🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑn yi don cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 69 & 70*
To a bangaren Anty Sakina kuwa, tana nan tana ci gaba da saide-saiden kayanta, har iddarta ta cika, babu abin da ya dame ta. Hankalinta ya kwanta sosai, ita a yanzu sam ba ta sha'awar komawa duniyar ma'aurata a kwana kusa. Duk cewa wasu mazan sun fara nuna kwarkwasa gare ta, musamman abokan aikinta. Amma dai ta ki ba da fuska.
Anty Zara'u ce take wa Anty Sakinar wani hange, sai dai ta rasa ta yadda za ta bayyana mata abin. So take yi yaya Ahmad ya auri Anty Sakina. Idan masu bibiyar wannan labari za su iya tunawa, matar yaya Ahmad wato Farida, ta rasu ne akan gwiwa, lokacin haihuwa. Kuma Har kawo yanzu bai yi wani auren ba, duk da matsin lambar da yake fuskanta daga wajen Hajiyarsa da kuma ita Anty Zara'un. Babu shakka ya dace a ce tuni ya yi wani auren, to sai dai gani yake kamar ba zai iya samun wacce za ta maye masa gurbin Faridar ba. Domin duk inda mace ta-gari ta kai, to Farida ta wuce nan. Tana da kunya da tsananin hakuri.
Watarana Anty Sakina ta je gidan su Anty Zara'u, suka yi yini suna hira gwanin sha'awa. Bayan ta tafi, sai Anty Zara'u ta sami Hajiyarsu take ce mata, "Hajiya da ma ina son mu yi wata magana ne da ke, amma ban sani ba ko ke ma kin hango dacewar abin."
Hajiya na kishingide bisa kujera ta ce, "Ina jin ki, wane abu ne haka?"
"Hajiya da ma ba wani abu ba ne, da a ce yaya Ahmad zai ji shawarata kawai ya auri Anty Sakina, ko ya kika gani?"
Hajiya ta yi murmushi tare da cewa, "Lallai kam, yo kina ganin ko zancen auren ma ba so yake ana yi masa ba, abin dai da kamar wuya, zaman akuya a fadar kura. To amma ga wani hanzari ba gudu ba, ita Sakinar ce ta nuna tana son shi ko kuwa dai shirinki ne?"
"Hmm! Hajiya ke nan, ba ita ce ta fada ba. Ita ma kamar yadda yaya Ahmad din ba ya son a yi masa zancen aure, haka ita ma take. Amma duk wannan hasashensu ne, idan Allah Ya kaddara aure a tsakaninsu babu yadda za su yi. Sai Allah Ya sauya zukatansu da tunaninsu nan take. Ni dai na san Anty Sakina, in dai har yaya Ahmad zai nuna yana son ta, to ba za ta taba juya masa baya ba. Ina son na fada masa tun lokacin da ta gama iddarta, to amma na rasa ta yadda zan bullo wa lamarin. Don Allah Hajiya ki shawarce shi, ke dai kika san yadda za ki yi masa ya amince."
"To shike nan, Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkairi, In Sha Allah zan yi masa maganar."
Haka kuwa aka yi, washegari da safe yaya Ahmad ya zo gai da Hajiyar kamar yadda ya saba kafin ya wuce kasuwa. Bayan sun gaisa din, jim kadan ya mike zai tafi sai Hajiyar ta ce, "Af ni na manta ma, ina son mu yi wata 'yar magana da kai."