Shɑfi nɑ 41 & 42

5 1 0
                                    

🐝

🐝🐝

🐝🐝🐝

🐝🐝🐝🐝

🐝🐝🐝🐝🐝🐝

       *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀ ᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*  

             🐝🐝🐝🐝🐝🐝

                      🐝🐝🐝🐝

                          🐝🐝🐝

                              🐝🐝

                                  🐝

*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*

≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫

  

_Written by:_

           *Sɑdik Abubukɑr*

_Wɑttpɑd @sɑdikgg_ 

 👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍️

 👮👮👮👮👮👮👮👮👮

*_Shɑfi nɑ 41 & 42_*

Humairah na gama da Usman kenan sai ga Binta sun iso da Mai Adaidaita Sahun da yake kai su makaranta, gida ta ta yi wa Mummy sallama sannan ta fito suka wuce. Shi ma gogan naku dan fama, shiri ya fara yi nan-da-nan ya gama ya fito ya hau mota, bai zame ko ina ba sai makarantar. Su Humaira ba su jima da isa ba, suna tattaunawa akan wani assignment da aka ba su; Humaira na son Binta ta yi mata.

Kiran wayar Usman ne ya shigo, dagawa ta yi kafin ta yi magana ya ce, “Ina fatan ban riga ku isowa ba ko? Kin ganni na shigo school din taku.”

Waigowa ta yi kafin ta yi magana ta dubi kofar makarantar, motarsa ta hango ya dan saki hanya kadan ya tsaya. Lumshe idanu ta yi sannan ta ce, “Gaskiya ka yi sauri; kamar kana bayanmu, ai ni na zaci ba yanzu za ka zo ba. Na hango motarka ai, ka dan kara shigo ciki wajen wasu dogayen bishiyun turare za ka hange ni.”

Taka motar ya yi kadan a hankali ya iso daidai wajen da ta yi masa kwatancen. Binta kuwa saroro ta yi tana kallonta cikin mamaki ta ce, “Waye kuma kuke waya da shi har kike kwatanta masa inda kike? Hala bako ne?”

“Hmm! Sarkin tambaya kenan, ke dai bakya iya gani ki yi shiru sai kin tofa. Wani saurayina ne, mun dade ba mu hadu ba; ma'aikaci ne ba a nan garin yake aiki ba. Hutu ya zo ne shi ne yake so mu gaisa; da wuri zai koma, ya matsu ya ganni shi ne ya biyo ni school.”

Murmushi Binta ta yi tare da cewa, “ya yi kyau, ni bari na wuce café sai an jima kenan?”
Canja fuska Humaira ta dan yi sannan ta ce, “Ban gane ki wuce café ba? Ba za ki zo ku gaisa ba? To ai sai ki je din.” Ta karasa maganar tare da galla mata wata masifaffiyar harara, dariya Binta ta yi ta ce, “Allah Ya huci zuciyarki, mene ne abin fadan kuma? Indai gaisuwa ce mu je ya samu.”

Mikewa suka yi suka iso inda ya yi parking, ya dan sauke glashin bangarensa yana sakin wani irin matsiyacin murmushi, sallama Humairar ta yi masa ya amsa sannan suka gaisa. Minti kamar daya haka, babu wanda ya yi magana. Zuwa can ya nisa tare da cewa, “Ya ya karatun dai, da fatan ana ganewa.”

Murmushi suka yi Binta ta dora da cewa, “Karatu Alhamdulillah.”

Hira ce ta barke sosai tsakaninsu game da harkar karatun nasu, hankalin Usman ya fi karkata wajen Binta, sauraren ta yake sosai fiye da Humairar sannan ga wani shegen kallo da yake yawan yi wa Bintar wanda har ita kanta ta fara kosawa da shi, ba ta son ta ce za ta tafi ne Humaira ta yi mata masifa da jaraba.

ƘUDA BA KA HARAMOpowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz