🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*_Shɑfi nɑ 39 & 40_*
Binta ta nuna matukar takaici da rashin jin dadin makin da Humaira ta samu, abin ya dame ta a rai sosai. Hakan yasa ta samu Humaira a karkashin wata bishiya suna hutawa, ta fara mata nasihohi da jan hankali kamar haka,
“Wai shin mene ne matsalarki? Gaskiya ni na rasa gano kan wannan lamari, ban ji dadin results din da ya fito a haka ba. Yanzu fa kina matsayin *probation* ne, ya zama tilas mu canja tsarin karatun nan. Ba zai yiyu mu cigaba da tafiya a haka ba, sam Mummy da Abba ba za su ji ba idan kika fada musu abin da kika samu a first semester. Ina ganin zai fi kyau kawai ki bari sai mun yi jarabawar second semester, idan aka hada makin da na baya aka raba biyu zai dan kara yawa koda maki biyu ne (2 points) kika samu a ND I ya fi. To sai gaskiya hakan ba zai samu ba sai kin sake daura sabuwar damara.”
Cikin yanayin ko in kula alamar abin bai ma dame ta ba, a wulakance ta dubi Bintar ta ce, “To wai wace irin damara kike so na daura kuma? Ba dai karatu bane ina yi sai me kuma?”
“Hmm! Ba haka za ki ce ba, nima kuma ban ce ba kya yin karatu ba, amma shin mene ne ba kya ganewa? Abin da nake nufi kenan, sannan kuma dama ina son na ba ki shawara. Ya kamata ki raba kanki da Ruky, matukar kina son rayuwarki ta yi kyakkyawan karshe. Kowa ya san halinta, ki duba irin kayan da take sawa kawai ya isa ya nuna rashin tarbiyarta sannan ba ta jin kunyar zama cikin taron maza.”
“Kin ga mu bar wannan maganar kawai, tunda kema kin fara zama 'yar sa ido.”
“Hmm! Humaira ya kamata ki yi tunani da nazarin maganganun da nake fada miki, shin wai kin manta nasihar da Mummy ta yi mana?”
“Ban manta ba, amma kula kawa sai ya zama laifi? Ai na ga ba maza nake kulawa ba ko malama ustaziya.”
“Hmm! Humaira kenan, hakane ba maza kike kulawa ba amma da ki kula Ruky gara ki kula namiji matukar ba maganar banza ya neme ki da ita ba, domin akwai maza mutanen kirki wanda taimakon ki ma za su yi. Ita kuwa wannan yarinyar da kike gani ba mutunci bane da ita, sannan babu me yi mata kallon wacce ta fito daga gidan mutunci. Muddin kika ci gaba da kula ta to babu shakka kema mazan za ki rika kulawa. Yadda ta zama kamar karya kema haka za ki zama, domin haka Hausawa ke cewa, abokina barawo shi ma barawon ne, kuma zama da madaukin kanwa shi ya ke kawo farin kai.”
“Ni dai zancen nan ya fara isa ta, wai to da kike cewa na rabu da ita, ba ki ga results dinta bane ya yi kyau? Idan wasa take ta ya ya za ta samu (3.75 points)?”
“Shi kenan na ji ba ta wasa da karatu, yanzu karatun za ta rika koya miki kenan?”
“E mana, tunda ke yanzu kin samu Sadik ba ki da time dina ai sai ki je ki karata da shi. Nima sai ki kyale ni na samu wadanda za su bani time dinsu.”