🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shɑfi nɑ 19 & 20*
To wadannan mutane guda biyu wato Anty Zara'u da Malam Sadik, abokan aikin Anty Sakina su kadai ne take dan fadawa matsalarta su taushi kirjinta ta samu sauki a ranta. Sun zama aminanta, ta su ta zo daya, su ukun nan tamkar 'yan uwan jini suke. Haka suke mu'amalarsu duk abin da ya samu daya to tamkar su ukun ya samu, sawa'un abin farin ciki ne ko kuma akasin hakan ne. Sukan hadu su yi duk me yiyuwa idan wata damuwa ta samu daya su samar da mafita ko kuma akalla su ragewa wanda abin ya samu damuwa. Sukan tallafawa junansu da kudi idan sabga ta samu, walau sha'anin bikin suna ko na aure. Wannan kenan.
*** *** ***
Shi kuwa Usman na gama cin abincinsa shimfidewa ya yi, ya shari baccinsa me isarsa sai misalin karfe 12:00pm na rana ya tashi a gaggauce domin ya kusa makara, ya shirya ya fice wajen aiki. Ficewarsa keda wuya Anty Sakina ta dawo daga wajen aiki, babu laifi ta dan samu saukin baccin ran da ta fita da shi sakammakon dannar kirjin da aminan nata suka mata, ba kamar lokacin da fita ba.
Sai dai kuma zaman doya da manja ne me matukar tsanani ya sake dawowa tsakaninta da Usman, kusan babu me tankawa wani, kowa sha'aninsa gabansa yake. Duk lokacin da ya gadama ya fita haka nan duk lokacin da ya yi niyya ya dawo. Kazalika halin nan nasa na yin waya da matan nasa na nan. Duk dai wani nau'in halin rashin kirki da iskanci babu wanda Usman ya fasa ko kuma ya rage.
*_BAYAN MAKO GUDA_*
To kawo yanzu dai an kafewa su Humaira admission kuma sunanta ya fito cikin jerin daliban da suka yi nasarar samun gurbin karatu a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kano, za ta karanta fannin harkokin kasuwanci (Business Administration) a turance. Bayan ta duba sunanta, Usman ne mutumin farko da ta fara kira ta fada masa, ya ce, “Kai Masha Allah, amma na ji dadi fa sosai. Congratulations, kin ga yanzu mun samu dama sosai, babu wani abu da zai zama cikas a tsakaninmu. At any moment za mu iya haduwa, ko ya ya kika ce?”
Murmushi me sauti ta yi sannan ta ce, “E haka ne.”
“To yanzu ya ya za'ayi, yaushe za'a fara registration din?”
“Sun bamu sati biyu daga yau din nan.”
“Okay to yanzu yaushe za mu sake haduwa kenan?”
“Duk lokacin da kake so amma fa gaskiya ina jin tsoron sake zuwa gidan nan, kada wataran Anty Sakina ta dawo ta riske mu fa, ka ga abin da take zargi sai ya tabbata, ka ga matsala ce za'a samu babba.”