ya ce mana ga yadda tsarin makarantar yake idan ba shi ba? Gaskiya ni dai na dauke shi a matsayin yayana, ba zai ba ni shawarar da za ta cutar da ni ba. Kuma na san kema kin fahimci hakan, kawai idan ba kya son sa ne to ki ce ba kya son sa amma yana da kyawun mu'amala sosai. Ko ba za ki yi soyayya da shi ba, to kema ki dauke shi a matsayin yayanki, zai fi wannan wulakanci da tsanar da kike masa babu dalili.”
“Hmm! Waye zan dauka a matsayin yayana din? Allah ya sawwake, ke din dai da kike kalen dangi ki je ya zama yayan naki. Kodayake ba ma maganar yaya a nan, kawai son sa kike yi ki fito ki fada masa tun da wuri. Amma ki sani Meenat da kika yi gani suna aiki tare ba kanwarsa ba ce, matarsa ce dansu daya da shi, kuma ki lura da ita sosai yanzu haka ma ciki ne da ita. Idan ba ki yarda ba kina iya tambaya.”