Shɑfi nɑ 61 & 62

5 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Shɑfi nɑ 61 & 62*

*"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN!"*

Mummy da Anty Sakina suka furta a tare cikin kidima. Da sauri Anty Sakina ta matso kusa da Humairar da ke kwance shameshame tamkar gawa, ta kai hannu ta kama ta da nufin ta tashe ta, ji ta yi zafi mai tsanani ya ratsa tafin hannun, sai firgicin nata ya kara ta'azzara. Duban Mummy ta ce, "Ai ba ta da lafiya ma, zazzabi ne a jikinta kamar wuta." Ta fada tare da jan Humaira jikinta ta rungume.

*"INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN! Wai me yake faruwa ne? Wace irin jarabawa ce take shirin faruwa da mu?"*

Mummy ce ta fadi haka cikin tsananin firgici gami da matsowa wajen da Humaira take, bayan ganin wani jini yana naso ta kasan Humairar wajen cinyoyinta. Gyara kwanciyar Humairar da Anty Sakina take yi, sai ita ma ta yi tozali da wannan jini. Nan fa razanar tata, ta fi ta Mummy.

"LA'ILAHA ILLALLAHU!" Ta fada cikin wani irin kuka mai tsananin tayar da hankali sannan ta ci gaba da cewa, "Usman Allah Ya isa tsakaninmu da kai."

Mummy kuwa salati da sallallami kawai take, Anty Sakina ta mike da sauri ta zari hijabinta sai titi. Ta taro Mai Adaidaita Sahu domin a dauki Humaira zuwa asibiti, cikin sa'a kuwa mutum na farko da ta tsayar ya biyo ta zuwa lungun nasu, tun bai gama tsayawa ba ta dire ta nufi cikin gida. Tana shiga suka dan gyara wa Humaira jikinta, suka ribanya mata zannuwa sakamakon jinin na ci gaba da zuba. Anty Sakina ta saba ta a baya ta fito da ita zuwa cikin Adaidaitar. Kai tsaye Asibitin Murtala suka nufa, sashen ba da kulawar gaggawa. Har lokacin Humaira a sume take babu alamun numfashi ma a tare da ita, sannan kuma jinin nan na ta ambaliya ta gabanta.

Da shigarsu kuwa cikin sa'a aka wuce da Humaira bangaren kula da masu ciki, hakan dai ya so ya ba wa Mummy mamaki, to amma kuma ba abin mamaki ba ne. Sai abin da bincike likitocin ya nunar. Likita ya baza komarsa akan Humaira ya fara bincike irin nasu na masana harkar lafiya. Gabanin hakan dai ya fahimci suma ta yi, don haka na'urar taimaka wa numfashi aka saka mata kafin daga bisani ya dora da bincikar sauran cututtukan da suke damun ta. Fiye da mintuna arba'in da biyar likitan ya kwashe yana ta gwaje-gwaje, a karshe dai binciken ya bayyanar da cewa, jininta ne ya hau sosai bisa matsananciyar damuwa da tsoro da ta shiga. Kuma a sanadiyyar hakan ne ma cikin jikinta wanda ya kai tsawon watanni uku da rabi ya zube, shi ne musabbabin zubar jinin nan na gabanta. Wannan shi ne sakamakon farko da ya bayyana, kuma kamar haka likitan ya sanar da su Mummy. Nan dai ya rubuta musu magunguna da allurai ya ce a yi sauri a nemo su. Anty Sakina ta karbi katin ta fito bakin asibitin asibitin shagunan da ake sayar da magunguna, har tuntube take saboda tsananin sauri, ta saya cikin hanzari ta koma ta kai.

ƘUDA BA KA HARAMDonde viven las historias. Descúbrelo ahora