🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝
*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*
_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮Shɑfi nɑ 43 & 44
BAYAN SATI BIYU
Bayan kamar sati biyu da zuwan Usman makarantar su Humaira, sai ya sake dawowa; amma a wannan karon ba wajen Humairar ya zo ba, ba da ita yake muradin haduwa ba. Saboda haka ma ko sanar da ita bai yi ba, gaba-gadi kawai ya niki gari ya tafi. So yake ya hadu da Binta ko Ruky; tun da ya gan su maitarsa da arwarsa suka doru akansu. Ya so tun a ranar ya samu lambar wayoyinsu, musamman Ruky dayake ganin da alama 'yar hannu ce ta san komai, ba za a sha wahala ba za ta ba da kai; domin ya lura kanta na dan rawa musamman idan ta ga kudi.
Cikin sa'a kuwa yana shigowa bakin kofar makarantar kafin ya kai neman wajen tsayawa, Ruky ta kawo kai za ta fita, kwatsam sai ya hange ta cikin ransa ya ce "Faduwa ta zo daidai da zama." Amsakuwwar motar ta danna; kamar ta san da ita yake, sai ta dubi inda ta ji sautin amsakuwwar yana fitowa daidai lokacin shi kuma yana dauke gilashin sashen da za su iya hada ido. Ai kuwa karaf suka yi ido hudu da juna, murmushi hade da sigina ya sakar mata; ba tare da ya kira ta ba kai tsaye ta nufi wajensa tana sakin nata murmushin yayin da shi kuma ya dan saki hanya ya gyara parking. Tana isa jikin motar kafin ta yi magana ya ce,
“Am sorry 'yammata, na dakatar dake daga uzurinki ko?”
“No ba damuwa; ni kamar ma na so na shai da wannan fuskar?”
Cikin sigar kwarkwasa da yaudara take wannan maganar, Usman ya dan lumshe idanu ya bude sannan ya ce, “May be haka ne, there was a time da na taba shigowa school din wajen wata yarinya kamar ma friend dinki ce.”
“Okay, tabbas na tuna Humaira ko? Ai tana ciki. Bari na kirawo maka ita.”
“No,kyale ta kawai ai ba wajenta na zo ba yanzu.”