🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝
*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*
_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Shɑfi nɑ 53 & 54
Binta na gama karanta takardar nan ta lumshe idanunta, wata kaunarsa take jin tana ratsawa hade da zagaya ilahirin farfajiyar birnin zuciyarta. “Babu shakka zantukan Hausawa tamkar nassi suke, na yarda kowacce kwarya da abokin burminta. Wannan shi ne mijina na hakika, don shi aka gina ni. Ya Ubangiji ina gode maKa bisa wannan ni'ima da zabi da ka yi mini. Ina kuma rokonKa da Ka saka fahimta da zaman lafiya a tsakanina da matarsa. Ya Allah duk abin da zai kawo mana cikas da sabani Ka kawar mana da shi.”
Zantukan da ta yi ke nan a ranta lokacin da ta zauna bisa kujera a tsakar gida, daidai lokacin kuma Baba Abu ta fito daga bayi, zumbur ta mike ta rumgume ta cike da murna tana fadin, “Baba to ya ya kika ga angon naki, na iya zabe ko?”
“Ah! TubarakAllah Ma Sha Allah! Babu shakka wannan angon namu na kwarai ne, da ganin sa dan manya ne kuma zai yi tausayi bisa ga dukkan alamu. Na san ba ki da matsala, irin shashancin nan na zamani duk bai dame ki ba, to amma ina son ki kara kama kanki, ki yi masa dukkan biyayya, kada ki kuskura ki daga masa murya duk abin da zai yi miki. Sannan ki dauki matarsa a matsayin 'yar uwarki ba kishiyarki ba, kada ki kuskura sa'insa ta hada ki da ita, yaranta yaranki ne. Ki kama su hannu bibiyu, ki ja su a jikinki, duk wahalhalunsu ki dauke mata. Mai d'a wawa ne, da d'ansa ake kama shi. Duk rashin kirkin mutum matukar kana son nasa ka ja shi a jiki, to sai dai ya yi wa wani rashin kirkin amma ba kai ba. Wannan ita ce dabarar zama da kishiya. Ina fatan Allah Ya hada zukatanku, Allah Ya tabbatar da alkairi.”
Binta ta kwantar da kanta a kan cinyar Babar tana sauraren ta a nutse, sai da ta gama maganar duka sannan Bintar ta sauke numfashi ta ce, “Amin summa amin. In Sha Allah zan kiyaye duk abin da kika ce mini, za ki same ni me matukar biyayya da bin umarninki.”
“Yawwa! Allah Ya yi miki albarka, Allah Ya jikan mahaifanki Allah Ya kai rahama kabarinsu.”
“Amin.” Ta amsa muryarta cike da rauni yayin da kwalla ta ciko a idanunta. Iyayenta ta tuno, duk da cewa lokacin da suka bar duniya ba ta da wani cikakken hankali. Share hawayen ta yi sannan ta mika wa Baba kudin nan tare da cewa, “Ga wannan dubu Ashirin ne, kudin aikin da nake taya shi ne. Tun a makaranta ya ba ni na ki karba shi ne ya biyo ni da su yanzu.”