🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 63 & 64*
Nan take Anty Sakina ta ce, a dauki nata jinin a gwada idan zai yi sai diba a kara wa Humairar. Aka dauki samfurin jinin aka gwada, sam ba zai yi ba, kuma ko irin a yi musayar nan da wani ma ba zai yi yu ba. Ita kuwa Mummy ba ma a jaraba daukar nata ba saboda larurarta. Anty Sakina ta rikice sosai ta shiga damuwa, nan ta kira Abba a waya ta sanar da shi.
Kai tsaye ya yo wa asibitin tsinke, yanzun ma dai tare da Najib suka sake zuwa. Da zuwansu likita ya dauki jinin Abba aka gwada, shi ma hakan take, wato ba zai yi wa Humaira ba. Najib da ke wajen ya dubi likitan ya ce, "To ko za a jaraba nawa a gani ko zai yi?"
"Me zai hana?" Likita ya fada.
Nan aka dauki jinin Najib din, cikin sa'a kuwa, shi jinin nasa irin lamba daya din nan ne. Wato dai zai iya ba wa kowanne mutum jininsa. lita guda aka kwasa a jikinsa, aka nufi dakin tantancewa aka yi duk gwaje-wajen da za a yi. Babu wata matsala a tare da shi.
Misalin karfe biyu na rana, mahaifiyar Najib ta yo abinci mai rai da lafiya ta kawo wa su Mummy. A lokacin an fara kara wa Humaira jinin, kuma su Najib ba su kai ga barin asibitin ba sakamakon likitan ya ce kada ya yi garajen yin tafiya ko kuma wani aikin, kasancewar an taba jininsa akwai bukatar ya huta sosai.
"Ikon Allah! Ashe dai abin babban ne haka? Har da karin jini? Mahaifiyar Najib ta fada, lokacin da Mummy ta kai ta da nufin ta sake ganin jikin Humairar.
"Wallahi kuwa kin ga dai lamarin Ubangiji!"
"To da ma wai ba ta da lafiya ne ko kuwa?"
"Wallahi lafiyarta kalau fa, jiya-jiyan nan da rana ta yanke jiki ta fadi a sume, to daga wannan faduwa ne kuma sai abubuwa ke faruwa, daga wannan sai wannan."
"To Ubangiji Allah Ya sawwake, Allah Ya sa zakkar jiki ce."
"Amin, kuma an sa ki dawainiya, Allah Ya saka da alkairi."
"Ah haba dai! Wallahi babu komai, ai an riga an zama daya, wannan duk yi wa kai ne."
Sai bayan La'asar suka tafi gabadaya, wato da Abba da Najib da kuma ita mahaifiyar Najib din, suka koma kasuwa ita kuwa ta yo gida. Wannan ke nan.
Yinin yau gabadaya Anty Zara'u ba ta shiga makaranta ba, kasancewar ba ta jin dadin jikinta, ta tashi jikinta duk ciwo yake tamkar wacce aka yi wa dukan tsiya. Tun safe take kwance kuma wayarta a kashe take. Ta kashe wayar ne domin kada a dame ta, sai yanzu da yammaci ta dan ji kwarin jikinta; ta mike ta yi sallah sannan ta bude wayar da nufin ta kira Anty Sakina, ta ji ya ya makarantar ta yini? Domin har kawo yanzu ba ta san me ke faruwa ba a bangaren Anty Sakinar.