Shɑfi nɑ 67 & 68

4 1 0
                                    

🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_* 

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝
                      🐝🐝🐝🐝
                          🐝🐝🐝
                              🐝🐝
                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑ yi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑn yi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
 

_Written by:_
           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/

👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑn yi don cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Shɑfi nɑ 67 & 68*

Nan dai Binta ta ci gaba da yi wa Humaira nasihohi masu ratsa jiki, tare suka yini gwanin ban sha'awa. Ranar Litinin da safe Anty Sakina ta umarci Humaira da ta shirya maza ta tafi makarantar, kamar yadda ta yi alkawari ta kawo kudi naira dubu ashirin (20,000), a gaban Mummy ta mika mata tare da cewa, "Ga kudin registration din ki je ki biya, idan akwai wani abin da kike bukata kuma ki sanar da ni. Allah Ya kiyaye Ya kuma ba da sa'a."

Humaira ta amsa da, "Amin na gode."

Mummy ta yi matukar farinciki da jin dadin yadda Anty Sakina take mu'amalantar kanwar tata, addu'ar fatan alkairi ta yi musu gabadaya tare da jaddada musu muhimmancin hadin kai da zumunci da kulawa da dan uwa. Ta sauke nasihar tata da kara jan kunnuwan Humaira sosai hade da buga mata misalin matsalolin rayuwa iri-iri da yadda ake magance su har a kai ga cim ma kyakkyawan buri. Nan dai Humaira ta shirya ta fita, kai tsaye bankin da suke biyan kudin makarantar ta nufa, ta biya sannan ta isa makarantar. A can suka hadu da Binta a cafe din Sadik.

Binta ta yi farincikin ganin komowar kawar tata cikin makaranta, nan take ta karbi scratch card din ta shiga shafin yanar gizon makarantar ta yi mata online registration, ta fitar mata da semester forms sannan kuma ta raka ta ofisoshin da ake sa-hannu aka sa mata. To wannan ke nan.

A bangaren soyayyar Sadik da Binta kuwa, abin sai son barka. Domin tuni aka yi baikonsu an tsayar da cewa bikin zai kama a cikin watan da za su kammala karatu gabadaya. Humaira ba ta ji dadin labarin ba, to amma ko kusa ba ta bari hakan ya bayyana a fuskarta ba, alatilas ta hadiye kishinta. Daga baya sai ta fahimci ashe shaidan ne yake kokarin hada ta da aminiyar tata, domin Binta mutum ce har mutum. Duk inda kawar arziki take to Binta ta kai, don haka sai ta rika nuna farincikinta da yin fatan alkairi. Sannan kuma ta daina yi wa Sadik din wulakancin da take masa a baya, hasalima Cafe din ne ya zame mata wajen zama a duk lokacin da suka fito daga lakca kafin su shiga wata, kasancewar Anty Sakina ta kafa mata takunkumin yawo da wasu kawayen wanda ba Binta ba.

Sadik ya fahimci iyayen Binta ba masu karfi ba ne sosai, hasalima ga shi sun mutu. Saboda haka bai dora musu wani nauyi ba, cewa ya yi, shi yarinya yake so, don haka ya yafe komai na dangane da kayan daki, shi zai yi mata komai.

Sai dai a hannu guda kuma yana fuskantar cikas da kalubale sosai ta bangaren matarsa Meenat,  domin lokacin da ya sanar da ita kudurin nasa na auren Binta, tsalle ta yi ta dire, ta tayar da kayar baya ta ce, sam bai isa ya yi mata kishiya ba. Ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa, ba zai yi yu ba. Sai dai ya zaba ko ita din ko kuma Bintar. Babu wani irin kalar rashin mutumci da tashin hankalin da ba ta nuna masa ba, ta yi tijararta son ranta. To sai dai duk wannan abin da ta yi bai bata wa Sadik rai ba, shi a kullum ba abin da yake illa ganin ya shawo kanta, ta hanyar faranta mata rai. Burinsa ya fahimtar da ita cewa, ba wai gazawa ta yi wajen biya masa bukata da kula da shi ba, sannan kuma ba wai son ta ne ya ragu a zuciyarsa ba. Abu dai har ya yi tsanani da ta daina kula shi gabadaya, hatta wajen aikin ma ta daina zuwa taimaka masa. Kyautuka iri-iri babu wanda ba ta gani, amma fur ta rufe ido ta ce, ita kawai ya gaji da ita ne shi yasa zai auri wata, da ma haka maza suke.

ƘUDA BA KA HARAMOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz