Shɑfi nɑ 23 & 24

8 1 0
                                    


🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

      ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
   *_PEN WRITERS  ASSOCIATION_*
      ✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://mobile.facebook.com/Pen-Writers-Association-100990022185172

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*_Shɑfi nɑ 23 & 24_*

Tuni wasu daliban sun fara zuwa sosai har an kafa layi. Binta cike take da mamakin Humaira, tambayoyi ne makil a ranta, daya kawai ta iya yi mata dangane da zuwan da Mai Adaidaita Sahu ya fara daukar ta sannan su wuce gidan su Humairan. Ta yaya hakan za ta kasance? Ita da ba waya ce da ita ba?

Murmushi Humaira ta yi sannan ta kada baki ta ce, “Kada ki damu wannan abu shi ya fi komai sauki, yanzu idan mun gama da nan za mu je a sayi layin waya sabo ayi miki register da sunanki idan mun koma gida zan ba ki wayata ki saka layin sai ki kira Mai Adaidaita Sahun ki yi masa bayani, ina fatan kin gane?”

“To shike nan babu damuwa.”

Layin su ma suka hau, bayan kamar mintuna arba'in (40 minutes) suka isa wajen me karbar kudi (cashier), suka biya kudin aka ba su Scratch Card, wanda da shine za su yi Online Registration su fitar da jadawalin darussan da za su karanta a wannan shekara ta farko. Fitowarsu keda wuya suka sake tare wani Mai Adaidaita Sahun, babu inda suka zame sai kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut. A nan Humaira ta sayi sabuwar waya irin ta ta komai da komai sannan kuma suka sayi sabon layi wanda za a ba wa Binta kamar yadda ta yi alkawari. Daga nan kuma kai tsaye unguwar su Humaira suka yo wa tsinke, babu jimawa suka iso.

Suna shigowa cikin gidan, Mummy ce da kannen Humaira sun dawo daga makaranta suna cin abincin. Sallama Humaira ta yi Mummyn ta amsa tare da cewa, “Har kin dawo? Babu cinkoso kenan?”

“E wallahi kuwa Mummy babu mutane sosai.”

Binta ta durkusa har kasa ta gaida Mummyn cikin ladabi da girmamawa, sannan suka wuce dakin Humairan. Daki ne madaidaici da ke dauke da gado da sif da lokoki, Humaira kadai ke kwana cikin dakin. Kana shiga za ka tabbatar da hakan domin a gyare yake da abubuwan kawata daki, kamshi ne kawai ke tashi. Shiga suka yi Humaira ta cire hijabinta ta fito kitchen ta zuba musu abinci ta koma suka ci sosai sannan suka huta.

Humaira ta mike ta dauko tsohuwar wayarta da ta boye kafin ta fita daga gidan, ta mikawa Binta ta ce, “Karbi wannan wayar ki saka layin nan a ciki ki cigaba da amfani da ita.”

Cike da mamaki Binta ta zaro idanu tana duban Humaira, ta gaza magana. Wani dan gajeren tunani ta afka, a ranta take cewa, “Wai wannan mafarki nake ko kuwa a ido biyu nake? Nine ce da waya yau? Ba ma wannan ba, shin dama har yanzu ana samun kawaye irin wannan? Ba mu dade da haduwa ba amma sai kyautuka take min haka?”

ƘUDA BA KA HARAMWhere stories live. Discover now