🐝
🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝🐝🐝*_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*
🐝🐝🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝🐝
🐝🐝🐝
🐝🐝
🐝*_❝Imɑm Shɑfi'i yɑ ce: "Zinɑ bɑshi ce, 'yɑ'yɑ mɑtɑ ke biyɑ. Idɑn kɑ biyɑ dirhɑmi dubu kɑyi dɑ 'yɑr wɑni to kɑi sɑi ɑnyi dɑ 'yɑrkɑ kyɑutɑ.❞_*
≪━─━─━─━─◈─━─━─━─━≫
_Written by:_
*Sɑdik Abubukɑr*_Wɑttpɑd @sɑdikgg_
✍✍✍✍✍✍✍✍✍
*_PEN WRITERS ASSOCIATION_*
✍✍✍✍✍✍✍✍✍
__________________________________
*~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~*
____________________________________
https://www.facebook.com/110384724043172/
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/👮👮👮👮👮👮👮👮👮
*Wɑnnɑn lɑbɑri kirkirɑrre ne dɑ bɑi shɑfi kowɑne mɑhɑluki bɑ. Idɑn sunɑ ko siffɑ sukɑ dɑce dɑ wɑni, to ɑkɑsi ɑkɑ sɑmu. Bɑnyi dɑn cin zɑrɑfin wɑni bɑ.*✍
👮👮👮👮👮👮👮👮👮*Shafi na 5 & 6*
Kamar yadda kuka ji kuma kuka karanta, Humaira da Anty Sakina 'yan uwan juna ne ciki daya. Wa da kanwa ne, su hudu ne a wajen iyayensu, Anty Sakina ita ce babba sai Humaira na bi mata, sai Haidar, koda yake tsakanin Haidar da Humaira akwai tazara mai yawa. Zainab ita ce 'yar autarsu wacce take bin Haidar. Zaune suke a dan gidansu na rufin asiri dake unguwar Zaitawa ta cikin birnin Kano.
Mahaifiyarsu sunanta Sadiya, amma suna kiranta da mummy, ita 'yar asalin garin Jigawa ce aure ne ya kawo ta garin Kano. Shi kuma mahaifinsu sunansa Alhaji Adamu mai goro. Dan kasuwa ne a kasuwar 'yan goro ta Ujile.
Huamira za ta kai kimanin shekaru goma takwas (18) da haihuwa, tana ajin karshe a makarantar sakandiren 'yan mata ta Masaka dake kofar mazugal. Humaira yarinya ce mai garin jiki, tana da tsayi da jiki sosai. Fara ce kyakkyawa akwai ta da kyakkyawar da sura mai jan hankalin 'ya'ya maza, musamman dukiyar fulanin nan dake makare a kirjinta. Kallo daya lafiyayyen namiji zai yi mata, ya ji wani abu ya darsu a cikin zuciyarsa.
Anty Sakina, mata ce ga Usman kamar yadda ya gabata, ya aure ta shekaru hudu da suka wuce, har kawo yanzu basu haihu ba. Koda yake shi Usman din ne baya son haihuwar, magani hana daukar ciki yake bata ba tare da ta sani ba. Shekara daya da yin auren nasu bayan ta kammala karatunta na N.C.E a kwalejin ilimi ta Sa'adatu Rimi, sai ta samu aikin koyarwa. Yanzu haka dai ita malamar makaranta ce.
Anty Sakina mace ce mai cikar kamala, tana da tsananin kula akan dukkan al'amura musamman wanda suka shafe ta. Dukkan abin da ta saka a gaba sai ta cimma shi da izinin Allah, bata taba fara abin da ta san ba za ta iya kammalawa ba. Kaifi daya ce, bata da boye-boye, sannan ta kasance mai matukar biyayya da girmama duk wanda ya girme ta.
Tsananin biyayyarta ne yasa ta amince har ta auri Usman, amma ba dan tana sonsa ba. Sam bashi da wani kyakkyawan hali ko kamalar da za ta so shi, cika umarnin mahaifinta ne da rashin son bata masa rai yasa alatilas ta aminta da auren Usman. Duk da kasancewar bata sonsa, hakan bai sa ta nuna masa wulakanci ba ko kuma ta rika bata masa rai. Sai idan ya yi abin da bai dace ba, takan nuna masa ya yi ba daidai ba ta hanyar da ta dace...
*_Shin to waye Usman kuma???_*
Cikakkken sunansa shine Usman Bala mai doki, koda yake tuni wasu daga cikin abokan aikinsa suka sauya masa suna, suke kiransa da *_ƙᴜᴅᴀ ʙᴀᴋᴀ ʜᴀʀᴀᴍ_*. Dan asalin unguwar Jakara ne duk a cikin birnin Kano. Ma'aikacin damara ne wanda ake musu kirari da *"Abokin kowa"*, igiya uku ce a kafadarsa.