🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 59 & 60*
To, a bangaren Anty Sakina kuwa, ta gaza magana. Kuka kawai take marar sauti, Mummy ta sake tambayar ta, "Sakina wai lafiyarki kuwa? Me ke faruwa ne ina ta magana kin ki ba ni amsa, sai kuka kike yi kamar wata karamar yarinya."
Cikin yanayin kukan ta ce, "Mummy Humaira, me na yi..." Sai kukan ya ci karfinta, maganar ta gagara fitowa.
"Humaira kuma, me ya samu Humairar? Hatsari ta yi ne?" Mummy ta fada cikin sigar zakuwa da jin halin da Humairar take ciki.
Anty Sakina ta karfafa muryarta ta ce, "Ita da Usman na gani a gida yanzu na koma duba wani abu."
"Ban fahimci abin da kike fada ba, dazun nan fa Humairar ta ce ta tafi makaranta."
"Mummy zan yi wa Humaira sharri ne, yadda na gan ta da Usman Allah Ya nuna mini Annabi haka." Tana fada ta zaro wayar Humairar, ta kunna mata daya daga cikin recording din wayar da suke yi mafi munin ji, sannan ta ci gaba da cewa, "Wannan wayar wace kuma muryoyin su wa kika ji? Mummy wai yaushe Humaira ta fara irin wannan rayuwa? Kuma me na yi mata da za ta ci amanata? Ta rasa wanda za ta kula sai mijina, muna ciki daya da ita?"
Amsoshin tambayoyin da Anty Sakina ba ta samu ba ke nan, domin kuwa bayan Mummyn ta gama sauraren abin da Usman da Humaira suka tattauna a recording din nan, sai wani duhu-duhu da ba ta san daga ina ya faro ba ya rufe mata idanu. Zaune take amma sai ta yi talau za ta fadi ta baya, Anty Sakina ta taro ta cikin firgici tare da fadin, *"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!* Mummy Mummy!"
Ina, Mummy shiru, idanunta sun rufe. Ta suma ne, sai kukan ya zame wa Anty Sakina guda biyu. Ga kukan bakin cikin Humaira sannan ga na suman Mummy, a kidime ta rika jijjiga ta kafin ta tuno cewa Mummyn na da hawan jini. Sai yanzu ta yi nadamar sanar da ita, "Na shiga uku! Me yasa na fada mata wannan maganar!" Ta furta tare da gyara mata kwanciya a nan tsakar gidan sannan ta shiga ta dauko tabarma ta mayar da ita kai. Ta shiga yin 'yan dabarun da kan iya dawo wa da Mummy numfashinta, amma dai shiru kake ji. Zuwa can sai ta tuno da wani likita makwabcin su Mummyn wanda ya kasance kamar aboki ne a wajen Anty Sakinar, domin tare suka tashi a unguwar.
kiran sa ta yi ya zo, to da ma shi ne yake duba Mummyn idan irin hakan ta faru, zuwansa keda wuya ya yi mata 'yan allurai kuma ya ba da tabbacin za ta farka ba da jimawa ba. Ba a fi awa daya da rabi ba, cikin ikon Allah sai Mummy ta farka, Anty Sakina na zaune a wajen ko motsawa ba ta yi ba, ta zuba tagumi, su Haidar ma sun dawo daga makaranta.
"AlhamduLillah! Sannu Mummy." Anty Sakina ta furta, su Haidar ma sannun suka yi mata.
"Yanzu ina Humairar take?"
Mummy ta tambaya cikin rarraunar murya.